bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:14:03
Hudu Iliya TAMBAYA GAMLAM TAHIR MENENE KIMAR SADAKIN MANZON ALLAH DA SAIDATUNA KADIJA(A)? MENENE KIMAN SADAKIN AMIRUL MUMININA ALI BIN ABUDALIB DA SAIYIDATUNA FATIMA ALEHIMUSSALAM ?
Lambar Labari: 299
Da sunan Allah maia rahama mai jinqai, tsira da Amincin Allah su tabbata ga manzo da Alayensa tsarkaka managarta.
 Cikin yardan Allah yanzu ne na samu damar Amsa tambaya dan uwa mal. Hudu iliya da yayi agare ni cewa: .
Hudu Iliya TAMBAYA GAMLAM TAHIR MENENE KIMAR SADAKIN MANZON ALLAH DA SAIDATUNA KADIJA(A)? MENENE KIMAN SADAKIN AMIRUL MUMININA ALI BIN ABUDALIB DA SAIYIDATUNA FATIMA ALEHIMUSSALAM ? MENENE KIMAN SADAKIN AIMMA HASSAN DA HUSSAIN ALEHIMUSSALAM GAMATANSU NAFARKO? ALLAH KYAUTA AIKIN MALAM INASON KARTIN HASKE.
To insha Allah zamu bashi Amsa ne da hadisai gada Amma (a.s) ga Hadisan kamar haka.
Na farko:
1-    فقه الرضا (عليه السلام): " إذا تزوجت فاجهد أن لا تجاوز مهرها مهر السنة وهو خمسمائة درهم، فعلى ذلك زوج رسول الله (صلى الله عليه وآله) وتزوج نساءه ".
مستدرك الوسائل النوري الطبرسي./ج/15/ص/62.
1-Ya zo a cikin fiqhur ridah (a.s) cewa: idan zakayi Aure kayi qoqari kada sadakin ya fi sadakin sunna, kuma yawansa shi ne dirhami 500, saboda  haka manzo (s.a.w) ya Auras (da fatima), kuma haka manzo (s.a.w) ya Auri matansa.
Mustadrakul wasaa'il na Annuri dabrisi./juz'I na 15/ shafi na/62.
Hadisi na biyu:

2-     عن الحسين بن سعيد، عن النضر بن سويد، عن عبدالله بن سنان، عن أبي عبدالله (عليه السلام) قال: كان صداق النساء على عهد النبي (صلى الله عليه وآله) اثنتي عشرة أوقيّة ونشّاً، قيمتها من الورق خمسمائة درهم.
وسائل الشيعة. باب إستحباب كون المهرخمسمائة درهم. جزء 21 / صفحة (248).
2-An karbo daga husaini dan sa'id, daga nadr bin suwaid, daga Abdullahi bin sinaan, daga Abi Abdullah (a.s) yace: Azamanin manzo (s.a.w) nauyin sadaki gwargwadon nauyin (Uqiyya) 12 ne, wanda qimar yayi daidai da dirhami 500.
Wasaa'ilush shi'a, babin abinda ake so na kasantuwar sadaki dirhami 500, juz'I na /21/ shafi na/248.
Hadisi na uku:
3-    وروى الحسن بن محبوب، عن أبي أيوب، عن محمد بن مسلم عن أبي جعفر عليه السلام قال: رجل تزوج امرأة على حكمها أو على حكمه فمات أو ماتت قبل أن يدخل بها، قال: لها المتعة والميراث، ولا مهر لها، قال: وإن طلقها وقد تزوجها على حكمها لم يتجاوز بحكمها على أكثر من خمسمائة درهم مهور نساء النبي صلى الله عليه وآله).
من لا يحضره الفقيه ج3 /ص415.
3-Hasan bin mahbub ya rawaito, daga Abi Ayyub, daga Muhammad bin muslim, daga Abi ja'afar (a.s) yacw: wani mutum ya Auri wata mata akan Abinda ya hukumta ko akan abinda ta hukumta, to sai ya mutu ko ta mutu kafin ya sadu da ita, sai imam yace: za ta ci gado, amma bata da sadaki, Amma idan saketa ya yi Al-hali ya Aureta ne akan hukumcinta to hukuncin sadakinta ba zai wuce sama da dirhami 500 ba yawan sadakin matan Annabi (s.a.w).
Manla yahduruhul faqih, juz'I na/3/ shafi na/415.

Hadisan suna da yawa amma don taqaitawa naga ya kamata mu wadatu da guda uku kadi, sannan Natijar da zamu iya fitarwa awadannan hadisai su ne:
1-manzo(s.a.w) ya Aurar da Fatima (a.s) a sadaki dirhami 500.
2-manzo (s.a.w) ya Auri matansa akan sadaki dirhami 500.
3-Ana so (mustahabi) ne yin Aure da dirhami 500.

To abin tambaya anan shi ne, shin dirhami 500 ya kai nawa idan aka kwatanta da kudin kasarmu? Watau naira.
Lallai dirhami 500 dai dai yake da dalan Ameri 135 wanda yake dai dai da 21,000 da motsi.
Wallahu A'alam
Wassalamu Alaikum warahmatullah.
 

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: