bayyinaat

Published time: 17 ,November ,2018      09:58:27
Hakika muminin da yake shudewa bisa radadi da wahalhalu da jarrabawoyi. Ta yiwu wannan abu daga kokwanto ya same shi ko kuma rudani ko kuma rikicewa a cikin hakikanin
Lambar Labari: 290
AL-AMARIN IMAM MAHDI (AJ)

Hakika lamarin imam Mahdi kamar lamarin imam Husain ne, yana da manufofi maus yawa a wajen gina al’umma ta gari a fagen akida da wayewa da kuma imani. Kuma Magana a kai tana da fadi, domin kamar fassara tarihi ne. Fassarar da ta dace da mahangar Al-qur’ani wacce take dauke da ra’ayin gadar da bayan kasa ga bayin Allah salihai. Allah Ta’ala ya ce: "Hakika mun rubuta a cikin Zabura bayan tunatarwa cewa lalle kasa bayi na na gari ne za su gajeta”. Ya ce: "Allah ya yi wa wadanda suka yi imani daga cikin ku kuma suka yi aiki na gari alkawari kuma ya rantse cewa sai ya sanya su halifofi a bayan kasa kamar yadda ya sanya wadanda suka gabace su kuma ya rantse sai ya tabbatar musu da addinin da ya yardarm da shi a gare su. Kuma ya rantse sai ya canja musu da aminci bayan tsoro, sannan su bauta mini baza su sanya wani abokin tarayya tare da nib a”.

Abinda ya shafe mu a cikin wannan bayanin shi ne yin nuni izuwa bangare imani da ruhi bisa gwargwadon da zai taimaka mu fahimci tafarkin imamai a wajen gina bangaren imani (ruhi) na jama’a ta gari, ta hanyar lamarin imam Mahdi (AS).

Hakika lamarin imam Mahdi ta mahangar mabiya ahlul-bait da shi’arsu kamar wani rayayyen jiki ne na tabbataccen tarihin da ambaton sa ya gabata. Ba kawai a matakin nan gaba wacce ba a sauraro ba. Kai! Har ma a matsayin yanzu wanda ake rayarwa wanda ya fara mislata nan gaba ta hanyar samuwar sa madaukakiya da rayuwarsa ta yanzu; domin sun yi imani da rayuwarsa da kuma haihuwar sa. Kuma lalle a yanzu din nan yana rayuwa a cikin wadannan yanayoyi masu wuya, wacce Musulmi suke fuskanta. Kuma yana ganin dukkan tajriba ta Dan Adam da ta zamantakewa wacce Dan Adam ya ke shudewa da ita, yake kai kawo a cikinta, domin kokarin tabbatar da hukuma ta adalci ta Ubangiji ta sake-ba-kaidi a rayuwar jama’a ta gaba.

Ana ganin wannan akida a sarari take a mahangar tarihin Dan Adam. Kuma ana bata fahimta ta sunnar Allah a tarihi wacce Kur’ani ya yi Magana a kanta.

Hakika muminin da yake shudewa bisa radadi da wahalhalu da jarrabawoyi. Ta yiwu wannan abu daga kokwanto ya same shi ko kuma rudani ko kuma rikicewa a cikin hakikanin tabbatattun abubuwa da kuma sunnoni na tarihi wadanda Kur’ani ya yi Magana akan su. Misali, sunnan yin galabar mumini ko kuma sunnar yin galabar gaskiya a kan karya. Allah Ta’ala ya ce: "Kuma ka gaya musu gaskiya ta zo kuma karya ta gushe, hakika karya mai gushewa ce”. Kuma Allah Ta’ala ya ce: "Lalle na rates za mu taimaki manzanninmu dama wadanda suka yi imani a wannan rayuwar ta duniya, haka ma ranar da za a tsaida shedu”. Allah Ta’ala ya ce: "Shi ne wanda ya aiko manzonSa tare da gaskiya kuma addinin gaskiya domin ya bashi nasara akan addinin baki dayansa”.

A kuma misalign sunnar canja wasu jama’u na Dan Adam Allah Ta’ala ya ce: "Yak u wadanda kuka yi imani, duk wanda ya yi ridda a cikin ku daka addininsa da sannu  Allah zai zo da wasu mutane yana son su suna son Sa masu kaskan da kai ga muminai kuma masu daga kai ga kafirai, suna yin Jihadi a tafarkin Allah kuma basa tsoron argin mai zargi. Wannan falalar Allah ce da yake bada ita ga wanda ya ga dama, kuma Allah mai yalwatawa ne, masani”. Allah Ta’ala ya ce: "Idan har kuka bada baya zai canja wasu mutanen da ku ba ku ba sannan ba za su zama kama ku ba”.

Haka ma misalign sunnar fuskantuwar fidira (halittatciyar dabi’ar mutum) izuwa samun kamala da yin imani da Allah ya ce: "Ka tsaida fuskarka izuwa addini kana mai daidatuwa, wannan ita ce fidirar Allah wacce ya halicci (fidirci) mutane a kanta. Ba bu sauyi a cikin halittar Allah, wannan shi ne addini tsayayye, sai dai yawa-yawan mutane basu sani ba”.

Haka nan misalign halifancin da Allah ya ba Dan Adam da fificin sa akan mala’iku a wajen halifanci. Allah Ta’ala ya ce: "Yayinda Ubangijika y ace da mala’iku lalle zai sanya halifa a doron kasa sai suka ce ashe yanzu kasa wadanda za su yi barna a cikinta su zaburar da jinni, alhali ga mu muna tsarkake ka sai ya ce musu na san abinda baku sani ba”.

Al’amarin ci gabantar da sakonni da kuma sako na karshe.

Dukkanin wadan nan sanannu ne da tabbatattun abubuwa za su iya fuskantar wannan babbar tambaya a kwakwalwar mutum mumini yayin da yake gain jin radadi da tarrabawoyi da barna duka sun cika doron kasa. Kuma gaskiya da kyakkyawa ba a aiki da su, sannan kuma ba a yin hani daga barna.

Amma idan mutum ya sa samuwar imam Mahdi (AJ) a gabansa tare da cewa da sannu zai cimma zai tabbatar da wadannan burace-burace da kuma cewa da sannu zai dabbaka hakikanin wadannan a sarari a gareshi.

A gefen dukkanin wadannan zai iya yiyuwa mu sami al’amura na ruhi masu zuwa wadanda suke kunshe a cikin wannan lamari da ya zama matattara ta gina jama’a ta gari.




comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: