bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:34:07
Addnin Annabi Ibrahim: a baya munce kafin larabawa su shiga shirka da bautar gumaka suna kan addinin Annabi Ibrahim ne kuma shi suke yi wa biyayya; amma yau da kunlum da gushewar zamani yasa larabawa suka kuma shirka da bautar gumaka.
Lambar Labari: 304
TARIHI KASHI NA BIYU CI GABA DAGA KASHI NA FARKO.
C   Kiristoci: akwai samuwar wasu dai-dai kun masu biyayya ga addinin kiristanci a zamanin jahiliyya a tsakanin larabawa wadanda suka yi rayuwa cikin larabawan. Amma adadin su da kuma yaduwar su bai wuce wani dan adadi ba. Mafi yawancin kiristoci a kasashen larabawa sun rayu ne a tsakanin yankin Najaran, da Yaman, kuma ta bangaren kasar Ruma suke karbar umarni. Kafin bayyanar addinin musulunci kiristoci masu da abokan gaban da suka wuce Yahudawa, in banda kiristocin Najaran da aka yi mubahala tsanin su da musulmai ba wasu kiristoci da suka yi saura(1) .
D   Addnin Annabi Ibrahim: a baya munce kafin larabawa su shiga shirka da bautar gumaka suna kan addinin Annabi Ibrahim ne kuma shi suke yi wa biyayya; amma yau da kunlum da gushewar zamani yasa larabawa suka kuma shirka da bautar gumaka. Sai dai duk da haka akwai wadanda suka tsaya akan wannan addini na Annabi Ibrahim wanda duk da wannan canjin zamanin basu bar wannan addini ba, ko kadan basu shiga cikin masu shirka da bautar gumaka ba, Akidar su ta kadaita Allah bata canza ba, wadanan mutan sune ake kira da ( Hunafa),wanda suka wanzu akan hukunce-hukunce da kuma shari’ar Annabi Ibrahim (a.s) kuma suke yi aiki da ita, mafi yawancin su tsarkakane kuma masu Aklak ne. Yan shi’a sunyi imanin cewa wadanan mutanen da suka tsayu akan addinin Ibrahimi kakannin Manzon Allah (s.a.w) ne, kuma gaba dayan su tsatsan su mai tsarki ne(2) .
ILIMI DA TSARIN KOYARWA A LOKACIN JAHILIYYA.
 Abinda kawai bashi da kima da mutumci a lokacin Jahiliyya shine ilimi, ilimi a wacan lokacin bashi da wani muhimmanci a tsakanin larabawan jahiliyya, saboda hakane ma a tsakanin su matsal tsalin da suka kewayesu basu wuce canfe-canfe da kuma wasu Akidu marasa tushe ba wanda jahilci da duhun kai ya haifar musu dasu; ga misali zamu dan buga, idan baka so kaji zafin rana lokacin da sahara take da tsananin zafi to ka sa riga a bai bai, ko kuma saboda neman kariya sai mutum ya zo bakin kofar gari ya tsaya idan yaji kukan jaki sai goma 10 to ba abinda zai same shi! Haka kuma idan mutum zai yi tafiya sai ya samu wani dan yankin kyalle ya daura shi jikin rashen wata bishiya, idan ya dawu daga tafiyar tashi sai ya zo wurin wannan rashen daya daura kyallen nan idan ya samu kyallen a daure to wai hakan yana nufin zai samu natsuwa cewa lallai matarsa mataci amanarsa ba, idan kuma ya samu wannan kyalle an kwance shi to tabbas matarsa ta ha’ince shi, saboda zai tuhumeta da laifin ha’inci kenan, ko kuma idan Rakumi ya tsallaka kabarin wani mutum to wai hakan yana nufin mutumin baya girmama shugaban kabilarsa, idan kuma bai tsallaka ba to tabbas yana girmama shugaban kabilar sa, da sai sauran camfi da suka yi fama da su a lokacin jahiliyya(3) .
Ubangiji madaukakin sarki yana bamu labari cikin littafinsa mai girma: Daya daga cikin hadafin aiko Manzon Allah (s.a.w) shine kawar da wadannan kurafat din da mutane suka nutse a cikin su, kuma ko kadan Manzon Allah (s.a.w) bai bada dama akan ci gaba da yin wadannan kurafat din ba, shi yasa saboda ko Karin cimma wannan hadafin na kawar da wadannan kurafat din bai bada dama a ci gaba da yin wasu abubuwa da suka saba ammafani dasu a lokacin jahiliyya ba.
HAIHUWAR MANZON ALLAH (S.A.W) DA KUMA WASU DAGA CIKIN KUNYARSA DA KUMA LAKABINSA  DAMA  ZUWA  WAFATINSA (S.A.W).
Manzon Allah (s.a.w), Annabi Muhammad (s.a.w) an haife shi ne a ranar 17 ga watan Rabi’u Auwal, a shekara ta 570 miladiyya wato ( shekaru 53 kafin Hijira kenan a shekarar gewaye) a garin Makka(4) .
Sunan mahaifinsa Abdullahi dan Abdul Mudallib, Mahaifiyarsa kuma sunan ta Amina Yar wahab bini Abdul Manaf.
Sananniyar kunyar Manzon Allah (s.a.w) ana kiransa da Abul kasim, da kuma lakabobinsa sanannu ana ce masa: Habibullah, Abdullahi, Sayyidul mursalin, Katimul Anbiya’u, da kuma Rahmatun lil alamin(5) .
Sannan Manzon Allah (s.a.w) ya yi wafati ne a ranar 28 ga watan safar Hijira nada shekara 11 wanda hakan ya yi dai-dai da shekaru ( 633 miladiyya) yana da shekaru 63 kenan ya yi wafati, kabarinsa mai girma yana garin Madina kusa da masallacinsa mai tsarki, Manon Allah (s.a.w) yanada ya ya bakwai maza uku mata hudu, duk kansu kafin wafatinsa suka rasu sai Fadimatu kadai ta rage har bayan wafatinsa (s.a.w) da wata shida a mafi tsawun ruwaya tayi wafati(6) .
       KAKAN NIN MANZON ALLAH (S.A.W).
Kakannin Manzon Allah (s.a.w) sanannu ne har zuwa kusan mutum 21. Sun shara da ilimi da kuma Aklak tsakanin larabawa ta yadda ba wanda ya kaisu ilimi da Aklak gaba daya a yankin kasar larabawa. Sannan ita wannan nasaba ta Manzon Allah (s.a.w) tana danganewa ne zuwa ga Annabi Ibrahim (a.s). sai dai Adadin kakan nin Manzon Allah (s.a.w) da sunayensu akwai sabani a kansu.
Kakan Manzon Allah (s.a.w) na hudu sunan sa ( Kussi bn Kilab). Wanda a lokacin samartakarsa larabawa suke kewaye dashi yana jagorantar su, sannan da wanda yake shugabantar al’amarin Dakin Aka’aba mai suna ( Kuza’a). Bayan Kuza’a ne sai Kussi ya karbi ragamar al’amuran Ka’aba da kuma shugabancin Kuraishawan Makka, a wannan gari ya rayu. Sannan shine dai wanda ya gina ( Darul Nadwa) Darul Nadwa wurine da dai dai kun kuraishawa suke haduwa domin yin shawara akan muhimman al’amura.
  Kussi ya yi shura wajen gina Darul Nadwa da kuma a cikin kuraishawa, bayan haka kuma ya yi suna wajen yiwa baki mahajjata hidima sannan mafi yawancin kabilun kuraishawa suna matukar girmama shi.
  Bayan wafatin Kussi, Dan yayansa ( Abdu Manaf) ya karbi ragamar ci gaba da shugaban cin kuraishawa da kuma kula da Dakin ka’aba da yiwa mahajjata wato baki hidima. Sannan bayan wafatin Abdu Munaf sai dansa mai suna Hashim ya karbi ragamar Dakin ka’aba da jagorancin kuraishawa, ita wannan hukuma ta hashimawa ta game duk bangarorin kuraishawa, duk da kuma cewa shine wanda yake kula da Dakin ka’aba da hidima ga masu ziyara, sannan kuma shine mutum na farko daya fara tafiya kasuwanci zuwa kasar sham lokacin zafi, sannan kuma lokacin sanyi kasar Yaman yake tafiya(7) .
  Bayanshi ne kuma dansa Abdul muddalib wato kakan Manzon Allah (s.a.w) ya karbi jagorancin kuraishawa da kuma kula da al’amuran Dakin ka’aba da yiwa masu ziyara hidima. Abdul Muddalib yana kan  addinin Annabi Ibrahim (a.s) ne, sannan yana da yaya maza 10 mata kuma 6, Baban dansa shine mahaifin Manzon Allah (s.a.w) wato Abdullahi bn Abdul Muddalib, kuma Abdul Muddalib ya raba ayyukansa tsakanin yayansa inda suke wannan hidima harzuwa lokacin data zo kan Manzon Allah Muhammad dan Abdulllahi (s.a.w).
Zamuci gaba insha Allah a kasha na uku. Allah ya bamu dacewa, da fatan za a biyomu a kasha na uku din.

Aliyu Abdullahi Yusuf: What’sapp, Telegram, Istgram, Facebook da sauran social Media Number: +2348037493872, ko kuma ta email address: ya.aliyuabdullahi@yahoo.com.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: