bayyinaat

Published time: 02 ,February ,2017      07:43:59
Auren mace fiye da daya zuwa hudu yana karya zuciyar mata sai su daina aikin gida, su nemi daukar fansa da kin kula da tarbiiyar yara, kai suna iya neman wasu maza sai su shiga ha’inci, zina, fasikanci, da barnar dukiya. 2-Auren mata hudu ya saba wa dabi’ar halitta domin ta tanadar wa kowane namiji mace daya ne shi ya sa yawansu yake kusan daidaita. 3-Auren mace fiye da daya zai kwadaitar da maza bin shwa’awa da zari, da son zuciya. 4-Auren mace fiye da daya ya saba wa shi kansa musulunci domin an ce: Namiji yana da ninki daya ne kan mace a gado da shaida da sauransu, me ya sa a aure har hudu ba biyu ba?
Lambar Labari: 29
Mutum makiyin abin da ya jahilta ne, duk sa'adda wasu jama'a suka jahilci wani abu to zasu ki yi masa adalci, a kan haka ne yammacin duniya da ya jahilci hikimar dokar halaccin auren mace fiye da daya sai ya shiga soke-soke kan lamarin. Akwai wasu irin wadannan soke-soken da wasu masu kin dokar musulunci ko jahiltarsa suke yi, da wasu matsalolin da musuluncin kansa bai yarda da su ba amma suke jifan musulunci da su, mu a nan zamu yi kokarin amsa wasu daga ciki a kan mas’alolin kamar haka. Wadannan soke-soken sun hada da cewa;

1-Auren mace fiye da daya zuwa hudu yana karya zuciyar mata sai su daina aikin gida, su nemi daukar fansa da kin kula da tarbiiyar yara, kai suna iya neman wasu maza sai su shiga ha’inci, zina, fasikanci, da barnar dukiya. 2-Auren mata hudu ya saba wa dabi’ar halitta domin ta tanadar wa kowane namiji mace daya ne shi ya sa yawansu yake kusan daidaita. 3-Auren mace fiye da daya zai kwadaitar da maza bin shwa’awa da zari, da son zuciya. 4-Auren mace fiye da daya ya saba wa shi kansa musulunci domin an ce: Namiji yana da ninki daya ne kan mace a gado da shaida da sauransu, me ya sa a aure har hudu ba biyu ba?
Amsar Sukan Farko
Amma cewar; Auren mace fiye da daya zuwa hudu yana karya zuciyar mata sai su daina aikin gida, su nemi daukar fansa da kin kula da tarbiiyar yara, kai suna iya neman wasu maza sai su shiga ha’inci da zina, da fasikanci, da barnar dukiya!. Mu sani cewa musulunci yana gina al’umma da tarbiiyantar da ita bisa asasin rayuwa na hankali ne bai kebanta da soyaiya ko kiyaiya ba , musulunci yana bin tsarin dokokin rayuwar al’umma na hankali ne, sai dai wannan ba ya nufin ya mance da halin bukatun mutum na zuci da na jiki ba. 
Tarbiiyar da mata suke tashi da ita a wadancan nahiyoyin na masu sukan ta saba da wacce musulunci ya yi wa musulmi shi ya sa suke kawo irin wannan suka. Domin a al’adunsu mace ba ta da tunanin cewa ba ita kadai ce zata iya zama matar aure a gidan mijinta ba, don haka ne yammacin duniya yake kiran auren mace sama da daya ha’intar ta farko ne, wannan kuwa yana nuni zuwa ga al’adar yamma ne ba duk kasashen duniya ba. 
Rushe wannan dokar ta halaccin yin auren sama da mace daya ya haifar musu da bin mata sake, sai ka ga namiji yana bin mata yana bin sha’awarwsa ga muharrama, da budurwa, da bazawara, da mai aure, da maras aure. Da wahala a kirga mutum dari a samu kashi biyar cikin dari da ba su yi haramtarciiyar mu’amala da mata ba a rayuwarsu, wannan kuwa ko namiji ko mace. Ba su tsaya nan ba har sai maza da maza, mata da mata, suka yi kawance da juna, daidai ne suke tsira daga abota da wasu matan alhalin suna da aure, har al’amarin ya kai ga majalisosin turai suna mayar da luwadi bisa doka, yanzu ana maganar shin dan shekara sha shida zai iya rijista a kungiyar luwadi da madigo ko kuwa?. 
 Amma abin takaici matan ba sa damuwa da jin zafi da zogin abin da yake faruwa fiye da idan an ce mijinsu ya yi aure ne, a nan ne zaka ga kotu da hukuma sun tsananta har da gidan sarka. Sai ya zama sakin jiki don kece raini da wasu matan bai zama abin muzantawa ba, matan da kansu suna ganin maza na yin wannan mummunar alfasha amma ba sa damuwa sosai, haka ma namiji yakan san cewa matar da zai aura ta kusanci mazaje masu yawan gaske amma yana alfahari zai auri matar da kowa yake so da farin jini kuma shi ya ci nasara. 
 Da yawa wannan sabanin ala’dun sun sanya rayuwar mutanen wasu kasashe da suka yi hijira zuwa yammancin duniya ta tsananta; da zaka binciki rayuwar mutanen gabas na kasashen musulmi da suka yi hijira zuwa yammancin duniya da ka samu bakar wahalar da suke sha saboda tsoron lalacewar tarbiiyar ‘ya’yansu mata, domin abin da ake gani lalacewa a yamma sau da yawa wani lokaci yakan saba da abin da ake kira da lalacewa gabas ta Tsakiya. 
 Haka nan da suke cewa mace zata yi daukar fansa ko ta bar aikin gida ya lalace wannan ma ya taso ne daga abin da muka yi nuni da shi na bambancin al’ada. Bambancin ala’adu ne suka sanya 'yan mata suke da tarbiiyar musulunci kafin su yi aure suna da siffa ta kamewa ne duk da kuwa halittarsu ba ta saba da ta matan yamma ba, sannan ba sa ganin miji nasu ne a bisa tilas su kadai, don haka fushi don an yi mata kishiya da daina aikin gida bai taso ba a gun ta sai dai bakin cikin hakan. 
Haka nan idan sun yi aure suna kiyaye dokokin da Allah (s.w.t) ya gindaya musu na kamewa domin suna da tunanin samuwar Allah, da Lahira, da Hisabi, da Wuta, da Aljanna, da ya dasu a tunaninsu da imaninsu. Mun san cewa akwai tasirin al'ada da akida a kowace al'umma, tunanin mutum da aiyukansa suna dansasa daga rabar al'ummar da yake rayuwa cikinta ne. 
 Sannan matar da ake aura ta biyu da ta uku da ta hudu duka ba bisa tilas ba ne duk da yardarsu da zabinsu ne, domin a musulunci auren tilas ba aure ba ne, don haka ke nan idan kuna yi ne da sunan sukan musulunci ko nemar wa mata ‘yanci to su ba su gode muku ba domin ba da yawun su ba ne. 
 Yawanci ba abin da yake sa mace rashin son zama su biyu ko sama da haka sai tunanin cewa idan wata ta zo ba mamaki a wulakanta ta. Bincike ya nuna mafi yawansu abin da suke tsoro ke nan. Abin da suke tsoro na biyu shi ne; Kada ‘ya’yan waccan su zama abokan gabarsu, abin da aka sani da ‘yan uba, lamari ne wanda da an yi tunani da abu ne na kaunar juna da karfafa soyaiya da gina al’umma ta gari. Kuma a nan iyaye mata ne ya kamata su taka babbar rawa domin gyara. Hanyar renon ‘ya’yan juna da kula da su, zata iya zama muhimmiya wurin daidaita wadannan lamurran, kuma suna daga cikin hanyoyin gina al’umma mai tunani, da hankali, da ci gaba, a gida mai mace sama da daya. 
Sannnan idan aka samu namiji yana bukatar karin mace sakamakon rashin samun kintsi da tattali da yake fuskanta daga matarsa, rashin tsafta, kasala, rashin haihuwa, rashin isuwa da daya, duk ya za a warware matsalar?. Ko da yake ba muna cewa warwarar kowace matasala shi ne namiji ya kara aure ba, domin wasu kan yi wannan kusukure ba tare da koma wa masana kan al’amarin iyali ba. Wani lokacin ma sai amarya ta zo da matsalolin da suka fi na uwar gida muni. Don haka lamarin yana bukatar kowa ma kwararru da masana don warware matsalar. Wani lokaci wasu matsalolin magani da likita ne warwarsu amma suna iya kaiwa ga saki ko karo wata matar!. 
 Sai dai masu sukan sun dogara da abin da yake faruwa ne a gidajen musulmi, sun duba sun ga wasu gidajen musulmi ne da zaka ga namiji yana da mata masu fitina da rayuwa maras dadi, da hassada tsakaninsu, maimakon so ya cika gida sai ya koma gaba, tausasawa ta zama tsanantawa, ba tausayi, ba rahama, ba so, ba zaman lafiya tsakanin miji da kishiyoyin. Maimakon ya zama hutawa sai ya yi zafi ya zama gidan azaba, da gaba, da bakin ciki, da wahala. Ga uba da ‘ya’ya duk rayuwa ta gurbace, dadin rayuwa ya tafi, wani lokaci ana ma iya kashe juna, al’amarin har ma tsakanin ‘ya’yan wannan da na waccan. Sai dabi’un al’umma su lalace, kashe-kashe, sace-sace, fashi, alfasha, saki, aurace-aurace, da tsaface-tsaface duk su yawaita. Sannan maza su koma babu wani abu da suka sani sai su dandani wannan su koma kan waccan. Wasu matan kuma su kama neman wasu mazan saboda takaicin rayuwa. Suka ce: Ba komai a cikin irin wannan rayuwa sai kawo tabewar mata da adadinsu ya kai yawan rabin wannan al’umma. 
 Sai dai tambaya a nan ita ce: Wa ne wuri ne kuma wadannan kasashe ne ma’anar aure ta kusa tafiya baki daya ta kusa fadawacikin sharar kwandon tarihi?!Sannan Wane waje ne a duniyar nan ya fi yamma lalacewar al’adu da dabi’a ta yadda mace ta zama kayan cimma buri da ha'inci ga miji!?. Na farko; Bincike ya nuna cewa sau da yawa wasu matan yammacin duniya suna son auren mazaje musulmi musamman daga arewacin Afrika da sauran yankunan kasashen musulmi da suke hijira zuwa yamma domin su kafa gida mai inganci da zai amsa sunan gidan aure sakamakon cewa yanzu a yammacin duniya an sami yawaitar komawar darajar aure matsayin abota kawai. Kuma idan muka duba lamari na biyu zamu ga cewa; Abin da kuka fada kamar yadda yake faruwa ga mai mace sama da daya yana faruwa ga mai mace daya. Duba ku gani kasashenku da suka fi ko’ina saki a duniya amma wannan ba don suna auren fiye da mace daya ba ne, misalin Amurka da saki ya fi ko’ina yawa a duniya, a cikin kasashen musulmi kusan Farisa da Turkiiya suna sahun gaba, amma wadannan kasashe ba safai ake auren mace sama da daya ba. 
Duba jadawalin sakamakon saki a Duniya a 1998 kasa ta daya Amerika 4. 3. Sannan Rasha 3. 4. Sai Ingila da Austaraliya 2. 9. Sannan Kanada 2. 4. Sannan Jamus 2. 3. Sannan Faransa 2. 0. Sai Japan 1. 9. Sai Masar 1. 1. Sai Thailand da Spain 0. 9. Sannan Barazil 0. 6. Sai Turkiiya da Italy 0. 5. Sai Meksico 0. 4. Sannan Clombia 0. 1. sannan sauran kasashe su biyo baya . Muna iya gani a wannan jadawalin babu wata kasa da ake auran mace sama da daya, sannan kuma kasar musulmi daya ce a ciki da ta zo ta tara, da wata kuma da ta zo ta sha uku. 
Sannan a wadannan kasashen masu sukan mace takan zama mai miji amma tana neman wasu, haka ma mijin yana da mace amma yana da mata masu yawan gaske da yake mu’amala da su, amma irin wadannan mutane suna da bakin magana da sukan musulunci don yana halatta yin auren mace sama da daya. 
Sannan kuma a ina ne aka fi kashe-kashe marasa dalili a duniya da ya kai irin na kasashen yamma, yi bincike kan adadin kashe-kashe ko fyade a duniya ka ga a wasu kasashen duk ‘yan mintina ana yi wa mace fyade. A Amurka a rahoton FBI kafin shekara ta 1987 ya tabbata cewa: A kowane minti 22 ana kisa, a kowane minti 5 ana fyade, a kowane sakan 49 ana sata, a kowane sakan 30 ana kai hari da makami, a kowane sakan 10 ana fashi . Ashe ke nan matsalar ba don auren mace sama da daya ba ne
Sannan Mutum nawa ne a aikace suke da mace fiye da daya a cikin musulmi, idan muka duba sosai a kasashen musulmi zamu samu cewa wadanda suke da mace sama da daya idan an kwatantansu da masu mace daya ba su wuce ishirin cikin dari ba wannan kuwa yana nuna nisan tazarar da take tsakanin wannan adadi guda biyu. 
Sannan ka da mu manta cewa auren mace fiye da daya bai kebanta da musulmi ba, akwai ma’abota addinai da al’adu masu yawa a duniya da musamman wannan ya kasance daya daga al’adunsu kamar tsofaffin addinan kabilun Amurka na farko. 
Amsar Suka Na Biyu
Suka ce: Auren mata hudu ya saba wa dabi’ar halitta domin dabi’ar halitta ta tanadar wa kowane namiji mace daya ne don haka ne yawansu yake kusan daidaita. Sai dai idan mun duba zamu ga cewa dabi’ar adadin halittar namiji da mace a yawa da adadi bai tabbata ba kamar yadda muka yi bayanin hakan a farko. Sannan mu ba mu cire Allah cikin maganar tsarin samar da halitta da adadin maza da ya dace da mata ba, domin Allah (s.w.t) yake halitta kuma ya tsara ta ba kamar yadda kuke kawowa ba. Sannan ku lissafa mata da mazan kasarku ku gani su wa suka fi yawa, idan kun ga mata sun fi yawa to ku tabbata maganarku game da halitta ba daidai ba ce. 
Kuma muna iya karin bayani kan haka da cewa: Balagar tunani da isa aure yafi sauri ga mace a kan namiji musamman a wasu yankuna da mace ‘yar shekara tara take isa aure amma namiji ba ya isa sai shekara ta sha shida wanda su ne shekarun da musulunci ya yardar masa yin aure. Sannan bincike ya nuna mata sun fi maza dadewa da tsawon rai wanda ya sanya adadinsu kan fi yawa. Haka nan dabi’ar haihuwa ga namiji ta fi dadewa, domin yawancin mata suna daina haihuwa ne a shekara hamsin amma namiji yana iya kai shekara dari, wannan kuwa yana nufin ba abin da zai hana namiji yin aure domin a samu ci gaba da haihuwa idan da bukatar haka. 
Sannan kuma bala’oin da suke rage al’ummar kasa sun fi shafar namiji kamar yaki, idan ka yi kokwanto bincika kasashen da suka samu yakoki ka samu bayani. Bincike ya nuna mata sun fi maza yawa a irin wadannan kasashe, sai ka ga mata sun kai shekara talatin zuwa arba’in kai wata har ta mutu babu miji, kuma ga wasu masu yawa da mazansu sun mutu amma saboda al’ada sun kasa samun yin wani auren. Ta haka ne matsaloli suka yawaita, ko dai su yarda da auren mace fiye da daya su jefar da al’ada, ko dai ya zama an ci gaba da zama haka nan wasu matan suna gani su mutu da bakin cikin rashin miji. 
Misalin malama Nadir da ta rabu da mijinta kuma ta samu mai aurenta sai dai magidanci ne sai ‘yan ajinsu suka ce: Ai irin wannan mata su hakura kawai, ai Allah daya ne mace ma daya ce . Sai na ba su amsa da wadannan dalilai da na kawo a sama. Bayan an tashi daga aji ne sai ta yi ta godiya ta ba ni labarin takaici da ke zuciyarta na ganin sauran mata da mazajensu amma al’ada ta tsananta a kan rashin yarda da auren mace sama da daya, ga shi kuma an tsananta mata a kan ba za a yarda ta zama ta biyu ba a gidan mijinta, hada da maganar cewa ita bazawara ce. Ta ce: Maganar ta karfafe ta auren mai mata, ai ita za ta yi wa kanta zaman. 
Haka ma ya taba faruwa a Jamus mata suka nemi auren mace fiye da daya ya zama doka don ga sunan da yawa ba aure, amma Gwamnatin ta matsa wa coci kada ta yarda da haka, aka yarda da zina da fasadi ya yi yawa maimakon auren mace fiye da daya .
Amsar Suka Na Uku
Suka ce: Auren mace fiye da daya zai kwadaitar da maza bin sha’awa da zari, da son zuciya. Sai dai abin da yake faruwa akasin abin da suka fada ne, domin aurar mace sama da daya yana sake kaiyade namiji ya yi masa iyaka da su ne kawai, da nisantar wasu matan daban, don haka ne a nan shari’a ta iyakance namiji don gudun yawace – yawace barkatai gun mata marasa kamun kai, domin shari’a ba tana kwadaitar da bin sha’awa ba ne, abin da take so shi ne sanya dokoki domin ka da a kai ga fasadi, don haka aka bayar da hanyar warwara ga dan'adam. 
Abin da ya tabbata shi ne; Galibi namiji ya fi mace saurin sha’awa, sau da yawa mace idan ta rayu a tarbiiya sai wannan tarbiiyar da kunyar su taimaka mata nisantar namiji sosai, amma namiji sai dai ya rike kansa domin sha’awarsa tana kusa. Haka ma ba safai yake mallakar kansa ba, shi ya sa daga hikimar Allah ya ba shi damar auren mace fiye da daya don kada ya yi tawaye ga hankalinsa ya bi sha’awarsa, sai a ka ba shi damar tara mata a gidansa don ka da ya kai farmaki da sha’awarsa wajajen fasadi. 
Kafin a sami namiji da yake kin matarsa a shimfida an samu mata masu yawa da suke hakan, shi ya sa Kur’ani mai girma a maganar Nushuzi  bai yi maganar namiji ba sai mace yana mai cewa: "…Wadannan (matan) da kuke jin tsoron kaucewarsu ga shimfidarku…” . Amma mace sau da yawa takan ki mijinta a shimfida, a kan haka ne shari’a ta ce: Idan ta ki shi sai ya yi mata nasiha, … sai kaurace mata a shimfida, … sai ladabtarwa. 
Wadannan dokoki shari’a ta gindaya su ne domin maganin fasadi da hana kai wa ga zinace-zinace, wannan ne ya sanya shari’a ta saukaka wa mutane kuma ta bayar da mafita ga sha’awarsu, ta shar’anta yin auren mace fiye da daya ko auren mutu’a . Shi ya sa Allah ya sanya haddi ga zina don babu laifin da yake da haddi sai da ya bayar da mafitar da zata hana aikata shi, In ba haka ba yaya Allah zai sanya haddi kan abin da mutum ba zai iya ba!?
Sa’annan mace duk wata tana haila, wata matar tana haila kwana bakwai a kowane wata, sannan idan ta samu ciki wata tara ba ta shawar namiji sai kadan. A wannan yanayi wata tana yarda da shi ne saboda ka da ta saba umarnin Allah, kuma idan ta haihu tana shayarwa a tsawon shekaru biyu ba safai ta damu da namiji ba. Sannan rashin lafiya da tayiwu a shekara kwana talatin ba ta da lafiya, ko ta yi tafiya, ko ziyarar iyaye da yan’uwanta, hada da aikace-aikacen gida da kan iya wahalar da ita kullum. Saboda haka a shekara hudu sai ka cire kwana bakwai na haila a kowane wata, sannan ka cire shekara biyu na shayarwa ga wata tara na ciki!. Koda yake ba dole ba ne kowace mace ta zama hakan, sai dai muna magana kan dabi’arta ne. Amma namiji shi ko da yaushe a sake yake, kuma yana iya samun baiyanar sha’awa matukar ya huta ko hankalinsa ya kwanta. 
Akwai wasu jama’a da suka yi kokarin kauce wa sha’awarsu da yakar ta, amma sai ga irin wadannan mutane sun zama manyan maciya amanar al’umma, su ba su bar mace kowace iri ce ba har matan aure, wannan kuwa jama’a ce da ta kirkiro Rahbaniyanci (kebewa don ibada). Haka ma wasu suka kirkiro shi a musulunci amma kamar yadda fada-fadan coci suka kasa kiyayewa su ma haka nan suka kasa. Duba ka gani mana a Amurka shekarar 2002-3 kaga irin abin kunya da ya faru a coci-coci har ma aka sallami wasu daga malaman coci saboda abin kunya. Haka nan ka duba kasashenmu ka bincika ka sha labari da mamaki a kan rayuwar wasu masu Sufanci da yakar sha'awar da Allah ya halitta a tare da su ka ga kasawar mafi yawancinsu. 
Akwai mai ganin sai ya yi ta yin azumi ya hakura ya kaurace wa sha’awarsa. Sai aka ce da shi: Don Allah in ka kai azumi ka sha ruwa ka huta yaya kake ji? ya ce: Wallahi shi wani lokaci yana kara jin sha’awa. Aka ce: To me ya sa kuka ce: Ya yi azumi? Sai suka ce: Akwai hadisi. Sai aka ce: Wasu malamai sun tafi a kan cewa ba haka ne manufarsa ba, domin wanda aka danganta hadisin gare shi ya yi aure kuma ya yi azumi. Azumin tasirinsa shi ne lokacin da kake cikin yunwa ba lokacin da ka sha ruwa ka huta ko a kwanakin da ka daina yin sa ba, ko ba komai ma'anar da wasu suke fassarawa ta yi karo da Ayar Kur’ani. Domin a watan azumi ne suke zuwa ga matansu da dare a lokacin Manzon rahama (s.a.w), sai aka saukar da aya cewa: "…Allah ya san cewa hakika kuna ha’intar kawukanku… a yanzu ku zo wa matanku… ” . Sai aka halatta musu zo wa matansu da dare, sai dai wannan ba ya hana yin tasirin azumi wurin kashe sha'awa ga wasu mutane matukar sun dimauci yin azumin. 
Musulunci ya sanya wadannan dokoki don yana son rayuwa da tsarin hankali da zai kai mutum zuwa ga kamalarsa tun daga nan duniya har lahira. Yana son nuna wa dan'adam hanyar da zai taka don kaiwa ga waccan kalamar ta ainihi a gidan dawwama na lahira. Don haka wanda lissafinsa yana kallon duniya ne kawai ba zai iya fahimtar hikimar Allah (s.w.t) a cikin dokokinsa ba. 
Siffofin Namiji Da Mace
Namiji nagetib ne ita kuwa mace pozitib ce saboda haka nagetib yana iya karbar komai aka zuba masa, shi ya sa ma sakamako dole ya bi shi kamar yadda yake a ka’idar Mantik. Amma mace pozitib ce tana da iyaka saboda haka ne ma dole shi ne za a iya ba damar auren mace sama da daya, dalili kuwa shi ne: Nagetib yana da karfin tafiyar da komai wanda shi pozitib ba shi da shi, shi ya sa siffofinsa suka fi karfi da rinjaye. Da nagetib ana iya gane dan waye ba da pozitib ba, shi ya sa da mace za ta zo wa namiji biyu ba yadda za ta iya sanya su daukar ciki, kai ko da sun kai maza dubu ne ba ta iya yi wa ko dayansu ciki balle ta tara ‘ya’ya da zuriya da zasu iya dangantuwa zuwa gare ta. Da an kaddara gida da maza hudu da mace daya a matsayin mijinsu, da abin ya zama sabanin dabi’ar dan'adam, a wannan yanayi lamarin yakan zama abin mamaki ga dan'adamsaboda sabawarsa ga dabi’ar halitta. Sannan kuwa yaya za a gane danta, don haka tambaya ita ce danta na waye a cikinsu? Idan gane shi ba zai yiwu ba wannan yana nufin haifar da al'umma maras tabbacin asali, kuma yana nufin samar da al'umma mai rashin tausayi da jin kai, da neman daukar fansa kan al'umma ke nan. Da hakan zai kasance da fitina da fasadi mafi girma sun faru a tarihin dan'adam. 
Nagetib shi yake iya juya al’amuran al’umma don yana iya dauke nauyin Duniya a kansa amma pozitib yana da iyaka kuma yana da rauni, kuma ya doru ne kan waninsa sai abin da aka ba shi, don haka ba yadda za a yi mace ta zama shugaba a kan gida. Namiji shi yake iya daukar yaki da daukar nauyi, kare kasa, tafiye tafiye, sayar da rai, amma mace ita jikinta laushi ne, da kyau, da ado, shi ya sa Jamalul-Lahi (kyawu da adon Allah) ya baiyana a halittarta, kamar yadda Jalalul-Lahi (kwarjinin Allah) ya baiyana a halittar namiji, tsakanin Jalal da Jamal kuwa akwai banbanci domin Jalal nagetib ne mai kunshe da siffofin korewa amma Jamal pozitib ne mai siffofin tabbatarwa . Kasancewar namiji nagetib  wannan ya sanya shi da dabi’ar dandano, shi ya sa ba safai wasu kan iya isa da mace daya ba, amma mace abin da take nema shi ne gamsuwa, in ko ta samu wannan to tana isuwa da namiji daya, haka nan Allah yayi halittunsa bisa hikima daidai da dabi’arsu. 
Idan muka koma a ka’idar mantik  shi namiji jagora ne amma mace mafari ce, ana kuma auna mafari ne da jagora domin samun hukuncinsa. Haka nan aka halicci dabi’arta, shi ya sa take bukatar kariya ta musamman daga namiji da dogaro da shi a abubuwa da dama domin cimma hadafin samar da mu da Allah ya yi, amma shi namiji yakan iya daukar nauyin mata masu yawa a kansa. 
Musulunci ba ya son barin mutum a sake ko a rayuwar gwauranci, sannan yana son yawaita musulmi musamman a wancan lokuta da karancinsu ya yawaita . Saboda haka da masu sukan sun yi tunani da su suka fi cancanta da suka da zargi da suka yardar wa dan'adam rashin iyaka ga sha’awarsa, ta yadda yana iya zuwa ya ajiye sha’awarsa gun wacce ya so a duk inda ya so. Amma masu sukan ba su tanadi irin wadannan dokoki masu hikima da zasu kare al’umma daga fadawa fasadi ba, don haka sai namiji ya jefa ruwansa duk inda ya ga dama, ya shayar da gonar da ba ta sa ba, ya wuce ba kunyar Allah ba ta mutane. Shi ya sa wasu masu ilimin yammacin duniya  suke cewa: "Ba abin da ya jawo mummunan yaduwar fasadi a duniya fiye da hanin da coci ta yi wa auren mace fiye da daya".
Amsar Suka Na Hudu
Amma fadinku cewa: Auren mace fiye da daya ya saba wa shi kansa musulunci domin an ce: Namiji yana da ninki daya ne kan mace a gado da shaida, me ya sa a aure har hudu ba biyu ba? . Da farko muna iya cewa wannan kiyasi ne da ba shi da wata ma’ana, domin kowane fage yana da nasa hukunci a shari’ar musulunci. Don haka lamarin ba kamar yadda kuka fahimta ba ne. Musulunci bai takaita wannan rayuwa ta aurataiya a bisa kiyasin sauran hukuncin rayuwa ba, bai kuma dora asasin dokokinsa bisa kiyasi ba, aure wani abu ne da shari’a ta gina shi bisa asasin hankali da kauna bisa yadda ta ga ya kamata. 
Shari’a ta sanya kowane babi na dokoki bisa sharudansa, gado yana da sharuda, limancin salla yana da sharuda, kuma duk bisa maslaha ne da mai shari'a wanda ya fi kowa sanin dan'adam ya gindaya. Wadannan dokokin ba suna nuna fifikon namiji kan mace ba ne, ko sun fi tausaya masa, ko sun fi sonsa, sai dai suna nuna wasu dokoki ne da suke da nasu sharuda a babobin fikihu. Musulunci ya kafu bisa dokar hankali da maslahar mutum ne, don haka ne ya kafa wadannan dokoki don tsara rayuwar namiji da mace ba don namiji ya fi mace ba. A musulunci ba wanda yafi wani tsakanin namiji da mace sai da tsoron Allah. Saboda haka su dokokin an gina su ne bisa maslahar rayuwar dan'adam ba don wani jinsi ya fi dayan ba. Idan mun duba dokokin musulunci zamu ga babu wani Addini da ya girmama mace irinsa. Da wannan ya kasance domin fifikon jinsi a kan wani jinsin da babu wani ma’auni da zamu iya auna hakan da shi, domin akwai hukunce-hukunce da ba sa hawa kan mace. Babban misali a nan shi ne wajabcin yaki ba ya kan mace amma ba mu taba ganin wani ya ce musulunci ya zalunci namiji ba. 
Hikimar musulunci ta sanya namiji ya iya auren mace fiye da daya ban da akasin haka, da mace zata auri maza da yawa da an rasa nasabar mutane, kuma da an rushe dangantakar mutane da sun koma kamar dabbobi ko mafi muni daga dabbobi don ba mai ganin wani danginsa, ba mai karbar maganar wani da kima kamar yadda zamu iya ganin karancin tausayin mafi yawan mutane ga wanda ba su san nasabarsa ba, hada da wasu hikimomin da muke jahiltarsu a cikin dokokin Allah madaukaki. Tarihi ya nuna cewar idan wanda ba a san nasabarsa ba ya rike shugabancin al’umma sau da yawa takan fuskanci rashin tausayi da bala’o’i masu yawan gaske, don haka ne a kowane abu musulunci yana duba maslahar al’umma don sanya dokokinsa. Wannan ne ya sanya masana masu yawa a yammacin duniya suka yaba wa Tsarin musulunci da shari’arsa.
Musulunci Da Musulmi
Sannan kuma mu sani ba a duba al’adun mutane a yi wa addininsu hukunci da shi, domin musulunci yana da tsarinsa mai kyau, sai dai mafi yawan musulmi ne ba su kiyaye tsarinsa a aikace ba, don haka kuskure ne babba a yi wa addinin al’umma hukunci da al’adunsu. Wannan kuwa ko da malaman wannan addinin ne, ko jagororinsa, ko mabiyansa. Idan ma abin da kuka ce gaskiya ne to sukanku yana hawan kan musulmi ne ba kan musulunci ba, domin da an kiyaye musuluncin, da musulmi ba su fada irin wannan ba. Musulunci ya sanya doka ne da ka’ida, ya dora hukunci da sharuda, kuma ya wajabta yin aiki da su a kan mutane, amma idan mutane ba su kiyaye ba to wannan ba ya zama laifin musuluncin. 
Mutumin da ba zai iya kiyaye adalci tsakanin matansa na aure ba amma sai ya auri sama da mace daya kuma matsaloli masu yawa suka babaye gidansa, wannan matsala ba ta musulunci ba ce ta shi mai sabawa dokar ne, idan da zai kiyaye dokar da ba zai fuskanci irin wadannan matsaloli da sakamakon aiyukansa suka haifar da su ba. Da wani musulmi zai yi kuskure to bai kamata a jingina shi da addininsa ba; Muna da misalai masu yawa kan hakan: Idan wani ya yi saki yana musulmi ba shaidu biyu adalai ba ta saku ba domin a wajan Allah matarsa ce, wannan ita ce mahangar mazhabin Ahlul-baiti (a.s) bisa koyarwar Kur'ani mai daraja. Da wani zai aure ta da ya auri matar wani ne domin Allah (s.w.t) yana cewa: "Ku sanya shedu biyu adalai daga cikinku” . To idan musulmi bai kiyaye wannan ba, ko bai kiyaye sauran sharudan saki ba kamar barin mace sai ta yi tsarkin jini, sai ya sake ta, sai saki ya yi yawa barkatai ba tsari , ba yadda za a jingina wannan da musulunci, idan ya zama musulmi sun saba, sai yawan saki ya faru wannan ba matsalar musulunci ba ce, ta musulmi ce . 
Kamar yadda: Da wani mutum mai auren da ya saki matarsa ya yi zina sai daular musulunci mai jagorancin tsarin musulunci ta kashe shi da jifa don ya taba yin aure, da ya rataya a kan musulmi don an kashe shi maimakon bulala, saboda Allah (s.w.t) bai ce a kashe shi ba, muhsini Allah ya yi umarni a jefe in ya yi zina. Muhsini shi ne wanda Ahlul-baiti (a.s) suka ce: "Yana da farji da yake zo masa safiya da yamma” . Amma ko da yana da aure amma ya kasance ba zai iya saduwa da matarsa ba to wannan ba muhsini ba ne a shari’a. Don haka mai auren da’imi da yake matafiyi idan ya yi tafiya sai ya yi zina ba ya cikin muhsinai, haka ma mai auren mutu’a ba tare da yana da da’imin aure ba shi ma ba muhsini ba ne. Da za a kashe wannan don ya yi zina maimakon a yi masa bulala, da laifin ya hau kan musulmi da daular musulunci ne da suka bar kofar Ilimin Manzonsu saiyidi imam Ali da Ahlul-bait (a.s) suka bi ijtihadodi da suke cike da sabani da kurakurai. Da sun bi kofar da aka ce musu da ba a samu wannan kuskure mai girma ba, kuma da an samu tsari da ba misalinsa a duniya. 
Haka nan: Da mata zata ki dafa abinci sai miji ya doke ta, ko ya sake ta, ko rayuwa ta yi muni a tsakaninsu, da ba laifin musulunci ba ne don Musulunci bai shar’anta duka ba a nan, kuma bai ce dole sai ta dafa abinci ba wajabci na shari’a, domin dafa abinci hukunci ne wajibi na kyawawan halayen musulmi ba na fikihun musulunci ba wanda saba shi zai kai ga wahala da karancin kauna da soyaiya tsakaninsu. Wannan mataki da ya dauka ya saba wa musulunci kuma kuskure ne a shar’ance, kuma tana da ikon bin hakkinta na duka sai in ta yafe masa. Da wannan zai jawo wahala tsakaninsu ba laifin musulunci ba ne laifin musulmi ne. 
Da musulmi ya mayar da matarsa na'urar dafa abinci da wanke yara kawai, sai ya yi watsi da hakkinta na yin karatu, da ya zama laifinsa ba laifin Musulunci ba . Yawancin gurbacewar rayuwa yana faruwa ne sakamakon rashin tsara aiyukan gida da lokuta, da rashin ba wa kowa hakkinsa na lokacin aiki da hidimar gida, tsari wani abu ne da musulunci ya yi wasiiya da shi ga musulmi baki daya . Rashin tsari ne ya sanya matar gida cikin wahala, ba lokacin karatu, ba na ‘ya’yanta, ba na hutawa, shi kuma mai gida lokacinsa gaba daya na hira ne da abokai da kasuwa sai bacci, amma ‘ya’ya da uwar gida ko kadan ba su da nasu lokaci da zasu tattauna da mai gida. 
Da mai gida zai ware; awa 8 don neman abin rayuwa, awa 6 bacci, awa 4 da yara, awa 2 da matarsa, awa 2 hutawa, awa 2 karatu. Amma sai ka ga ya ware awa 7 na bacci, awa 10 kasuwa, awa 7 hirar waje, shi ke nan duk rayuwa haka za ta tafi. Haka ma uwar gida tana iya tsara nata awoyin; a misali ta ware awa 7 hira da aikin gida ne, awa 4 da yara, awa 2 da mijinta, awa 3 karatu, awa 2 hutawa, awa 6 bacci. Haka ma mace tana iya dafa abincin rana da na dare a lokacin rana, da dare sai ya zama ba abin da ya rage mata sai karatunta da kula da na yara, amma rashin tsari sai ya jawo ta rayu cikin wahala ta tsufa ba ta san komai ba har ma wajibi ba ta sani ba. 
Ga maza ma haka ake samun irin wannan rashin tsari da jahilci, har ma wani jahili ya saki matarsa don ya yi baki ita kuma ta dafa danwake, shi kuwa a wajansa danwake ba wani abinci ba ne na burgewa. Wani kuwa yana da jikoki amma ya dauka wankan janaba sai wanda ya saba wa Allah ya yi zina ne yake hawa kansa. Wadannan misalai ne kadan daga cikin masu yawa daga abubuwan da suke faruwa a cikin al’ummar musulmi, sai dai ina wadannan halayen suke da wata alaka da Musulunci!?. Tsakanin wadannan halayen da musulunci ya kai tsakanin sama da kasa. 
Bayan al’ada da tasirinta dole ku fahimci cewa daidaikun mutane ma kowannensu yana da mahangarsa da ta bambanta da ta wani game da mace. Kallon daidaikun mutane ga mace ya sassaba; wani namijin yana ganin mace kamar yadda mai farauta yake ganin kifi ne da zai sanya fatsa ya kama, wani yana ganin mace a matsayin uwa a cikin gida, wani yana ganin mace a matsayin mutum mai kamala mai renon al’ummarta wadanda masu wannan tunanin suna da karanci sosai. Wani yana ganin mace kamar dabba ce da take da jiki irin na mutane kawai kamar yadda mafi yawan mutanen titi suke ganin ta, wani yana ganin mace a matsayin baiwa ce da zaka saya ka sayar da aikinta bai wuce kwanciya da dafa abinci ba kamar yadda mafi yawan masu rayuwar kauyanci da jahilci suke ganin ta, wani yana ganin mace ta fi komai daraja ta fuskoki masu yawa; irin wadannan mazajen sun fi komai karanci. Don haka ne gidaje sukan bambanta kan yadda ya kamata su rayu sakamakon bambancin mahangar da masu gidajen suke da ita game da mace wacce da yawa ta saba da ta musulunci da tsarin da ya zo da shi. 
Da wannan ne zamu ga al’ummar musulmi daya ce a duniya amma al’adu da mazhabobi da ra’ayoyi sun yi tasiri a aiyukansu, kuma sun taka rawa sosai kan yadda rayuwar ma’aurata ya kamata ta kasance, wannan kuwa ba matsalar musulunci ba ce matsalar su musulmin ne!. 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: