bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      14:52:34
Shi so tsakanin jinsin maza da mata ya kasu nau'i nau'i dangane da manufa da buqatu, idan ya zama manufa da hadafin cikin sa wargi ne da son zuciya, da neman shayar da shaawa ta atacciyar hanya wanna soyayyar ta zama haramun
Lambar Labari: 294
SOYAYYA KAFIN AURE
So wata xabia ce ta zuciya kafaffiya a cikin zuciya, hankali da nufin mutum, saboda haka rayuwa babu soyayya kamar kogi ne babu ruwa ko ace bishiya babu ganye, soayyay haske ne da ke haskaka zuciyar wanda mutum ke samun nutsuwa da hutu da ita, duk da cewa so kafaffe ne a cikin zuciyar mutum, amma nufi ko iko ne ke juya shi wajan fuskantar da shi inda ya ga dama, daga cikin so akwai son jinsi, wanda shine na xabi'a  da namiji kewa mace ko mace ta yiwa namiji, shine so na zuciya ga zuciya, ruhi da  ruhi, jiki ga jiki, kallo ga kallo, harshe ga harshe, ta yadda zasu dinga misayar kalmomi da kallo, so tsakanin namiji da mace babu haramci a cikin sa matuqar gaskiya ne, tsarin musulunci ya halatta soyayya, tsarin musulunci na son mutun ya dinga hukunci da hankali, a kan xabi'ar sa, musulunci bai hana magana da bayyanar da so ga juna ba, domin a tsara al'umma ingantacciya ta gari, tsarin musulunci yana halatta yin soyayya tsarkakakkiya, daga wata varna ake gina ta a kan hankali da kamewa ta yadda ba za a kaucewa hankali a cikin ta ba, domin musulunci na son mutum ya dinga aiki da hankali a kan son ransa.
Shi so tsakanin jinsin maza da mata ya kasu nau'i nau'i dangane da manufa da buqatu, idan ya zama manufa da hadafin cikin sa wargi ne da son zuciya, da neman shayar da shaawa ta atacciyar hanya wanna soyayyar ta zama haramun, domin zai kai mutum ga aukawa cikin halaka, wanna itace soyayyar qarya da ha'inci, yaudara, wadda ta sha banbam da soyayya ta mutunci da hankali, gaskiya da kamewa, ko wacce soyayya ta haqiqa wadda tsarin musulunci ya yadda da ita.
Akwai kuma soyayyar da ake ganin ta bisa hadafi da manufar yin aure, da gina iyali ta hanyar aure, ita ma wanna soyayyar ta kasu kashi-kashi kamar haka :
1-    Soyayya tsakanin masoya da zata fara da gani da haxuwa, sannan al'qawarin sake haxuwa da yin zance, kevewa da haxuwa inda ba kowa don neman sabo da fahimtar juna.
Daga nan sai shaawar xaya ta karkata zuwa xayan, sai a yi qoqarin jiyar da juna daxi ta wasu hanyoyi, kamr wasn banza, tave-tave, kiss ko runguma, daga nan sai shaawa ta haxu da shaawa har ta kai ga shayar da ita ta haramtacciyar hanya.
A nan gaba xayan soyayyar haramun ce koda kuwa ta kai su ga yin aure a qarshe.

2-    A samu so cikin zuciyar masoya tare da sanin junan su a kan hakan, ko kuma xayan su ya bayyanar da hakan ta hanyar saqo, wasiqa ko magana da ssauran su.
Daga cikin hanyoyin bayyanar da soyayyar aure da gina iyali, amman duk sai an yi hakan ne ta hanyar kame kai ga juna da tsarkakakkiyar hanyar sadar sa saqon soyayyar da nesantar duk wata hanyar ganawa kevantacciya, wannan soyayyar babu aibi a cikin ta idan aka tafiyar da ita a kan wannan haddin.
A samo so a cikin zukatan masoya biyu, sannan a fara da zance na shari'a sai a qulla al'qawarin aure ba tare da vata lokaci ba, wanna shine son da tsarin musulunci ya fi kwaxayi, domin ya na tsarewa al'umma faxawa varna ko kauce hanya, kuma hanya ce ta gina gaskiya da jin daxin ruhi da jiki baki xaya.
Gabatar da maganar aure  tun afarkon zance na taimakawa wajan samun nutsuwa ga masoya baki xaya, domin idan an samu savani na rashin yadda daga xayan su xayan ba zai sha wahala ba sosai wajan haqura, savanin a ce an sava kuma an shaqu.
Manzon Rahama (SAW) na cewa : "ba abinda aka gani ga masoya kamar aure".
Domin da soyayya ta gaskiya ne masoya zasu samu galaba a kan zuciyar su da shaawar su, wanda da shine zasu kange kan su daga karkata zuwa ga son rai, su samu kaiwa marhal maxaukakiya sakamakon soyayya, saboda haka rayuwar auratayya zata zama mai inganci maxaukakiya, akwai qissoshi da yawa da ke tabbatar mana da hakan.
Muna da aboki a ma'aikatar ilimi, duk lokacin da muke hira da shi, yana yawan kawo mana maganar matar sa , ya yi ta yabon yayana yi mata addu'a da fatan alheri da ci gaban zaman su, kuma baya nisa da ita, duk da cewa ba a garin yake aiki ba, amman koda yaushe yana kawo uzuri don kada ya samu hutu kar ya je aiki.
Sai wata rana muka tambaye shi sirrin wannan auren nasu, sai ya ce mana na kasance ina karantarwa a wata makarantar gaba da primary. Sai muka saba da wata yarinya (mata ta ta yanzu).
Sai na fahimci halaiyyar ta da fahimtar ta, na binciki dangin ta don a samu yaqini da cewa zan iya auren ta, sai na rubuta mata wasiqa a ciki na bayyana mata haqiqani na da matsayi na da ra'ayi na game da ita daga qarsshe na nem ta da ta zamo abokiyar rayuwa ta.
Daga baya dangin ta suka rubuto min amsa, bayan xan lokaci kaxan muka samu dacewa, muka yi alqawarin aure bayan shekara xayta muka yi aure.
Wannan soyayyar da muka qulla ta gaskiya itace sirrin sa ya sa auren mu ya yi danqo kamar haka, yanzu shekarar mu shida, amman kamar yau aka xaura mana auren.

ILLAR MUMMUNAR SOYAYYA KAFIN AURE
Shi so kamar yadda aka fara shi da gani da magana daka nan sai alaqa ta qullu bayan maimaita haxuwa, da ganin qaunar xayan su ta shiga zuciyar xayan, har ya zama yana tasiri a kan xabi'ar sa da shaawar sa, daga nan sai ya zama ana cikakkiyar haxuwa ko da yaushe kamar ya zama ana haduwa a makaranta ko kan titi, ko gidan aboki ko qawa, har ma da wuraren shaqatawa da sauran su.
Daga nan sai a fara haxuwa kevantacciya kallo da murya su canza a fara zama ko tsayawa kusa-kusa da juna, da haka ne kwaxayi da shaawa ke tashi su tunkuxa su har ta kai su ga manufar haxuwa don kawar da shaawa da jiyar da juna daxi, musamman ga namiji savanin mace domin ita sau da yawa ana rinjayar ta ne, inda masoyin nata ke rinjayarta kuwa shine idan ya mallaki zuciyar ta sai ya zama kai tsaye ya mallaki gavovin ta, sai ta sallama masa kanta, bayan xan lokaci ana wasa da tabe-tabe wannan kuma al'amari ne na xabi'a.
Domin ita shaawa tana buqatar a biya mata buqata saboda haka kowanne daga cikin su yana so, kuma yana kwaxayin ya isa zuwa ga jin daxi bayan tashin shaawar sa.
Idan aka kai wannan matakin mai zai hana haxuwar jiki da jik bayan an riga an haxu zuciya da zuciya, kuma mai zai hana saduwa, bayan an gama tayarwa da juna shaawa?
Wasu na ganin cuxanya tun ana yara, yana sa soyayya ta gaskiya da kamewa wadda babu varna a cikin ta, sai dai a haqiqa an tabbatar da kuskuren wanna ra'ayin, domin cuxanya da rashin cuxanya zai iya haifar da soyayyar gaskiya da kamewa, haka abinda ya buxe qofa ga saurayi da budurwa ya ba su damar cuxanya da abinda ya rufe qofa garesu amma ya basu damar kaxaita da wasa, dukkan waxanna abubuwan biyu na bada dama ga hanyar shayar da shaawa da zuwa ga jin daxin juna.
Babu mai hani ko tsarewa bisa aukuwar sa na addini ko na al'ada ko zuciya da zai hana su, idan ya kasance ga mahanin na addini ne ya kamata ga wanda ya yi imani da shi, ya tsaya a matsayar sa da koyarwar sa, idan kuma al'ada ce ta hana to su kula da ita kafin su kaxaita, idan zuciya ce ta hana su to ta tsare su abisa haxuwa da kaxaita da mummunan wasa da kallo.
Irin waxanna samarin kamar masunta ne masu kamun kifi, ko maharba masu xana tarko, domin suna xana tarkon soyayya su kama yarinya idan ta zo hannun su, sai su yi yadda suka ga dama da ita, daga baya su barta a wulaqance, Allah ya raba 'yan mata da irin waxannan samarin, Ameen.



comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: