bayyinaat

Published time: 17 ,November ,2018      09:36:04
Yau ce ranar da na kammala addininku gareku na cika ni'imata kanku na yardar muku da muslunci a matsayin addini.
Lambar Labari: 286
 
Ina farawa da sunansa madaukaki dukkanin godiya da yabo sun tabbata da mahaliccin samuwa tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halittu Muhammad da iyalansa tsarkaka
Allah madaukakin sarki cikin bayyanannen littafin sa da yankaken zancen sa yana cewa:
(إنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللهِ الإسْلامُ ) .
Hakika addinin a wurin Allah shi ne muslunci.
(وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإسْلامِ دِينآ فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ ) .
Duk wanda ya nemi wani addini koma bayan muslunci ba za a karba daga gare shi ba.
(اليَوْمَ أكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإسْلامَ دِينآ).
Yau ce ranar da na kammala addininku gareku na cika ni'imata kanku na yardar muku da muslunci a matsayin addini.

Muslunci mai girma shi ne addinin Allah madaidaici kamar yadda ayoyi masu daraja da lafiyayyen hankali suka nassanta hakan da dukkanin bayyanarwa kan haka.
Muslunci shari'a ce daga sama wacce aka aiko Muhammad annabi mafi girmama annabin rahama kuma rahama ga dukkanin talikai (s.a.w) ya aiko shi da wannan shari'a wacce gabaninsa ya aiko wasu annabawan da manzanni da ita.
Sakon muslunci sako ne karfaffa kubutacce daga dukkanin jirkita cikin ginshikan sa da asalan sa, yana tafiya kafada da kafada da dukkanin zamani da lokaci, lallai shi sako ne na dukkanin duniya da yake danganta mutum zuwa ga ubangijin sa da makomar sa, sakon muslunci na warware dukkanin matsalolin al'umma har zuwa tashin kiyama. Lallai shi sako ne madawwami, kuma haske ne mai habbaka da bazuwa cikin dukkanin loko da lungunan rayuwa. Yana kuma game baki dayan bangarorin rayuwar duniya da lahira, taken sa na tauhidi ya sauya ya koma zuwa tabbatattun abubuwan ilimi cikin bangarorin da fagen rayuwa, ya shiga cikin tarihin samuwar mutum, ya kuma taimaka cikin kera shi da halaittar jama'a sabuwa ma'abota wayewa da cigaba cikin ilimansu da fannoninsu da rayuwarsu mai habbaka, kufan sakon muslunci mai matukar tasiri bai takaitu ba cikin gina wannan al'umma abar jin kai, bari dai ya mika karkashin sa domin al'umma ta kasance mai karfi da tasiri cikin dukkanin duniya kan doran hanyar tarihi a karkashin sa.
Shi sakon muslunci shi ne samfuri na karshe daga sama, shi ne karshen tsari da hanyar ubangiji da cikamakin sa ga annabta da take karfafawa da tabbatar da cigaba da mikewar sakon muslunci tsawon zamanunnuka masu zuwa, kamar yanda sakon muslunci ke kore bayyana wata annabtar sabuwa daban a dandalin duniya.
Sakon muslunci madaidaici ne cikin dokokin sa da hukunce-hukuncen sa, yana daukaka kan dukkanin sakonnin sama da suka gabace shi, domin yana dacewa da tsarin lafiyayyar halittar dabi'ar mutum da hankalin sa madaidaici, yana bude dukkanin sasannin sa tun daga zanin shimfidar da aka haifeshi har zuwa kabari, alheri da arziki da farin ciki da ni'imtuwar rayuwa  da rayuwa mani'imciya ga dukkanin wanda ya dabbaka shari'ar muslunci a aikace cikin rayuwar sa da sulukinsa da tunaninsa, duk wanda ke san yin bincike da tabbatarwa kan addinai da mazhabobi da sanin lafiyarsu da gano gaskiya daga cikinsu to wajibi kansa da farko ya fara da bincika addinin muslunci, domin cewa da hukuncin lafiyayyen hankali bincike da dandakewa da ya gabata yana wadatarwa daga wanda zai zo daga baya bawai akasi ba.
Kamar yadda ya wajaba kan dukkanin musulmi wanda yayi imani da sakon muslunci da ya san musluncin sa hakikanin sani, ya koyo hukunce-hukuncen sa da dokokin sa, ya nemi samun fahimta cikin addini hakan na daga kamalar sa bari dai kamalar dukkanin kamala kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja daga shugabanmu Abu Jafar imam Bakir amincin Allah ya kara tabbata gare shi:      
«الكمال كلّ الكمال : التفقّه في الدين ، والصبر على النائبة ، وتقدير المعيشة »  .
Kamalar dukkanin kamala su ne: neman fahimtar addini, hakuri kan musiba, yin tsakatsaki cikin al'amuran rayuwa.

Mun yi imani hakikar imani da cewa lallai addini wurin Allah shi ne muslunci cikin kur'ani mai girma wani lokacin ana kiran muslunci sai a nufi ma'ana mafi gamewa wanda shi ne addinin dukkanin annabawa tun daga annabi Adam har zuwa cikamakin annabwa (s.a.w) wannan addini daya daga wajen wanda yake shi daya ne rak tal shi ne sallamawa Allah matsarkaki, addini wurin Allah shi ne addinin muslunci, makasudi cikin wannan aya mai daraja:
 (إنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللهِ الإسْلامُ )
Lallai addini a wurin Allah shi ne muslunci.
Shi ne muslunci da ma'ana mafi gamewa, a wani karo kuma akan amfani da Kalmar islam cikin kur'ani a nufi kebantacciyar ma'ana da ita, wacce shi ne bijiro da addinai da shari'o'in sama daban kamar yahudiyya da nasraniyya, lallai Allah ya hattama annabta da manzanci annabawa da addini muslunci mai karkata ga gaskiya, hakika ya sanyawa dukkanin annabi tsari hanya da shari'a, sai dai cewa ya hattama hanyoyi da shari'o'in sama da shari'ar muslunci saukakka, bai yarda ga wani mutum wani addini daban ba bayan muslunci da kebantacciyar ma'ana, kamar yadda ya zo cikin fadin sa madaukaki:
 
(وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإسْلامِ دِينآ فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ ) ،
Duk wanda ya nemi wani addini bayan muslunci ba za a taba karba daga gare shi ba.
 (اليَوْمَ أكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإسْلامَ دِينآ)
Yau ne na kammala addini gareku na cika ni'imata kanku na yardar muku muslunci a matsayin addini.

Sai ya zama an shafe baki dayan ragowar shari'o'i, ba kuma za a kara karbar wani addini daga wani mutum ba face addinin muslunci da kebantacciyar ma'ana wanda shugaban annabawa cikamakin manzanni Muhammad bn Abdullah (s.a.w) ya zo da shi, wanda shi ne shari'ar Allah ta gaskiya wacce ta hattama shari'o'in annabawan sama, ita ce mafi kammalar shari'o'in sama kuma mafi tsinkayar farin ciki da arzikin mutum, mafi tattaro maslahohi cikin rayuwar su da makomarsu, ita ce mafi dacewa ga wanzuwa tsawon mikewar zamanunnuka, kamar yadda ta zo don ta wanzu ba zata taba canjuwa ba ko sauyawa ba cikin gundarinta da hakikaninta, tana da ubangiji da yake kareta, kamar yadda ya fada cikin bayyanannen littafin sa mai girma:

(إنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا الذِّكْرَ وَإنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ ).
Lallai mu ne muka saukar da Ambato lallai kuma mu ne masu bashi kariya.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: