bayyinaat

Published time: 17 ,November ,2018      09:51:34
Babu kokwanto cewa dukkanin gwagwamaryar da ta ke so ta wanzu ta ci gaba ta kuma taka rawa domin cimma manufofinta, babu makawa sai ta raya wannan ruhi ta kuma wanzar da wannan kyandiri ko fitila.
Lambar Labari: 289
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin kai
Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Ga Manzon Rahama Da Alayensa Tsarkaka

WALKIYAR TSAMMANI (BURI) WACCE BATA GUSHEWA
KYANDIRIN BURI WANDA BAYA MUTUWA.

Wanzar da kyandirin buri a nan gaba da kuma kokarin samun kamala na wannan hanya bisa radadi da jarrabawoyin da wahalhalu ta yadda ya kasance daga cikin abubuwa masu tasiri a wajen wanzarwa da ci gabantar da gwagwamarya da kuma isuwa zuwa cimma hadafofin ta.

Babu kokwanto cewa dukkanin gwagwamaryar da ta ke so ta wanzu ta ci gaba ta kuma taka rawa domin cimma manufofinta, babu  makawa sai ta raya wannan ruhi ta kuma wanzar da wannan kyandiri ko fitila.

Don haka ne za mu samu cewa wannan sakon na Musulunci yana zaburarwa a marhaloli  mabanbanta a kan raya buri da kuma taba haramta yanke kauna da tsammani duk yadda yanayi da wahalhalu da radaid suka kasance. Allah (T) ya ce: "Har sai idan mazanni sun yanke kauna, suka kuma yi tsammanin an karyata sun e, sannan sai taimakonMu ya zo musu, sai mu tseratar da wadanda muk ga dama. Ba a iyakawar da azabarmu daga mutane masu laifi…”. Allah (T) ya ce: "Shin kun yi tsammanin shiga Aljanna alhali irin abinda ya sami magabatan kubai same ku ba? Musiba da cututtuka su same su, kuma an girgiza su har said a manzo da wadanda ke tare da shi suka ce yaushe ne taimakon Allah zai zo? (Ku saurara) lalle taimakon Allah makusanci ne”.

Hakika mason Allah ya kasane yana Magana akan mafi tsananin jarrabawa tare da sahabbansa. Yana yi musu alkawarin bude kasar Kisra da Kasa’ir kamar yadda tarihi yake bada labari a waki’ar Uhudu da Ahzab.

A yayin da makiya Musulunci da munafukai da wadanda suke da ciwo a cikin zuci suke kokarin jefa shakku da kuma sanya yanke tsammani a cikin zukata domin su cimma manufofinsu kamar yada surar Ahzab ta ke Magana akan hakan – domin da zarar fitilar nan ta buri ta bice kuma debe kauna ya soma rarrafowa cikin zukata, za su sami dammar cimma burinkansu na –kamar yadda surar Ahzab ta ke Magana akan hakan domin da zarar an bice buri kuma yanke kauna ya sami mazauini a cikin zukata, Dan Adam zai yi saranda ya kuma mika wuya a gaban wahalhalu, sai ka ga burin ya canza izuwa makami mai kisa.

Kuma shi yaki na ruhi a koda yaushe ya fi kokarin cimma babban burinsa wanda shi ne bice asalin buri da kawar da shi daga cikin tunanin Dan Adamtaka.

Hakika Ahlulbait (AS) sun magance wannan bangare ta hanyoyi mabanbata daban-daban. Wadanda za mu iya ganin wasu daga cikin su a nukudodin da suka gabata, duk da cewa mafi muhimmancin nukuda ita ce gina al’umma ta gari. A wannan bigire wannan na nufin al’amarin sauraron bayyanar shugaba tsayayye (tsayayyen shugaba) ta yadda imamai (AS) a yayin Magana akan sa ba su isu da yin tsokaci akan wannan hakika da kuma neman mabiyansu su yi imani da ita kawai ba. A maimakon haka sun kasance a koda yaushe suna yin sa’ayi domin ganin shi;arsu suna rayadda lamarin sauraro na hakika domin bayyanar imam na hakika domin bayyanar imam da kuma  tsayawarsu a cikin zamuna mabanbanta. Kai! Har ma a lokacin/zamanin imaman su kansu ta yadda mabiyansu sun kasance suna rayuwa cikin tsammanin yiyuwar kowane dayansu ya zama shi ne shugaban da zai tsaida adalci. Lamarin da yak e tabbatar da al’umma ta gari ta samu kwarin guiwa na ruihi wanda yake motsa su kuma ya zama babban buri a wajen tabbatar da nasara da hadafofi da kuma cin galaba akan yanayoyin zamantakewa marasa kyau da kuma kasancewar akidojin da kyawawan halaye.

Duk da cewa wannan tsokaci ya kasance yana da wasu yanayoyi marasa kyau a cikin rayuwar al’umma ta gari. Kamar yadda ya faru a lokacin wasu imamai (AS) yayin da  wasu suka yi imani da cewa shi ne imami tsayayye, saboda haka sai ya zama da wuya zukatan wadannan mutane su gamsu da cewa wannan imamin ya rasu. Daya daga cikin wadannan misalan shi ne imam Musa dan Ja’afar Al-kazim (AS), domin motsinsa na siyasa ya yi karfin day a sa wasu daga cikin mabiyansa sun yi imani da cewa shi ne tsayayyen imamin da ya tsai da al’amari. Don haka yayin da ka kashe shi ta hayar guba a cikin kukuku, sai  wadannan sahabbai basu gamsu da rasuwarsa ba. Wannan ya sa wasu suka fara cewa imamanci yak are daga kansa. Sai matsala ta faru bayan wafatinsa tsakanin al’umma ta gari, ta yadda suka kasu izuwa wanda ya yi imani da imamancin Aliyu dan Musa Al-Ridha (AS) da kuma wadanda suka tuke akan imam Al-Kazim (AS) har zuwa lokacin da imam Ridha ya cimma nasara a kan fitinar. Sai dai wandannan alamomi marasa amfani nan da nan suke gushewa, kuma imamai (AS) suke samun galaba a kanta saboda ikon da suke da shi wajen gamsarwa da kuma yadda gaskiya ta ke zama a sarari a gefen su. Kuma sai ka ga kyakkyawan tasiri shi yake jagoranci a tsakankanin jama’a.

Bisa wannan asasi ne sauraro ya wayi gari a matsayin ibada, wacce take daga cikin mafifitan ibadu –kamar yadda ya zo daga manzon Allah (SAW) –wadanda ‘ya’yan al’umma ta gari suke yi, suke kuma matsawa bisa tushenta. Daga nan sai aka wayi gari bisa shimfida kyakkyawa don bayyanar da daya daga cikin dalilai maus tasiri wajen matsowa don tsaida hukuma ta adalci na saki-ba-kaidi a tsawon tarihin wannan jama’a.

Ta yiwu lamarin imam Mahdi (Allah ya gaggauta bayyanarsa), bayan haka tana kunshe da karfafwa akan abubuwan da suka kebance shi da kuma yadda sauraron say a kasance a cikin boyuwar sat a gajeren lokaci da kuma ta dogon lokaci, suna da tasiri mai girma a wannan bangare na imani wanda wannan jama’a ta banbanta da shi.

Wannan alamomin suna daga cikin abinda bama ganin su kuma bam u san sub a a gurin sauran jama’u na Musulunci, ba don ba su yi imani da imam Mahdi (AS) ba, domin wannan lamari yana daga cikin wadanda al’ummar Musulmi suka hadu a kansa. Kuma ba daya daga cikin su da aka yi sabani da shi akansa. Kadai banabcin shi ne a wajen karfafawa da mumarasa da kuma daure kawuka (hada alakoki) akan wannan lamari. Haka nan ma lamarin yin imani da samuwar imam Mahdi da rayuwarsa Allah ya gaggauta bayyanarsa madaukakiya, ba za ka taba samun sa bisa wannan gwargwado da wannan yanayi a cikin rayuwar Musulunci ta sauran jama’u ba.

A wannan matsayi ya kamata mu yi nuni a tsakaice izuwa lamarin imam Mahdi (AJ) da kuma tasirin tan a ruhi da imani.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: