bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:17:58
kuma muka yi lissafin cewa idan mun kwatanta da dirhamin da muke amfani da shi yanzu zai kama dala 135 wanda yayi dai dai da #21,000 da motsi
Lambar Labari: 300
Da sunan Allah maia rahama mai jinqai, tsira da Amincin Allah su tabbata ga manzo da Alayensa tsarkaka managarta.
 Cikin yardan Allah yanzu ne na samu damar ci gaba da kawo bahasin da na fara kashi na biyu duk wanda ke biye damu a bahasin da ya gabata mun kawo Hadisan da suka tabbatar da cewa sadakin manzo (s.a.w) da sayyida fatma (a.s) dirhami 500 ne, kuma muka yi lissafin cewa idan mun kwatanta da dirhamin da muke amfani da shi yanzu zai kama dala 135 wanda yayi dai dai da #21,000 da motsi. Sai dai akwai tambayoyi kamar haka:
1-Tambayar itace: shin dirhamin da ake amfani da ita a zamanin manzo (s.a.w) itace irin wacce ake amfani da ita yanzu aqasar Emaarat??? Idan itace shikenan (sabatal matlub), watau bahasin da muka gabatar ya wadatar.
2- Amma idan ba da ita bace, to tayaya zamu iya gane qimar dirhamin  zamanin manzo (s.a.w) da kudin zamaninmu??? Musamman da naira.
3- Shin dirhami 500 a zamanin manzo (s.a.w) kudi ne mai yawa ko kuma kudi ne kadan ???
Daukkan wadannan abubuwa guda uku muna so mu tattauna a sadakin manzo (s.a.w) kasha na 3, in sha Allahu sai a biyomu a karo na gaba nan da Awa 72. Wallahu A'alam
Wassalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: