bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:23:13
Lambar Labari: 302

Da sunan Allah maia rahama mai jinqai, tsira da Amincin Allah su tabbata ga manzo da Alayensa tsarkaka managarta.
A ci gaba da yin bayani akan SADAKIN MANZO (s.a.w) mun tsaya ne a inda muke cewa: To meye abunyi? Shin yanda muka kawo daga farko ne dai dai watau Naira dubu 21, 000 ko kuma wanda muka kawo daga baya ne dai dai watau 400,000? Amsa nan shine: ita dai sayyida Azzahra (a.s) sadakinta shi ne dirhami 500 wanda yayi dai dai da 380, 000 zuwa 400, 000, wanda da shi ne aka saya mata kayan daki daki da shi, to mu ayanzu meye Takalifinmu?
Amsa:
Takalifinmu shi ne yin aiki da abinda maraji'u suka mana umrni da shi, to amma tambaya anan shi ne shin meye maraji'un suka umrcemu da shin?  
Amasa:
Maraji'u sun umurcemu da yin sauki a sadaki, kuma sun hanemu da yin tsada a sadaki, sannan tsadan sadaki ko saukinsa ya danganta ne daga kasa zuwa kasa, kenan tsadar sadaki ko saukinsa yana da alaka da yadda su mutanen kasar suka tafi akai, misali: idan mutanen kasa suka tafi akan cewa duk sadakin da ya wuce naira dubu hansin 50 yayi tsada to makaruhi ne kai ka bada fiye da haka, sannan mustahabi ne ka bada kasa da haka ko kamar hakan, sannan yana daga cikin daukaka da daraja ga matar da aka biyata sadaki kadan, kamar yadda muka tabbatar da haka ahadisan da muka kawo abaya, don sayyida Zahra (a.s) sadakinta kadan ne kamar yadda malami suka tabbatar mana, shi yasa ma suke hani kan tsadar sadaki, misali: malaminmu Allama  Assayyida hashimul madari yace:(yin tsadar sadaki ba maslaha bane ga Al-umma, kuma ya qara da cewa sadaki sayyida azzahra (a.s) kadan ne, ba mai yawa ba), da sauran maraji'u da sukayi hani akan tsadar sadaki irinsu:
1-Assayyidul qaa'id.
2-Allama nasir makarim shirazi.
3-Allama bahjat, da sauransu, don haka natija anan itace: yin tsada a cikin Aure makaruhi ne, kuma yin sauqi acikin Aure mustahabi ne, kuma sauqi ko tsadan shi, sai abinda urfin mutane suka tafi akai. Wallahu A'alam
Wassalamu Alaikum wa rahamatullahi wa barakaatuhu.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: