bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      14:57:09
Wannan na nufin siffofin ilimi, iko, gabata da ire-iren su na tare da zati sune ainihin
Lambar Labari: 296
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin kai
Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Ga Manzon Rahama Da Alayensa Tsarkaka

Ci gaba:-
1-    Rassan tauhidi
Mun yi imani da cewa tauhidi na da rassa huxu kamar haka.
a-    Tauhidin zati.
Ma'anar sa shine kaxaita zatin Allah cewa bashi da mai kama da shi.
b-    Tauhidin siffofi.
Wannan na nufin siffofin ilimi, iko, gabata da ire-iren su na tare da zati sune ainihin zatin Allah maxaukakin sarki, ba irin siffofin halitta bane waxanda suke bamban ta da zatin su, wato sun rabu da zatin su, a yadda xabi'ar yanayi take kasancewar zatin Allah shine siffofin sa to wannan na buqatar tunani da kulawa sosai.
c-    Tauhidin ayyuka.
Duk wani aiki da motsi a duniya yana faruwa sanadiyyar  Allah da mashi'ar sa kamar faxin Allah cewa : { Allah shine mahaliccin dukkan komai kuma shine abin dogaron komai }20
Kuma da faxinsa cewa : { mabuxan sammai da qassai a hannun sa suke } 21
Kwarai : ba wani mai tasiri a duniya sai Allah amma hakan ba yana nufin an tilas ta mu akan ayyukan da muke aikatawa bane, an bamu dama muyi aiki tare da xaukar matsayin da muke so kamar faxin sa maxaukaki : {haqiqa mun shiryar da xan Adam hanya ko dai yayi godiya ko ya kafirce }22  kuma da faxin sa maxaukaki cewa : {ba za a bawa mutum komai ba sai sakamakon aikin sa }23
Waxannan ayoyin masu girma suna bayyan cewa mutum na da yanci a manufar sa, sai dai Allah shi ke bada wannan yancin da ikon yin aikin da kuma matsayi, don haka ne ake danganta aiyyukan mu gare mu ba tare da an rage komai ba, a kula.
Kawai Allah ne yaso muyi ayyukan mu cikin yanci don ya jarraba mu ya sanyamu a hanyar kamala (cika), domin mutum baya samun kamala sai da yancin manufa da shiga hanyar xa'a da ainihin zavin sa, domin kuwa aikin da aka tilasta mutum a kai, ya fita daga yancin zavi kuma baya nuna gyaruwar mutum ko lalacewar sa sabida an nuna masa fin qarfi.
Da ana yilasta mu a cikin ayyukan mu, da babu ma'ana a turo mana annabawa, domin bata da amfani balle ma har a saukar musu da litattafai, da wajabta mana al'amuran addini, da bayar da sakamako idan mutum yayi aikin kirki ko azabtarwar da Allah sun koru, wannan shine abinda muka koya daga makarantar ahlilbait (AS) cewa babu tilastawa kuma babu barin mutane sakaka (wato abun na tsakanin cewa an baka damar aiki kuma ana da iko a kanka).24
d-    Tauhidin Ibada.
Ana nufin kaxaita Allah da ibada shi kaxai, babu abin bautawa idan ba Allah ba, wannan reshen ana bashi muhimman ci a rassan tauhidi, kuma annabawa sun himmatu da shi sosai { ba'a umarce su ba sai don su bautawa Allah shi kaxai suna masu bin addinin gaskiya ... wannan shine madaidaicin addini }.25
A lokacin da mutum ke wuce cikar matakan xabiu da sanin Allah to a lokacin ne mutum ke qara kutsawa cikin ma'anar tauhidi, har ma ya kai matsayin da baya tunanin wannan matakin sai don Allah kuma ya na neman saduk inda ya sauka ko ya tafi, kar ya shagaltar da kansa da wanin Allah  : { duk abinda ya shagaltar da kai har ka bar Allah to shine gunkin ka }.
Haqiqa mun yi imani da cewa ressan tauhidi basu da iyaka sabida bayan abinda muke faxa akwai wasu rassan, daga ciki akwai tauhidin mulki ; {duk abinda ke cikin sammai da qassai na Allah ne }.26 da tauhidin hukunci { duk wanda baiyi hukunci da abinda Allah ya saukar ba wannan na daga cikin kafirai }.27
2-    Annabawa na yin mu'ujizozin su da izinin Allah.
Tabbas mun sakan kance cewa farkon tauhidin ayyuka na qarfafa haqiqanin lamari, amfanin sa shine mu'ujizozin annabawa da ayyukan da suke savawa xabia duk suna yin sa ne da izinin Allah, kamar yadda yazo cikin al'qurani mai girma game da annabi Isa (AS) : {kana warkar da makaho da kurma da izinin Allah, kuma kana raya matattu da izinin Allah}.28
Kuma yazo game da xaya daga cikin waziran annabi Sulaiman (AS): { wanda ke da ilimin littafi yace ni zan kawo maka shi kafin ka qifta idon ka lokacin da ya gan shi a gaban sa a tabbace sai yace wannan fallar ubangiji na ce }.29
Don haka ne warkarwar da annabi Isa (AS) ya yiwa makaho, kuturu da raya matattu duk da izinin Allah ne kuma shine ainihin tauhidi.
3-    Mala'iku.
Haqiqa mun yi Imani da mala'iku waxanda Allah ya xora musu nauyin wasu aiyyuka a kevance, daga cikin su akwai waxanda aka xora musu isar da saqon wahayi ga annabawa.30  daga cikin su akwai masu rubuta aiyyukan bayi,31 daga cikin su akwai masu karvar rayukan bayi,32  daga cikin su akwai waxanda aka basu aikin taimakon mumin da ya tsaya kan tafarki, 33  daga cikin su akwai waxanda ke taimakawa muminai a wajan daga,34  daga cikin su akwai waxanda horon masu savo da masu tsaurin kai,35 da wasu saxanda ke yin wasu aiyyuka na tsarin gudanar da duniya .
Waxannan aiyyukan da mala'iku ke yi baya kore asalin tauhdin aiki da tauhidin rububiyya (allanta), ai sune ma ke tabbatar da shi, domin suna gudanarwa ne da izinin Allah da gudanarwar sa da qarfin sa.
A nan ne maganar ceton annabawa da ma'asumai da taimakawar mala'iku ke fitowa fili, domin shine ainihin tauhidi domin baya tabbata sai da iqinin Allah maxaukaki : { ba wani mai ceto sai da izinin Allah }.36
Zamu kawo muku qarin bayani mai yawa kan waxannan maganganu musamman ma waxanda suka shafi tawassuli (kamin qafa) cikin bayanin annabta.
4-    Allah shi kaxai ne abin bauta.
Mun yi imani cewa Allah shi kaxai kawai ake yiwa bauta (kamar yadda muka faxa a bayanan tauhidin (bauta) ibada, domin duk wanda ke bautawa wanin sa to mushriki ne, domin kuwa duk kiran da annabawa ke yi ya kafu ne a kan wannan : { ku bautawa Allah ba ku da wani ubangiji sai shi }, wannan bayanin ya zo a ayoyi da yawa na qur'ani mai girma a harshen annabawa.37
Wannan babban take na musulunci na maimai tuwa ne a kan harshen mu kullum sau da yawa a salla cikin suratul hamdu lokacin da muke cewa : { kai kaxai muke bautawa kuma gareka muke neman taimako }.
A fili yake mun yi imani da ceton annabawa da mala'iku da izinin Allah, abinda ayoyin qur'ani suka zo da shi, ba wai ana nufin ibada ba. Kamar yadda tawassuli da annabawa baya shiga cikin tauhidin ibada, domin yana nufin nema daga wanda ake tawassuli da shi ya roqi Allah ya warware matsalar mai tawassulin wannan sharhinsa zai zo a bayanin annabta.
5-    Vuyan haqiqanin zatinsa maxaukaki.
Mun yi imani cewa haqiqanin zatin sa maxaukaki ya vuyarwa kowa duk da yawan samuwar guraben sa a duniya, ba wanda zai iya sanin haqiqanin zatin sa ko waye,  domin zatin sa na fil azal ne ba shi da iyaka ta kowace fuska, mutum kuwa na da iyaka da haddi ba zai yiyu ya kewaye da Allah ba, Allah ne mai kewayewa da komai : { ai Allah ne mai kewaye da dukkan komai }.38 { Allah ya kewaye su da sanin sa ta bayan su }.39
Ya zo a hadisin manzon rahama (SAW) : (( ba mu bauta maka haqiqanin bauta maka ba kuma bamu sanka haqiqanin sani ba }.40
A nan ya wajaba kada mu faxa kuskure kuma muqi karanta dunqulallen ilimi na sanin Allah, na tsaya kan annabta wasu lafuzzan da basu da ma'ana, domin an hana mu gano ilimin da aka yi masa filla-filla, yin haka toshe qofar sanin Allah ne, wannan ba muyi imani da shi ba, don ba mu yarda da wannan ba, sabida qur'ani da sauran litattafan sama sun sauka ne don buxe qofar sanin Allah, domin yin bayanin hakan zai yiyu mu kawo misalai, mu bamu san haqiqanin ruhi ba sai dai mun san ma'anar sa a dunqule, domin nuna alamomin samuwar sa (gurbin samuwar sa) na nuna mana tabbacin samuwar sa.
Imam muhammad bin Ali (AS) yace : ((duk abinda kuka gane shi da tunanin ku a cikin zatin ma'anar sa to shima halittacce ne, Allah ne ya yi shi kamar ku mutane shima halittacce ne )).41
Imam Ali (AS) ya bayyana hanyar sanin Allah da wani bayani mai kyau a fili yana cewa : (( Allah bai tsinkayar da hankula iyakance masa siffofi ba, kuma bai kore hankula daga wajabcin sanin sa ba )).42
6-    Babu yin tataxili (wato wuce gona da iri ko nwargaza siffofin Allah.
Haqiqa mun yi imani cewa faxawa cikin kwarin kamanta shi kuskure ne haka ma kuma kore sanin Allah da siffofin sa ya zama kuskure, ma'anar haka shine; bazamu iya cewa hanyar sanin Allah a rufe take ba, kamar yadda ba zamu iya xaukar Allah a matsayin wanda yayi kama da halittar sa ba, sabida haka bin xayan hanyoyin nan biyu ya zama shige gona da iri, xaya kuma ya zama sakaci, a gaskiyar magana abu ne mai yiyuwa a san Allah ta hanyar ayyukan sa a cikin baki xayan duniya. Sai a kula.   


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: