bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:07:34
Kuma ku taimaki juna a wajen aikin kwarai da kuma takawa” (Sura Ma’ida aya ta 2)
Lambar Labari: 298
A cikin wata ayar mai girma kuma Allah subhanahu wa Ta’ala yana cewa:
[ وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَى وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ ] (سورة المائدة : الأية 2).
"Kuma ku taimaki juna a wajen aikin kwarai da kuma takawa” (Sura Ma’ida aya ta 2).
Ya zo a cikin tafsirin Amsal sheikh Nasir Makarim ya ce: Ayar tana karfafawa ne a kan cewa – dangane da ci gaba a kan bahasin da aka ambata, to a bisa hadafin kammala shi (sai ayar take magana cewa) – dole ne musulmi – maimakon su hada kawukansu a kan daukar fansa ga abokanan husumarsu wadanda daga baya sun riga sun karbi musulunci to – su tattaru gabaki dayansu domin su hada kawukansu wajen aikata ayyukan alheri da tsayuwa a kan takawa, kuma ka da su yi taimakekeniya a kan munanan ayyuka da sharrance-sharrance da kiyayya.
To a yayin da yake karin bayani a kan wasu nukutoti a karkashin ita wannan aya din mai girma sai yake cewa:
Taimakekeniya a Cikin Ayyukan Alheri: Lallai ne cewa kira zuwa ga yin taimakekeniya wanda wannan ayar mai girma take karfafarsa abu ne wanda yake mafari kuma gamamme a koyarwar musulunci, hakan nan ma zai iya shiga cikin kowanne bangare na rayuwar zamantakewa ta jama’a, kyawawan halaye, siyasa, haddodi da sauransu. Kuma wannan kira yana nuna wa musulmi cewa dole ne su yi taimakekeniya a kan ayyukan alheri, haka kuma ya hane su ga yin taimakekeniya a kan munanan ayyuka da sabo wadanda za su iya kai su ga shiga cikin zalunci, keta da wuce gona da iri a dukkan nau’oinsu.
Mafari wanda yake a bisa koyarwar musulunci yana mai tsananin kishiyantar mafari irin na zamanin jahiliyyar Larabawa wanda ya yadu a wancan lokacin ya zama kamar ruwan dare, kuma har zuwa wannan lokacin namu wannan mafarin shi ne yake aiki, wanda ya doru a kan ka’ida da ke cewa: <Ka taimaki dan uwanka ko da ya kasance azzalumi ne shi ko kuma wanda ake zalunta ne>. Shi ya sa za ka ga a zamanin jahiliyyar Larabawa idan jama’a ta wata kabila tana yakar jama’ar wata kibalar daban, su sauran ‘yan kabilar kawai za su goyi bayan kabilarsu ne wacce ta kai harin ba tare da sun tsaya sun yi bincike a kan cewa shin wannan harin a bisa adalci ne ko bisa zalunci aka kai shi ba. Irin wannan yadda yake haka din nan za mu gani a wannan zamanin namu dangane da ma’amalolin wasu kasashe, suna tattare da guggubin mafari irin na wancan zamanin jahiliyyar Larabawan, musamman kasashen da suke kawance da juna, za ka samu suna goyon bayan kasar da suke kawance da ita cikin lamurran da suka shafi kasashe ba tare da la’akari da mafari na adalci da kuma la’akari da wace kasa ce azzaluma ko wacce ce ake zalunta a tsakaninsu ba.
Amma lallai musulunci ya rushe wannan mafarin da wannan ka’idar ta zamanin jahiliyya kuma batacce ne. Haka nan kuma ya yi kira ga musulmi da su yi taimakekeniya a kan ayyukan alheri da tsare-tsare masu amfani da gina kai, ba wai ta hanyar sabo, zalunci da wuce gona da iri ba.
Kuma wani abin lura mai muhimmanci a cikin wannan ayar shi ne zuwan <Taimakekeniya/aikin kwarai> da <Takawa> a tare kuma a jere a cikin ayar, wanda kalmomin farko suna nuni ne a kan ayyuka masu amfani wadanda suke karbabbu, ta daya bangaren kuma kalmomin (zunubi da zalunci) suna nuni ne a kan nisantar munanan ayyuka wadanda aka yi hani a kansu – to kuma a bisa wannan asasi – dole ne taimakekeniya a kan ayyuka su zama ta kowanne bangare; shin ayyukan nan sun kasance na kwarai ne ko kuma hani ga munanan ayyuka ne.
{Al-Amsal Fi Tafsiri Kitabillahil Munzal, mujalladi na 3, shafi na 410 - 412} .
Daga nan ne za mu iya kara fahimtar muhimmancin da wajabcin taimakon juna wanda musulunci ya kasance a tsawon lokuta yana karfafawa zuwa gare shi.
Kamar taimakon jama’ar da aka kallafa masu yaki (musamman a wannan lokacin da muke ciki) wanda za mu ga akwai kasashe da yawa wadanda aka kallafa wa raunanan mutane na wadannan kasashen fadawa cikin wani irin mummunan hali a rayuwa, wasu sun rasa garuruwansu, mahallansu, gidajensu, tufafi da abinci da ma dai sauransu. Wanda a nan yana da matukar muhimmanci mu dinga tunawa da su ya zama tunaninsu yana cikin ranmu kuma mu dinga neman hanyoyin da za mu kai masu taimako da tallafi na abin da Allah ya hore mana ta hanyar ba su mafaka ne ko sutura ce ko kudi ko abinci, kai hatta idan da hali ilimantar da su, kuma ka da wannan ya sanya mu manta da raunanan da ke kewaye da mu a cikin danginmu na jinni da na addini, unguwanninmu, garuruwanmu haka ma da wadanda muka hadu da su a halitta, (kamar yadda yake cewa hatta wadanda ba musulmi ba an kwadaitar ga musulmai cewa su dinga taimaka masu daidai gwargwadon hali).
Allah Ta’ala a cikin Qur’ani mai girma yana cewa: "Lallai ne Allah yana son masu kyautatawa”. To mene ne ya fi dadi yau a ce kana cikin wadanda Allah yake so?! Ta yiwu ya zama akwai hanyoyi da yawa wadanda bawa zai bi ya yi aiki sai Allah ya so shi, to amma ai daga cikin irin wadannan hanyoyi akwai ita ma wannan wadda za ka taimaki dan uwanka mabukaci sai Allah ya so ka ya kauna ce ka.
Haka nan ma ya zo daga Annabin Rahama Muhammad (s) ya ce: "Tabbas Allah Ta’ala yana taimakon bawansa mumini madamar yana taimakon dan uwansa mumini”. (Sawabul A’amal shafi na 135). Haka nan kuma a wani gurin Manzon Allah (s) ya ce: "Duk wanda ya biya wa dan uwansa mumini bukatarsa to ya kasance kamar wanda ya bauta wa Allah ne bauta wacce ba ta da iyaka (ba ta da karshe, wato har abada)”. (Biharul Anwar, mujalladi na 71, shafi na 302).    


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: