bayyinaat

Published time: 22 ,January ,2017      11:12:10
Bayan wafatin manzon tsira imam Ali (a.s) wanda shi ne ya fi kowane mutum sanin kur’ani bayan manzon rahama, ya zauna a gidansa bai wuce wata shida ba da wafatin manzon Allah (s.a.w) sai da imam Ali (a.s) ya hada kur’ani gaba dayansa a bisa jerin yadda ya sauka gaba daya, aya tana bin aya, sura tana bin sura .
Lambar Labari: 3
Saukar Da Kur’ani
Kur’ani mai girma ya sauka daga Allah sauka iri biyu; ta daya ita ce sauka daga Baitul ma’amur da yake sama ta hudu zuwa wannan saman duniya wanda ya kasance a cikin watan Ramadan. Amma sauka ta biyu ita ce; saukarsa ga manzo (s.a.w) daga saman duniya da ta faru a cikin shekaru ishirin da uku.
Amma farkon abin da ya sauka shi ne ayoyi biyar na farkon surar Alaki, ayar da take karshen sauka kuma ita ce; ayar kammala addini da ta zo a surar ma’ida, wato wani bangare na aya ta 3 a surar ma’ida da yake cewa: "A yau ne na kammala muku addininku na kuma cika ni’imata a gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini…”.

Rubuta Kur’ani
Adadin surorin kur’ani dari da goma sha hudu ne, annabin rahama (s.a.w) ya kwadaitar da musulmi a kan rubuta kur’ani mai girma har ma wasu daga sahabbansa suka shahara da sunan masu rubuta wahayi, al’amarin da yake nuna matukar damuwarsa da ganin an rubuta dukkan abin da ya sauka na kur’ani daga ubangiji (s.w.t), farkon wanda ya rubuta wahayi a Makka shi ne imam Ali (a.s) kamar yadda farkon wanda ya rubuta shi a Madina shi ne Ubayyu dan Ka’abu.
Bayan wafatin manzon tsira imam Ali (a.s) wanda shi ne ya fi kowane mutum sanin kur’ani bayan manzon rahama, ya zauna a gidansa bai wuce wata shida ba da wafatin manzon Allah (s.a.w) sai da imam Ali (a.s) ya hada kur’ani gaba dayansa a bisa jerin yadda ya sauka gaba daya, aya tana bin aya, sura tana bin sura .

Hada Kur’ani
Tun lokacin da aka aiko Annabi da sako har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (a.s) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (s.w.t) a hankali a hankali har littafin Kur'ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (s.a.w) ya yi umarni da a hada shi kamar yadda yake a yau din nan.
Manzo (s.a.w) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu'amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.
Bayan cikar addini da kafa Ali dan Abu Dalib (a.s) shugaba na al'umma kuma halifa bayan Annabi (s.a.w) wannan kuwa ya faru a ranar Gadir ne goma sha takwas ga zulhajji a shekarar hajjin bankwana sai Allah ya saukar da ayar: "A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni'imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini" . Sai Annabi ya yi rashin lafiya mai sauki, sai dai ya yi tsanani har sai da ya hadu da Ubangijinsa a 18 ga watan safar na 11H. 
Kuma wasiyyinsa halifansa Imam Ali (a.s) shi ne ya yi masa wanka da salla da binne shi a dakinsa a Madina inda kabarinsa yake yanzu.
Ya kansace abin koyi ne shi a rikon amana da ikhlasi da gaskiya da cika alkawari da kyawawan halaye, da girma, da kyawawna dabi'u, da baiwa, da ilmi, da hakuri, da rangawame, da afuwa, da sadaukantaka, da tsentseni, da takawa, da zuhudu, da baiwa, da adalci, da kaskan da kai, da jihadi.
Jikinsa ya kasance kololuwa wajen kyau da kuma daidaito da dacewa, kuma fuskarsa kamar wata ne mai haske da ya cika, kuma zuciyarsa da ruhinsa sun kai matuka wajen kamala, mafi kamalar halaye da ladabi da dabi'a kuma sunnarsa tana haske kamar rana a tsaka-tsakinta.
Atakaice, ya tattara dukkan wata dabi'a mai kyau da girma da daukaka da kuma ilimi da adalci da takawa da kuma iya tafiyar da al'amuran duniya da na lahira, wadanda babu wani mahaluki da yake da irinsu.
Wannan shi ne annabin musulmi kuma wannan shi ne addinin musulunci, kuma addininsa shi ne mafificin addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai domin shi: "Barna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin yabo" .

Annabi (s.a.w) Da Kur'ani
Daga maimunul kaddah  daga Abu Ja'afar a wani hadisi ya ce: "Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ni ina mamakin yadda na kasance ba na yin furfura idan na karanta Kur'ani".
Daga Ja'afar dan Muhammad daga babansa daga Imam Ali (a.s) a wata magana mai tsayi yana mai siffanta masu tsoron Allah ya ce: "amma da dare suna masu daidaita kafafunsu suna masu karanta Kur'ani karantawa suna masu bakin ciki kuma suna masu ishara da shi domin tayar da bakin cikinsu a kan zunubansu, da kuma jin ciwonsu (ga laifuffukansu), idan suka wuce wata aya mai ban tsoro sai su karkata zukantansu da jinsu da ganinsu zuwa gareta, kuma fatar jikinsu tana tashi sai su ga kamar suna cikin karar jahannama ne kuma kukanta yana isa kunnuwansu, idan suka wuce wata aya ta kwadaitarwa sai su yi kwadayi kuma rayukansu su tsinkaya zuwa gareta domin bege, kuma su yi tsammanin cewa kamar tana gabansu ne" .
Daga Abu Hamza assumali daga Abu Ja'afar ya ce: "Imam Ali ya ce: bana ba ku labarin masani na gaskiya ba? Shi ne wanda bai sanya mutane sun yanke kauna daga rahamar Allah ba, kuma bai sanya su sun amintu daga samun azabar Allah ba, kuma bai sanya su sun yanke kauna daga rahamar Allah ba, kuma bai ba su damar saba wa Allah ba, kuma bai bar Kur'ani ba domin kwadiatuwa zuwa ga waninsa. Kuma ku sani cewa: babu wani amfani ga ilimin da ba shi da wata fahimta cikinsa, kuma babu alheri ga karatun da babu tadabburi a cikinsa, kuma babu wani amfani ga ibada da ba bisa ilimi take ba" .

Ahlul Baiti (a.s) Da Kur’ani
Kafin mun tsawaita magana kan wannan maudu’i, muna iya nuni da cewa:
1- An ambaci sunan Ahlul Baiti (a.s) a cikin kur’ani mai girma da wannan kalma a surar Ahzab .
Kuma da yawa daga ruwayoyi sun zo suna masu bayanin su waye Ahlul Baiti (a.s) da suka hada da Ali da Fatima da Hasan da Husain (a.s) da kuma tara daga zuriyar Husain (a.s).
2- An ambace su da sunan ma’abota kusanci, kuma haka nan manzo (s.a.w) ya yi bayanin Ali da Fatima da Hasan da Husain (a.s) a matsayin su ne ma’abota kusanci
3- A ayar mubahala tafsirai da tarihi an bayyanar da su a matsayin mutanen da ayar take nufi domin su ne alamin addinin musulunci, kamar yadda kowane addini ma’abotansa na koli su suke alamta shi, mai son karin bayani sai ya duba kissar mubahala a cikin kowane littafi na tarihi da tafsiri da ya zo da labarin kissar.
4- A ayar ciyawar da ta zo a surar insan. Da sauran wurare da dama a kur’ani mai girma.
Amma alakarsu da kur’ani wani abu ne wanda yake a fili a zahiri da yake sananne gun jama’ar musulmi gaba daya, sai dai wanda yake makiyi ga wannan gida da ya rufe idanunsa ya musanta hankalinsa.
Hakika manzo ya sanya su a matsayin abubuwan da ya bari guda biyu ga al’umma wato Ahlul Baiti (a.s) da kuma littafin Allah kamar yadda yake a cikin ruwayar nan mutawatira, da fadinsa (s.a.w) cewa: Ni na bar muku nauyaya guda biyu; Littafin Allah da kuma Ahlin gidana, hakika su ba zasu rabu ba har sai sun riske ni a tafki, ba zaku taba bata ba, matukar kun yi riko da su .
Ahlul Baiti (a.s) sun zama su ne aka gwama su da kur’ani, don haka ne ma ba a taba ganin sabawarsu gareshi ba, ko kuma inda ya zama sun bar shi ko da taki daya, kuma koda wannan zai kai ga rasa rayuwarsu da dukkan abin da suka mallaka ne. 
Misali ya isa ga waki’an nan ta karbala da imam Husain (a.s) ya sadaukar da komai saboda kur’ani.
Ahlul Baiti sun fi kowa karanta kur’ani da tafsirinsa da bayanin ilimominsa, wannan kuma wani abu ne wanda yake ba sabo ba ne ko bako game da rayuwarsu, domin su ne aka gwama da shi, aka hada su a matsayin tsaransa. Idan mun so muna iya komawa zuwa ga maganar imam Ali da wasiyyarsa da karanta kur’ani domin mu ga misalai masu yawa game da hakan .
Haka nan sayyida Zahara (a.s) ta ce da Asma’u ‘yar Umais zan shiga daki domin in karanta kur’ani, hakika ni ina son karanta kur’ani, idan ba ki ji ni ba, to ki tabbata na mutu. 
Amma labaran sauran imamai game da karantawarsu ga kur’ani suna da yawa, ya zo cewa imam Hasan (a.s) yana mai yawan karanta kur’ani, idan ya wuce wata aya da aka ce: "Ya ku wadanda kuka yi imani”. Sai ya ce: Amsawarka ya ubangiji!.
Amma game da imam Husain (a.s) ya zo cewa a daren ashura ba abin da ake ji daga gareshi sai rurin muryar nan ta karanta kur’ani tun farkon dare har alfijir.
Imam Zainul Abidin (a.s) kuwa gidansa ya zama waje ne da mutane suke labewa da dare domin su ji muryarsa mai dadi tana tashi da kanshin sautin kur’ani mai girma.
Ahlul Baiti (a.s) ba su gushe ba suna masu karanta kur’ani da umarni da karanta shi, da kuma bayanin ma’anoninsa da tafsirinsa ga mutane kuma da kiyaye shi da rubuta shi, da kuma umarnin mutane da hakan.

Shi'a Da Kur’ani
Dukkan musulmi Shi'a da Sunna sun tafi a kan cewa wannan littafin na kur’ani mai girma babu dadi babu ragi shi ne littafin da Allah ya saukar ga manzon rahama Muhammad dan Abdullah (s.a.w) wanda barna ba ta iya zo masa ta bayansa da ta gabansa, idan an samu wani karkata a ma’anarsa to wannan yana tasowa ne daga malamai wadanda ba su san hakikaninsa ba sai su fassara shi bisa son ran su yadda suka ga dama.
Shi'a suna ganin cewa; mai fassara kur’ani na hakika mai gaya wa mutane abin da ya kunsa na tawili da bayani shi ne manzo (s.a.w) sannan sai Ahlul Bait (a.s) bayansa, kamar yadda ya gwama su da kur’ani a cikin wasiyyar da ya yi wa al’ummar musulmi cikin abin da ya bar musu guda biyu.

Mumini Da Kur'ani
Daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: "Bai kamata ba mumini ya mutu har sai ya koyi Kur'ani ko ya kasance a kan hanyar koyar da shi .
Daga Walidi dan Musulmi daga Abdullahi dan Hahi'a daga Musraj, daga Ukuba dan Ammar ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Allah ba ya azabtar da zuciyar da ta hardace Kur'ani" .
Daga Nu'uman dan Sa'ad daga Ali (a.s): Annabi (s.a.w) ya ce: mafificinku shi ne wanda ya san Kur'ani kuma ya koyar da shi" .
A Nahajul balaga Imam Ali (a.s) ya ce: 'ku koyi Kur'ani domin shi ne kakar zukata kuma ku nemi ceto da haskensa domin shi ne warakar zukata, ku kyautata karanta shi domin shi ne mafi amfanin kissoshi, domin ku sani masani mai aiki ba da ilmiminsa ba, kamar jahili ne mai dimuwa da ba ya farkawa daga jahilcinsa, hujja a kansa ma ta fi girma, kuma hasara gareshi ta fi lizimta, kuma ya fi zama abin zargi wajen Allah" .
Daga ma'azu ya ce: Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Babu wani mutum da zai sanar da dansa Kur'ani sai Allah ya daura wa iyayensa hular sarauta a alkiyama kuma an sanya musu kayan ado da mutane ba su taba ganin irinsu ba" .
Daga Annabi (s.a.w) cewa; ma'abota Kur'ani su ne mutanen Allah kuma kebantattunsa" .
Daga gareshi: "Mafificiyar ibada ita ce karanta Kur'ani" .
Kur'ani wadata ce babu wata wadata bayansa, kuma babu talauci bayansa" .
Daga gareshi: "mafificiyar al'umma ita ce masu hardace kuran'ani kuma ma'abota dare" .
Daga gareshi: "Kur'ani walimar Allah ce, kuma ku koyi walimarsa yadda zaku iya, wannan Kur'ani igiyar Allah ce kuma haske bayyananne kuma waraka mai amfani, kuma kariya ga wanda ya yi riko da shi kuma shi tsira ne ga wanda ya bi shi" . har zuwa karshen hadisi.
Daga gareshi:  Kur'ani har ya bayyana shi, ya kuma kiyaye shi, Allah zai shigar da shi aljanna kuma ya ba shi ceton mutane goma daga ahlin gidansa dukkaninsu wutar jahannama ta riga ta wajaba a kansu" .
Daga gareshi: "Masu hardace Kur'ani a duniya su ne masanan malaman aljanna a ranar kiyama" .
Daga gareshi: "idan malami ya ce da yaro:ce ne: Bismillahir rahamanir rahim, sai yaro ya fada to Allah zai rubuta wa yaro da iyayen yaro da malaminsa kubuta daga wuta" .

Saurayi Da Kur'ani
Daga minhal alkassab , daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: " Kur'ani yana saurayi mumini kuma ya cakuda Kur'ani da namansa da jininsa Allah zai sanya shi tare da safaratul kiram masu daraja na mala'iku, kuma Kur'ani zai kasance mai kariya gareshi a ranar kiyama, yana cewa: ya Ubangiji duk mai aiki ya samu lada ban da mai aikina, ka ba shi mafi girman kyautarka. Ya ce: sai a tufatar da shi tufafin ado guda biyu na aljanna, kuma a sanya masa hular girma a kansa sannan a ce da shi: shin ka yarda da abin da muka yi masa? sai Kur'ani ya ce ni na yi masa fatan sama da hakan sai a ba shi aminci a hannun damansa da dawwama a hagunsa, sannan sai ya shiga aljanna sai a ce karanta aya sai ya karanta ya sake daukaka daraja, sanan sai a ce da Kur'ani yanzu ka yarda da abin da muka yi masa, sai ya ce E. ya ce:  shi da yawa ya saba da karanta shi da kyar da wahala Allah zai ba shi lada biyu ne" .
Daga Aban dan Taglib daga Abu Abdullah ya ce "wanda ya samu Kur'ani ya yi imani da shi to kamarsa kamar doddoya (lemon masar) ce da take da kamshi kuma cikinta mai dadi, amma wanda bai samu Kur'ani ba kuma bai yi imani da shi ba kamar kubaku ne da dandanonsa mai daci kuma ba ta da wani kamshi .
Daga Fudail dan yassar daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ku koyi Kur'ani, domin shi zai zo ranar kiyama ga ma'abocinsa a surar saurayi mai kyau, yana mai launi mai ado, sai ya ce da shi: ni ne Kur'anin da ka kasance ka raya darenka ka yi kishirwantar da makogwaronka, ka busar da yawunka ka kuma zubar da hawayenka (har ya ce) ka yi murna, sai a zo da wata hula sai da dora a kansa sai a ba shi aminci a damansa dawwama kuma a aljanna a hagunsa, kuma a tufatar da shi kayan ado biyu sannan sai a ce da shi: ka karanta ka samu daukakar daraja, kuma duk sa'adda ya karanta aya sai ya daukaka da daraja kuma a tufatar da iyayensa kayan ado biyu idan muminai ne, sannan sai a ce da su wannan saboda kun koya masa Kur'ani ne" .
Daga Asbag dan Nabata ya ce: "Imam Ali (a.s) ya ce: Allah yakan so ya azabtar da mutanen duniya gaba daya, ta yadda babu wanda zai tsira daga cikinsu idan suka yi aiki da sabo kuma suka yi miyagun laifuffuka, amma idan ya duba ma'abota furfura masu taka kafafunsu zuwa salloli da kuma yara masu koyon karatun Kur'ani sai ya tausaya musu ya jinkirta wannan daga garesu" .

Tajiri Da Kur'ani
Daga Fudail dan Yassar  daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: me zai hana tajiri a cikinku mai shagaltuwa a kasuwancinsa idan ya koma gidansa kada ya yi bacci har sai ya karanta sura ta Kur'ani, sai a rubuta masa kowace aya da yake karantawa lada goma kuma a shafe masa zunubai goma".
Daga Sa'ad dan Darif, daga Abu Ja'afar Bakir (a.s) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w) ya ce:  ayoyi goma a kowane dare ba za a rubuta shi daga masu gafala ba, wanda kuma ya karanta ayoyi hamsin za a rubuta shi daga masu ambaton Allah da yawa,  ayoyi dari za a rubuta shi daga masu ibada,  ayoyi dari biyu za a rubuta shi cikin masu khushu'I,  ayoyin dari uku za a rubuta shi cikin masu rabauta,  ayoyi dari biyar za a rubuta shi cikin masu ijtihadi,  ayoyi dubu to za a rubuta masa sisi, sisi kuwa shi ne awo dubu goma sha biyar na awon zinare… mafi karanci kamar girman uhud, mafi girmansa kamar tsakanin sama da kasa.
Daga Abu Hamza assumali daga Abu Ja'afar (a.s) ya ce: wanda ya kammala Kur'ani a Makka daga juma'a zuwa wata juma'a ko kasa da hakan ko sama da haka to Allah zai ba shi lada daga farkon juma'a ta duniya zuwa ta karshe ta duniya, kuma haka nan ma sauran ranaku" .
Daga Jabir, daga Abu Ja'afar (a.s) ya ce: "Kowane abu yana da kaka, ku sani kakar Kur'ani shi ne watan Ramadan" .

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
12 Rabi’ul awwal 1427 - 22 Parbardin 1385 - 11 Afrilu 2006

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: