bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:27:31
Manzon Allah (s.a.w) a zamanin Jahiliyya ya zo Duniya. Kalmar jahiliyya daga jahilci ta samo asali, wato ma’ana rashin sani, saboda hakane ma kur’ani mai girma bayan
Lambar Labari: 303
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai, Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Mafificin Halittun Allah Kuma Manzonsa Muhammad Dan Abdullahi (S.A.W) Da Iyalen Gidansa Tsarkaka Wadanda Allah Ya Tsarkake Daga Barin Duk Wani Sabo.
Yau sarkin sarakuna Ubangijin halittu kuma ya sake nufarmu da yin rubutu akan fiyayyen halitta Annabin mu Annabi Muhammad (s.a.w), insha Allah zamu fara Magana tun daga haihusar sa (s.a.w) har zuwa abinda ya sauwaka cikin tarihinsa fiyayyen halitta (s.a.w). dafatan zaku biyomu sannu a hankali, Allah ya bamu da cewa da samun Albarkacinsa (s.a.w).
    WASU DAGA CIKIN SIFFOFIN JAHILIYYA.
Manzon Allah (s.a.w) a zamanin Jahiliyya ya zo Duniya. Kalmar jahiliyya daga jahilci ta samo asali, wato ma’ana rashin sani, saboda hakane ma kur’ani mai girma bayan zuwan musulunci yake buga misali da ayyukan wasu da irin ayyukan jahiliyya, abinda kur’ani yake nufi a nan ba wai kawai jahilcin ba, a a duk ma wani aiki daya sabawa ko yarwar musulunci yana hukunta shi a matsayin aikin jahiliyya, tun kafin aiko Manzon Allah (s.a.w) sama da shekaru 150 duk lokaci ne na jahiliyya(1) .
SIFFOFIN  MUTANE  A LOKACIN JAHILIYYA.
Na farko: Kabilanci da rashin tsayayyar hukuma. Na  biyu: Matsalolin rashin Aklak da kuma yake-yaken cikin gida. Na uku: Rashin sanin Allah shi ya cancanci a bauta masa da kuma zuwan wasu addinai na karya. Na hudu: Rashin ilimi da tsarin karantarwa.
Na farko: Kabilanci da rashin tsayayyar hukuma: A wancan zamanin mafi yawancin  Larabawa suna rayuwa ne a sahara wurin da babu ruwa babu abinci kai hattama da ciyawar da Dabbobin su zasuci a irin wannan wurin da suke rayuwa babu,  wannan ne abinda ya tilasta larabawa neman duk wani wurin da zasu samu abinci da ruwa da kuma abincin da Dabbobin su zasuci. Saboda hakane ma mafi yawancin aikin su ya zama kiwun Rakuma da Dawaki da sauran Dabbobi saboda neman abinci, Dai dai kunsu kan karbi kiwun Dabbobi domin samun abinda zasu rayu da shi, suna yawu a cikin sahara a tsakankanin larabawa, wannan ya taimaka wajen rashin tsari da rashin samun hukuma tsayayya a kasashen larabawa, saboda haka larabawa suna sake ne batare da wata duka da tsarin rayuwa ba.
Hakan yasa  dole larabawa suka kasance cikin matsalolin tsananin zafin sahara a kai a kai, ga kuma yaki da yake faruwa a wancan bangaren a kai akai wanda  wancan rashin tsarin ya haifar a tsakanin su shima saboda neman samun nasara akan saura, tunda a wancan lokacin mai karfi shi keda iko kuma shi ake tsoro, wato duk kabilar da ta zama tanada karfi dole a sallama mata. Saboda samun galaba akan saura da kuma kawar da matsalolin kai da kai suna rayuwa ne a matsayin Kungiyoyi; wanda a jefa guda kuma ba wanda ake da aminci dashi. Saboda haka rayuwar larabawa ta doro ne akan asasin kabila, dole ne kayi kabilanci ka kare kabilarka, saboda hakane ma idan aka taba dan kabilar ku ko koma dan kabilar taku ne ya jawu fada dole ka kareshi, wannan yana nufin koda bashi da gaskiya ko kuma shine yayi zalunci a kan wani, ma’auni kawai shine dan kabila kaza ne, dole a kareshi batare da wani sharadi ba.
Mafi mahimmancin siffofin rayuwar kabilanci: 1 A tsarin kabilo dole ne ko wane dan kabila ya yi biyayya ga shugaban kabila. 2 Duk wani dan kabila dole ne ya kare kabilarsa kuma a irin wannan yanayin waye ya yi zalunci ko kuma waye a ka zalunta bashi da wani muhimmanci. 3 sannan ba wani wanda yake da hakkin warwar bai’arsa, dole da abinda yake dai-dai dama wanda ba dai-dai bane ka yarda dashi, wato dai-dai da rashin dai-dai bashi da wani muhimmanci.
Na biyu: Matsalolin rashin aklak da kuma yake-yaken cikin gida: Kabilu sun rayu cikin mummunan rashin ladabi da mafi munin wahala a wancan zamanin na jahiliyya, wanda a hakikkanin gaskiya zamu iya ma siffanta wancan rayuwar tasu da kamar  rayuwar Dabbobi a daji. A lal misali mutum yakan iya binne yarsa da ranta batare da wani hakki ba, sannan sukan kashe ya yansu daboda tsoron talauci kamar yadda Al kur’ani mai girma ya tabbatar suna yi(2) . Sai dai duk da haka a tsakankanin larabawa cin amana wani abune da suke ganin shi da matukar muni wanda akanshi har sukan iya yin dafa’i, amma kuma gaskiya da karya bata da wani muhimmanci a wajen su. A hakikan nin gaskiya larabawa a lokacin jahiliyya basu da wani tsari guda daya, ko kuma a ce wata gwamnati taka mai-mai, rayuwa ce kawai wacce zamu iya cewa ta jeka nayi ka. Tabbas daya daga cikin dalilan da sukasa larabawa shiga wannan yanayin bai wuce kare kai daga abokan gaba ba, saboda ba wanda zai kareka tunda ba wata gwamnati a tsakanin su.
Na uku: Rashin sanin Allah ne ya cancanci a bauta masa da kuma zuwan wasu addinai na karya: Al kur’ani mai girma yana cewa: Annabi Ibrahim shi dansa Annabi Isma’il sunje Makka kuma suka gina dakin Ka’aba akan Addini da Tauhidi saboda mutanan larabawa suyi kuyi da hakan(3) . Amma saboda tsawun zamani  da yake wucewa yau da kunlum Akidar Tauhidi da yake tare da hukuncinsa, ta bangaren larabawa sai suka canza shi zuwa shirka da bautar Gumaka, sai suka wayi gari mafi ya wancin larabawa mushirikai ne. tabbas a zahiri akwai wadanda suka yi saura akan wannan addinin na Annabi Ibrahim da sunnarsa, amma dai a nan abinda muke so a kula da shi shine mafi yawancin larabawa a wancan lokacin mushirikaine, misali kuma a nan shine, mafi yawancin su suna matukar girmama ka’aba, amma kuma gaba daya zagayen dakin ka’aba din kewaye yake da Gumakansu daban-daban, ko kuma wata biyayya da ake yiwa addinin Ibrahim shine a watanin Haram basa yaki, amma kuma watan nin na wucewa za a ko kuma gidan jiya(4) .
MAFI MUHIMMANCIN ADDINAI A LOKACIN JAHILIYYATIL ARAB.
A   shirka da bautar gumaka. B  Yahudanci. C   Kiristanci. D  sai addinin Annabi Ibrahim.
A    shirka da bautar gumaka: kamar yadda mukayi bayani a baya a lokacin jahiliyya shine mafi yawancin mutane suke akanshi, mushirikai ne masu bautar gumaka, duk da cewa suna da akidu ma banbanta amma mafi yawansu bautar gumaka ne babban addinin su, mafi yawancin mushirikai basu yi imani da kiyama ba, sannan manyan shuwagabanin kabilu sune suke ayyana addinin da za a yi, saboda hakane ma ko wace kabila akwai irin hukunce-hukunce da dokokin data ke banta dasu.
B   Yahudawa: A gefen madina ko kuma muce garin Yasrib akwai yahudawa kuma da suke rayuwa, wadanda suke da tsari da kuma nizami mai kyau, kai harma da tattalin arzikinsu mai kyau. Mafi yawancin su sunzo Yasrib ne saboda bushara da akayi musu acikin  littattafansu cewa Annabin karshen zamani a wannnan yanki za a haife shi. wato a kasashen larabawa, saboda hakane ma kungiyoyi daban-daban na yahudawa suka yo hijira daga kasashen su zuwa wannan wuri. Tabbas yahudawa tsawun lokaci suna zaune a wannan wuri, sai dai basu iya cin nasarar jawo dai-dai ko cikin addinin suba(5) .
Zamuci gaba a kasha na biyu insha Allahu sai a biyo mu sannu a hankali. Allah ya bamu dacewa.

Aliyu Abdullahi Yusuf: What’sapp, Telegram, Istgram, Facebook da sauran social Media Number: +2348037493872. Ko kuma email address y.aliyuabdullahi@yahoo.com.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: