bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:00:20
Idan ba za a sami ruwan da zai isa alwala ko wanka ba
Lambar Labari: 297
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin kai
Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Ga Manzon Rahama Da Alayensa Tsarkaka

Hukunce-hukuncen Taimama
 72> (m.655, d.s) TaImama tana wajaba maimakon alwala ko wanka a wajaje bakwai:-
1.    Idan ba za a sami ruwan da zai isa alwala ko wanka ba.
2.    Rashin samun ikon debo ruwa saboda tsufa ko tsoron 'yan fashi da makamancinsu.
3.    Jin tsoron cutuwa da yin ammfani da ruwa.
4.    Tsororn kishirwa a kansa ko wata dabba mai daraja idan ya yi amfani da ruwan don yin alwala.
5.    Rashin isar ruwan don yin tsarkin dauda da tsarkin kari, (hadasi da habasi) gaba daya.
6.    Kasantuwar ruwan ko kuma kwanon da yake ciki wanda ya haramta a yi amfani da shi ne.
7.    Kuncin lokaci ta yadda idan ya yi alwala ko wanka, dukkanin sallarsa ko sashenta zai fada wajen lokaci.
 73> (m. 692) Ya inganta a yi taImama a kan kasa mai tsarki, saboda haka lalle taImama tana inganta a kan kasa da tsakuwa da rairayi da dutse.
 74> (m.708-709) Mafi soyuwa taImama ta kasance a bisa tsari mai zuwa:-
 Bayan yin niyya, sai ya buga tafukansa gaba daya a kan abin da ya inganta a yi taImama da shi, sannan ya shafa dukkan goshinsa da hannayensa, tun daga matsarar gashi har zuwa gira (girori biyu), tare da saman hanci, (wato mafarar hanci inda yake hade da gira da kuma karshen goshi), sannan ya shafi dukkan bayan hannunsa na dama da cikin tafin hannunsa na hagu, sannan ya shafi dukkan bayan hannunsa na hagu da cikin tafin hannunsa na dama.
A taImama da ke wakiltar wanka, bayan da ya yi niyya ya buga kasa da hannayensa ya shafi fuskarsa da su kamar yadda aka bayyana a baya, wajibi ne kuma ya buga kasa da hannayensa, sannan ya shafi bayan hannayen nasa.


Hukunce-hukuncen Salla
Mafifitan ayyuka ita ce salla "Idan salla ta karbu dukkan ayyuka sun karbu idan kuma ta baci to dukkan ayyuka sun baci". Kuma ita ce saman dukkan wani aiki na wajibi da yake kan dukkan musulmi da musulma, inda Allah (S.W.T) yake cewa:- "Hakika salla ta kasance wajibi mai tsayayyen lokaci a kan dukkan muminai" Nisa'i/ 103.
 Da kuma fadinsa:- "Ka tsaida salla, hakika salla tana hana alfasha da abin ki". Ankabut/ 45.
 Da kuma fadinsa:- "Azaba ta tabbata a kan masu salla. Wadannan da suke rafkanwa a cikin sallarsu. Wadannan da suke yin riya. Sannan suke kin bayar da gudunnmuwa. Ma'un/ 5-7.
 Yazo a hadisi madaukaki cewa:- "Salla ginshikin addini ce".

 75> Salla Wajiba Ta Kullum Guda Biyar Ce
Sallar asuba – raka'a biyu ce.
2 da 3- Sallar azahar raka'a hudu, da Sallar la'asar raka'a hudu.
4 da 5- Sallar magriba raka'a uku, da sallar isha, raka'a hudu.



Sharuddan Salla Da Magabatanta
76> (m.737 ds) Lokacin sallar safiya yana farawa tun daga bullowar alfijir na gaskiya har zuwa bullowar rana.
Lokacin sallar azahar da la'asar daga karkatar rana yake farawa har zuwa faduwar rana. Kebantacce lokacin sallar Azahar shi ne farkon lokacin gwargwadon lokacin yinta, a yayin da la'asar take kebanta da karshen lokacin ta yadda abin da ya rage zuwa faduwar rana gwargwadon lokacin da za a yi ta wannan (lokacin) ya kebanta da la’asar kawai, kuma abin da (lokacin da) ke tsakanin lokacin da ya kebanta sa sallar azahar da kuma wanda ya kebanta da sallar la’asar lokaci ne da suka yi tarayya a cikinsa.
Amma lokacin sallar al'muru (magariba) da isha, daga faduwar rana ne zuwa rabin dare. Lokacin sallar magriba na musamman shi ne:- Tun daga jaja-jajan gabas zuwa wucewar gwargwadon lokacin da za a iya yin raka'a uku. Lokacin da ya kebanta da isha shi ne idan kimanin lokacin da za a iya yin raka'o'i hudu ya rage zuwa rabin dare. Amma abin da ke tsakanin haka sun yi tarayya a cikinsa.
 Idan lokacin salla ya zama yalwatacce kuma ya zama akwai mai binsa bashi da yake jiran sa, to wajibi ne ya fara biyan bashin idan hakan zai yiwu, sannan ya yi sallar. Haka nan idan ya zama akwai wani wajibi na gaggawa, a gefe, kamar gusar da najasa daga masallaci, don haka ya wajaba ya fara gusar da najasar kafin sallar. Da zai gabatar da sallar ya yi sabo, amma sallarsa ta yi.
 78> (m.806) An shardanta abubuwa shida a bisa tufafin mai salla:-
1.    Ya kasance mai tsarki.
2.    Ya kasance na halal.
3.    Kada ya kasance daga wani yankin jikin mataccen abu.
4.    Kada ya kasance daga wani bangare na abin da ba a cin namansu.
5da6. Idan mai salla ya kasance namiji, kada tufafinsa ya kasance ibrisim (abrisham) tsantsa.
Ko kuma wanda aka saka da zinare ko aka yi masa ado da shi.
79> (m.840) Haramun ne ga namiji ya yi ado da zinare kuma sallarsa tana baci da shi. Amma ya halatta ga mata a cikin salla da wajenta.
 80> (m.857) Wajibi ne jikin mai salla da tufafinsu su kasance masu tsarki, sai dai in jikinsa ko tufafinsa ya kasance akwai jinin rauni ko miki ko kurji, ta yadda zai yi wahala ga mafi yawan mutane su tsarkake shi ko su canja tufafin kafin warkewar mikin ko raunin a wannan lokacin sallar ta inganta tare da wannan jinin.
 81> (m.796) Wajibi ne ga namiji a lokacin salla ya suturce al'aurarsa, mafi kyau ya suturce daga cibiyarsa zuwa gwiwa.
 82> (m.797) Wajibi ne mace ta suturce dukkan jikinta yayin salla, har kanta da gashinta. Amma fuska daidai gwargwadon inda ake wankewa a alwala da tafukanta na hannaye da kafafu ba dole ba ne ta suturta su.
 83> (m.875) Salla tana baci in aka yi ta a wurin kwace, koda kuwa mai sallar yana tsaye ne a kan shimfida ko tabarma ko makamancin su. Amma salla ba ta baci idan aka yi ta a karkashin rufi ko hema ta kwace.
 84> (m.909) Haramun ne a najasta masallaci da rufinsa da geffansa da bangonsa na ciki, kuma wajibi ne a tsarkake shi da zarar an san da najastuwarsa.
 85> (m.902 ds) An so a yi salla a masallatai, yin hakan mustahabbi ne mai karfi, mafificin masallatai shi ne masallacin harami sannan masallacin Annabi, sannan kaburburan Imamai. An karhanta wa makwabcin masallaci ya yi salla ba a masallacin ba. Amma masallacin mace shi ne dakin ta.
 An so tsarkake masallaci a kuma haskaka shi da fitilu, kuma an so ga wanda zai shiga cikinsa ya sa turare da tufafi masu tsafta na alfarma, kuma ya binciki takalminsa don kada ya sa dauda a cikin masallaci. An karhanta bacci a cikin masallaci sai inda larura, haka nan magana a kan lamuran duniya da shagaltuwa da sana'o'i, kamar yadda aka karhanta a kazanta masallaci ko a yi tofi ko kaki a cikinsa, kai da dukkan abin da ake ganin zai zama sanadi na gushewar alfarmar masallaci koda kuwa daga murya ne, in ba don kiran salla ba.
 86> (m.774) Alkiblar da aka shardanta a cikin salla ita ce ainihin Ka'aba mai daraja wacce take a Makka mai girma, don haka wajibi ne a fuskance ta yayin yin salla. Sai dai ya isar ga wanda yake nesa ya fuskance ta, ta yadda za a gan shi a matsayin wanda ya fuskance ta.




Wajiban Salla
87> Wajiban salla kala biyu ne:-
1- Niyya: wajibi ne ga baligi ya yi niyyar yin salla da nufin neman kusanci da Allah (S.W.T), haka nan ya wajaba a cikin niyyar sallar azahar da la'asar ya ayyana kasancewar sallar ta azahar ce ko la'asar.
2- Tsayuwa yayin kabbarar harama wajibi ce, haka ma yayin karatu kafin ruku'u da bayansa.
3- Kabbarar harama:- Ita ce fadin (Allahu akbar) yayin fara salla.
4- Karatu:- karanta fatiha da sura a cikin raka'o'i biyu na farko, haka nan karanta fatiha ko tasbihohi guda hudu a raka'a ta uku da ta hudu.
5- Ruku'u.
6- Sujjada.
7- Zikirin ruku'u da sujjada.
8- Tahiya.
9- Sallama.
10- Jerantawa:- Wajibi ne yin dukkan ayyukan salla daya bayan daya, idan ya yi niyya, bayanta sai kabbarar harama, bayan ta sai karatu… har zuwa karshe.
11- Bibiya:- wajibi ne kada ya rarraba tsakanin wajibi da wajibin da yake bayansa, ta yadda za su zama a rarrabe, dole ne ya yi su daya na bin daya.
88> (m.951) wajiban salla kala biyu ne:-
 Rukunan salla da wadanda ba rukunai ba. Amma rukunai su ne wadanda salla take baci da kara su ko tauye su, da gangan ko da rafkanwa, sun hada da:-
1- Niyya.
2- Kabbarar harama.
3- Tsayuwa yayin kabbarar harama da tsayuwa da ke hade da ruku'u gabaninsa.
4- Ruku'u.
5- Sujjadodi biyu a raka'a daya.
 Amma sauran wajiban ba rukunai ba ne, wannan yana nufin idan aka dada su ko aka rage su da gangan salla ta baci, amma idan ya kasance bisa rafkanuwa ne, salla ba ta baci ba.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: