bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:20:36
Amsar tamabayar farko itace: a a, watau dirhamin da Ake amfani da shi zamanin manzo (s.a.w) ba shi ne
Lambar Labari: 301
Da sunan Allah maia rahama mai jinqai, tsira da Amincin Allah su tabbata ga manzo da Alayensa tsarkaka managarta.
A ci gaba da yin bayani akan SADAKIN MANZO (s.a.w) mun tsaya ne a inda muka kawo wasu tambayoyi guda uku da suke buqatar Amsa gasunan kamar haka:
1- shin dirhamin da ake amfani da shi a zamanin manzo (s.a.w) shi ne irin wanda ake amfani da shi yanzu aqasar Emaarat??? Idan shi ne shikenan (sabatal matlub), watau bahasin da muka gabatar ya wadatar.
 2-Amma idan ba da shi bane, to tayaya zamu iya gane qimar dirhamin  zamanin manzo (s.a.w) da kudin zamaninmu??? Musamman da naira.
 3-Shin dirhami 500 a zamanin manzo (s.a.w) kudi ne mai yawa ko kuma kudi ne kadan???
AMSA:
1-Amsar tamabayar farko itace: a a, watau dirhamin da Ake amfani da shi zamanin manzo (s.a.w) ba shi ne wanda ake amfani da shi a yanzu ba, don kuwa dirhamin da ake amfani da shi a zamanin manzo (s.a.w) shi ne (fidda maskuk) qerarren Azurfa, wanda guda 10 dai dai yake da (zahab maskuk) qerarren zinare guda 1.
2-Amsar tambaya ta biyu itece: yanzu zamu iya kwatanta qimar dirhamin zamanin manzo (s.a.w) ne ta hanyar kwatanta nauyin qerarren Azurfa 500, ko nauyin zinare 50 kamar yadda wasu malaman sukace.
3-Amsar tambaya ta uku itace: a zamanin manzo (s.a.w) dirhami 500 ba shi da qima, watau ba kudi ne masu yawa ba, don bai wuce kudin sulke ba.
Amma abin tambaya anan shi ne: to idan aka kwatanta da kudinmu zai kai nawa???
 A yau 20/6/1434 wanda yayi dai dai da 11/2/1392 da watan shamsiyya, kuma yayi dai dai da 1/5/2013 na watan girigori, mithqaal na Azurfa khalis ya kai kimanin Tuman din kasar iran 14,700 wanda dari 500 zai kai kimanin 7,350,000 na Tuman, wanda zai kai kimananin Dalan Amerika 2400 wanda idan muka maida shi da Naira zai kai 380,00 da motsi,  zuwa 400,000 bisa sabani, wanda hakan ke faruwa sakamakon qimar Azurfa daga kasa zuwa kasa ta daban.
To meye abunyi? Shin yanda muka kawo daga farko ne watau Naira dubu 21, ko kuma yanda yanzu muka kawo ne watau 400,000? Don bada cikekken Amsa sai a biyomu a Bahasi na gaba nan da Awa 48 wanda shi ne zai kasance bahasinmu na qarshe akan Sadaki. Wallahu A'alam
Wassalamu Alaikum wa rahamatullahi wabarakaatuhu.
 
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: