bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      14:49:37
Dikkan waxannan ba haram bane saidai harancin kan iya zuwa yadda aka yi cuxanyar, domin musulunci bai yadda da alaqar da zata tayar da shaawa ba.
Lambar Labari: 293
CUXANYA TSAKANIN NAMIJI DA MACE
Musulunci ya tsara yadda al'umma ya kamata su yi cuxanya a tsakanin su, don musulunci ya zo ne domin ya tsarawa mutane alaqar su, tare da yadda zasu tsayar da uta bisa mutunci da amana, adalci,  soyayya, qauna,  kuvutarwa.
Saboda haka ba a haramta cuxanya tsakanin mutane ba sabida zaman ta dole a tsakanin al'umma cikin duk vangarorin rayuwa. Kamar cuxanya cikin jama'a domin neman ilimi, lafiya da ma'aikata.
Dikkan waxannan ba haram bane saidai harancin kan iya zuwa yadda aka yi cuxanyar, domin musulunci bai yadda da alaqar da zata tayar da shaawa ba, ya kuma toshe dukkan hanyoyin da za a bi a kai ga aikata varna, domin duk cuxanyar da zata sanya haxa jiki tsakanin mace da namiji wadda kan iya haifar da sha'awa tsakanin su wannan bata halatta ba.
Bai halatta ba ga mace ta yi tafiya a hanya mai cunkoson mazaje, a nan musulunci ba tafiyar ya haramta ba, cuxanyar da zata yi da maza ce abin lura, domin hakan kan iya haifar da shaawa.
Manzon Rahama (SAW) ya ce : (ba komai ga mata don sun yi tafiya a kan hanya, sai  dai su bi gefen katanga da hanya)1
Musulunci ya hana cuxanyar da zata jawo fitina da fasadi, amman ba wai kowace cuxanya ba. An gudanar da bincike a makarantar da ake cakuxa maza da mata, inda sakamakon haka aka samu mafi yawan 'yan mata da samarin makarantar sun qulla alaxa mummuna a tsakanin su, wanda sakamakon haka ya raunana matsayin karatun su, sabida shagaltuwar su da lamarin soyayya vatacciya, don haka musulunci ya tsara cuxanya tsskanin namiji da mace, sabida kaucewa faxawa cikin varna, misali : an haramta kaxaita tsakanin namiji da mace balgaggu, domin zai zama mafarin afkawa cikin qulla mummunaar alaqa ne.
Abin nufi da kaxaita shine : zama xaki ko gida xaya a kulle su biyu, ta yadda zai kasance sun kaxaita da juna ba tare da samun na ukun su ba, irn wannan kaxaitar galibi tana jawo mummunar alaqa, Manzon Rahama (SAW) ya kasance ya hana irin wannan inda ya ke cewa : "kada namij ya kaxaita da mace domin na ukun su shaixan ne"2
Abu ne mai saqi kaucewa hanya tsakanin namiji da mace musamman ma ace qofa a kulle take, a nan ma Manzon Rahama (SAW) ya tsanan ta haramcin hakan da cewar sa : "duk wanda ya kasance ya bada gaskiya ga Allah da ranar lahira, kada ya kaxaita da mace idan babu muharrami a tsakanin su" .
Ya kuma qara cewa : " na hane ku zance da mace a kaxaice, domin kaxaitar namiji da mace idan babu muharramin ta a tare da ita, face sai ya so ya neme ta" 3
Muharrami shine wanda ke da dangantaka da mace ta nasaba wadda bai halatta ya aure ta ba, kamar uba, Kaka, xan wa, xan qani, qanwa, baffa, da sauran waxanda suka zo cikin qur'ani, duk wanda baya cikin waxannan ba muharrami bane ga mace. Saboda haka bai halatta mace ta kaxaita da shi ba tare da na ukun su ba, saidai idan a waje ne ba cikin xaki ba ko gidan da yake a kulle, an tambayi xaya daga cikin bayin Allah salihai, aka ce masa ya zaka kasance idan ka kaxaita da mace, sai ya ce : ina roqon Allah (SW) da kada na samu kaina a irin wannan halin, akwai abubwa da yawa da suke faruwa cikin al'umma da suke jawo kaxaita tsakanin namiji da mace wanda a qarshe ke kaisu ga kauce hanya da afkawa cikin varna, akwai wata makaranta ta wasu samari da 'yan mata ke koyon karatu a cikin ta, kuma ajin su xaya, da aka yi hutu, sai xaya daga cikin samarin ajin ke zuwa gidan su xaya daga cikin 'yan matan ajin su ana yin nazari, har iyayen yarinyar suka nutsu da halin sa da xabi'un sa, har ta kai ana barin su su biyu, ba a jima ba sai wata rana uban yarinyar ya kama su da mummunar xabi'a.
Haka wata yarinyar, ta nemi wani malami da yake koyar da ita wani darasi da ba a yi musu a makaranta, shu kuma wannan malamin yana da matsayi a cikin al'umma ana ganin sa da qima, an yi 'yan kwanaki tana zuwa karatu sai shaawa ta mtsawa malamin, ya nemi ya kai hannun sa kan qirjin ta, wani abu kuma mai hatsari da ke faruwa cikin al'ummar mu a yanzu shine, wasanni da sakin jiki da juna tsakanin namiji da qanwar matar sa, ko qanin miji da matar wa, haka ma qanin miji da qanwar mata, ko aboki da matar abokin sa, domin yin haka na jawo qulla mummunar alqa haramtacciya a tsakanin juna.
Manzon Rahama (SAW) ya hana shiga wajan mata lokacin da mazajen su basa nan ya ce : "kada ku karkata ga waxanda (mata) mazajen su basa nan, haqiqa shaixan yana bin jini"1
Akwai wani aboki ya kasance yana shiga wajan matar abokin sa idan baya nan, sai haka ya jawo aikata masha'a tare da matar abokin, suka yi ta yin haka har tsawon wasu watanni, sai ta shirya da abokin mijin nata a kan su kashe mijin ta, suka sa ranar aikata hakan, sai matar tai tafiya ganin dangi, shi kuma wannan abokin ya yi qoqarin kashe wannan mijin nata, yai masa rauni ya barshi a cikin jini, daga baya ya farfaxo ya faxi abinda ya faru aka kamo shi, daga baya mijin matar ya mutu shima aka kashe shi.
To mai karatu ka ji kaxan daga shrrin aboki ya dinga shiga wajan matarka idan baka nan, Allah ya kiyaye.
Haka akwai wani attajiri, ya kasance yana kyautatawa wani magidanci talaka, ya na xauke musu wahalhalun rayuwa, sai ya zama an samu fahimtar juna sosai a tsakanin mai kuxin da talakan, domin ya na girmama shi sosai, har ta kai ga mai kuxin na shiga gidan talakan ya na neman matar sa lokacin da ya fita, daga qarshe Allah ya tona asirin su 'yan uwan talakan suka kama su, sai talakan ya saki matar shi kuma mai kuxin ya kunyata.

TAKA TSANTSAN WAJAN CUXANYA
Bayani ya gabata a kan cewa, tsarin musulunci bai haramta cuxanya tsakanin maza da mata ba, sai dai ya qayyade shi da qa'idojin kamun kai.
Manzon Rahama (SAW) na cewa : "idan mace ta tashi daga wuri nan take, kada namiji ya zauna"2
Domin wasu mazajen na tasirantuwa da duk wan al'amari da ya shafi mace, wanna kuwa wani abu ne da yake sananne ga al'umma, kuma hakan ya faru a haqiqa, saboda haka zama wajen da mace ta tsahi yana tayar da shaawa ga wasu.
Idan kuma shaawa ta tashi, ko ya nemi hanyar shayar da ita wadda ba ta shari'a ba ko ya sha tsanani da wahala sakamakon rashin shayar da ita, kaga rigakafi shine yafi masa kyau a nan wajan, kawar da abin tun kafin ya faru.
Manzon Rahama (SAW) na cewa : "duk wanda ya yi imani da ranar lahira, kada ya kwana a wajan da zai dinga jin numfashinta macen da ba muharramar sa ba"3.
Numfashin mace na tayar da shaawa ga wasu, idan suna jin sa, domin haka na jawo namiji ya nemi wasu sassa daga jikin ta da zai jawo fitina na jikin ta, sakamakon jin numfashin ta, wannan kuma abu ne da yake faruwa a haqiqanin ga wasu da yawa, daga mazaje wani mai suna Faxin Bin Najihi na cewa : (idan azzakari ya tashi, xaya bisa ukun hankali na gushewa)4
Haka nan ma don rigakafia kan shaawa musulnci ya hana musafaha (gaisawa hannu da hannu tsakanin namiji da mace), domin haxa hannu na tayar da shaawa sosai ga wasu mazajen.
Jikan Manzon Rahama (SAW) Imam Ja'afar Assadiq (AS) ya ce : "bai halatta ga namiji ya yi hannu da mace ba sai wadda ta haramta ya aura, kamar 'yar uwa (qanwa ko ya), 'yar sa, 'yar qanwar sa ko yar sa, da makamantan su, amma  wadda ya kamata ya aura, bai halatta ya yi hannu da ita ba, sai dai ta bayan tufafi ba zai miqa hannun ta ba"1
Hakan nan dai a kan rigakafin tayar da shaawaaka hana simbanta ko rungumar yarinya 'yar shekara shida.
Imam Musa (AS) na cewa : "idan yarinya ta kai shekara shida, bai halatta ga namijin da ba muharramin ta ba ya simbace ta ko ya rungumeta ba"2
Haka nan abin yake ga yaro idan ya wuce shekaru bakwai.
Manzon Rahama (SAW) na cewa : "yaro idan ya kai shekaru bakwai ba zai simbanci mace ba"2
Waxannan wasiyyoyi ne da faxakarwa dangane da kariya tare da rigakafi domin gudun faxawa cikin varna sakamakon alaqa tsakanin namiji da mace.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: