bayyinaat

Published time: 02 ,February ,2017      07:46:06
Amma abin sani game da Manzo (s.a.w), ya auri mata daya ne da ya rayu da ita tun yana shekara ashirin da biyar tana da shekaru arba'in har kusan karshen rayuwarsa yana dan shekara hamsain. Haka ya zauna (s.a.w) da mace daya bai sake aure ba yana ta ibada da tunanin fitar da al’umma daga kangin bautar mutum zuwa ‘yancin bautar Allah. Bai auri ta biyu ba sai bayan yana dan shekara hamsin da uku a lokacin ya manyanta.
Lambar Labari: 30
Amma sukan da kuka yi kan yawan matan Manzo (s.a.w) zaku samu raddi mai kaushi daga alkalami mai raddi da taimakon Allah (s.w.t) . Ku kun ce: Yawan matan ko ya zama don sha’awa ko don son su. 
Sai mu ce: Amma son mata ba aibi ba ne, al’amarin son mata ga namiji yana daga cikin kamala da cika da daukaka, domin wanda ba ya son su to lallai akwai nau’in tawaya ko na ruhi ko na jiki ko kuma na tunani da yake tare da shi ne, kamar yadda sha’awa ita ma ba aibi ba ce, ita nau’i ce ta halittar Allah da ya yi wa dan'adam, kuma matukar ya kiyaye ta bisa yadda ya gindaya masa to zai ma samu ladan Allah ne. 
Sannan kuma aure domin sha’awa wani abu ne mai wuyar ganewa domin yana bukatar ka san mai auren da dalilinsa na yin auren. Da wani zai yi aure ba wani da ya isa ya danganta shi da sha’awa, galibin aure yana kasancewa ne domin kame kai. Sannan kuma yawanci irin wannan yana bukatar budurwa ne da shi mai auren zata iya dauke masa kewar sha’awar tasa sabanin macen da ta manyanta sosai ko ta tsufa. 
Amma abin sani game da Manzo (s.a.w), ya auri mata daya ne da ya rayu da ita tun yana shekara ashirin da biyar tana da shekaru arba'in har kusan karshen rayuwarsa yana dan shekara hamsain. Haka ya zauna (s.a.w) da mace daya bai sake aure ba yana ta ibada da tunanin fitar da al’umma daga kangin bautar mutum zuwa ‘yancin bautar Allah. Bai auri ta biyu ba sai bayan yana dan shekara hamsin da uku a lokacin ya manyanta. 
Idan dai ba neman sukan fiyaiyen halitta ba, wane irin rashin hankali ne zai kawo batun sha’awa a wannan hali. Alhalin ga shi tun da ya fara kira yana cikin takurawar sanya masa takunkumi, ga yake-yake, ga shi kuma kowane wata ana kawo masa hari, ga kafiran Kuraish, ga na Jazira, ga munafukan cikin gida, ga Rum, ga Farisa, ga Yahudawan jazira da Madina da Khaibar, ga kiristocin Yaman, ga sallar dare wajibi ce a kansa, ga azumi a kansa, ga shiryarwa da koyarwa ga duniya, da abubuwa masu yawa da ba za su kirgu ba. Da sha’awa ce ta sanya yin auren da ya yi aure-auren tun yana saurayi kuma da bai auri masu shekaru da suka manyanta ko suka tsufa ba, ku duba shekarunsa da shekarunsu mana ba ‘yan mata ba ne. Duba ku ga Ummu Salama ta haura hamsin haka ma Zainab ‘yar Jahsh. 
Sannan su matan ne suke alfahari da aurensa, har ma an ba su zabi cewa suna iya barinsa in sun so amma suka zabe shi . Kuma yawanci aurensu ya kasance da manufar cimma hadafin musulunci kamar kira zuwa gare shi ko shiryar da wata al’umma. Wata kuwa mijinta ya yi shahada kuma ga ta da ‘ya’ya masu yawa kuma ba mai kula da su ko mai renonsu. Wasu kuwa don karfafa Musulunci, ko don sun bayar da kansu ga Annabi shi kuwa ba ya iya kin karbar su, ko don al’ummarsu su musulunta. 
Duba matar da ya aura Sauda wannan ya kasance don an kashe mijinta a Uhud ne wato Abdullahi Dan Jahsh, kuma tana da alheri har ma ana cewa da ita "Uwar miskinai" saboda alheri da tausayi, sai ya aure ta don ya debe mata kewar rashinsa. Haka ma Ummu Salama mumina mai ibada da tunani mijinta ya mutu tana tsohuwa ga ‘ya’ya da yawa. Ga Safiya da an kashe mijinta ne a Yakin Khaibar, don haka Manzo ya sadar da zumuncinsa da ‘Ya’yan Isra’ila. Haka ma auransa da Zuwaira ya sa musulmi sun ‘yanta mutanenta. Maimuna kuwa ta bayar da kanta ga Annabi ne, ga Ramla ya aure ta don dakewarta a kan musulunci bayan mijita ya zama Kirista a Habasha lokacin da suka yi hijira zuwa can. Kuma ya auri Hafsa ne saboda an kashe mijinta a Badar, ga A’isha ya aure ta budurwa mai shekaru kusan goma sha takwas bisa magana mafi inganci ba tara ba kamar yadda ya shahara gun wasu marubuta, wannan dalilai ne a kan sabanin da’awar ‘ya’yan Jahiliiyar yamma a kansa mai tsira da aminci 
Amma sukan da kuke yi game da yawansu wannan wani abu ne da Allah ya kebance shi da shi kamar yadda ya kebance shi da wajabcin sallar dare, da annabta, da wahayi, da fara kai hari, da azumin wisali, da kai hari Makka sau daya. Don haka a wancan lokacin hatta da makiyansa ba su taba sukan sa da auran mata da yawa ba, domin duk wanda ya yi haka ba mai yarda da maganarsa ko ma ya zama abin yi wa izgili, ba kamar yadda shi mutumin yamma a yanzu da ya ke har yanzu bai waye ba yake wannan sukan yana jingina tawaya ga fiyaiyen halitta. 
A yanzu ku ba ku san cewa akwai abubuwa da su ka kebanta da Isa (a.s) ba a zamaninsa! Wa yake raya matacce ko warkar da marasa gani? Sannan duk kisan da ake yi ba wanda aka dauka sama sai shi? saboda haka Allah ya kebance Annabinsa da wasu dokoki ba laifi ba ne kuma ba aibu ba ne. 
Daukaka sha’anin mata yana daga cikin abin da zamu iya fahimta a wannan auren nasu da shi (s.a.w), domin aurensa ya daukaka sha’aninsu kuma ya nuna wa duniya cewa; da su ne komai zai iya ci gaba, kuma da su ne ya kamata a tafi kafada da kafada kamar yadda yake a tarihin dan'adam da ci gabansa, sabaninku da kuka mayar da mace domin cimma burin rayuwar Duniya. Don me ya sa ba mu ga kuna suka kan wani Addini ba sai na musulunci? Ko don hassada da kuke masa cewa Addini ne cikakke kuma fiyaiye daga kowanne mai kunshe da dokoki da tsari kammalalle. 
Sukan Yamma ya yawaita kan musulunci, wata mata  ta kasance tana nuna damuwarta kan yadda suke shan suka a ajinsu, har ma wata rana ta taba tambaya cewa: Yaya zata iya bayar da amsa a makaranta a London da a kan nuna masu musulunci kamar cibayaiyen Addini musamman yayin da ake nuna wasu mata a kasar Afganistan?. A irin wannan babu wata amsa sai cewar addinin musulunci daban aiki ko fahimtar musulmi daban, domin su wadannan matan imma dai suna hada musulunci da al’adunsu ko kuma sun yi wa musulunci wata fahimta ne. Idan kuwa masu sukan suna nufin hijabin mata shi ma fahimta ce da kowa ya ikance nau'insa bisa mahangarsa. Amma idan suna nufin rufe tsaraici ne, to suna bakin ciki ne da samun wasu mata da ba sa ba wa wani mutum damar ganin tsaraicinsu balle fasadi ya yadu. Haka nan Musulunci yake kafa dokokinsa bisa maslaha da kare hakkin iradar mutane matukar ba zai bude musu hanyar fasadi da ta saba da hadafin halittar dan'adam ba. 
Da za a kwatanta Musulunci da sauran addinai da ka ga fifikon musulunci da hikimarsa a kansu, amma abin takaici shi ne a duniyar musulmi an samu wasu masu sandararren tunani da suke kallonsa ta mahanga tsukakkiya sai su nuna shi a duniya da wata fuska daban, sau da yawa irin wannan lamarin yakan jawo masa suka har ya sanya makiyansa su rika yi masa wani kallo da ya saba wa hakikaninsa. 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: