bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:38:24
sarautar farisa ta girgiza har wani bangare ya yanke ya fado kasa, da wasu abubuwa da yawa da suka faru a lokacin haihuwar Manzon Allah (s.a.w).
Lambar Labari: 305
          HAIHUWAR MANZON ALLAH (S.A.W).
Kamar yadda bayani ya gabata an haifi Manzon Allah (s.a.w) a garin Makka, a mafi sharar ruwaya ranar Juma’a sha bakwai 17 ga watan Rabi’u Auwal shekara ta 570 miladiyya wato shekara 53 kafin Hijira. A lokacin haihuwar Manzon Allah (s.a.w) abubuwa da yawa sun faru, kamar yadda aka sani ashe karar jiwaye aka haifi Manzon Allah (s.a.w), sannan lokacin haihuwar sa abubuwa dama sun faru kamar: Gaba daya Guma kan dake gefen ka’aba sun fado kasa, sannan wutar farisa ta mutu wacce tayi sama da shekaru dubu akunne an bauta mata, da kuma katangar sarautar farisa ta girgiza har wani bangare ya yanke ya fado kasa, da wasu abubuwa da yawa da suka faru a lokacin haihuwar Manzon Allah (s.a.w)(1)  .
Duk wadannan abubuwa sun faru ne saboda busharar haihuwar fiyayyen halittar Ubangiji dan sako daga Allah cika makon Annabawan Allah Annabin Rahama, Rahama ga duk duniya Muhammad dan Abdullahi (s.a.w). Bayan haihuwarsa Manzon Allah (s.a.w) yana gaban kakansa Abdul Maddalib, tunda yan watanni kafin haihuwarsa mahaifinsa Abdullahi ya yi wafati, a haryarsa ta zuwa Sham rashin lafiya ta kamashi  a wani wuri kusa da garin Yasrib ya yi wafati. Bayan nan kakan Manzon Allah (s.a.w) wato Abdul Maddalib yaci gaba da kulawa dashi.
Abdul Maddalib a cikin yayansa yafi son Abdullahi mahafin Manzon Allah (s.a.w), shima rasuwar Abdullahi ta matukar girgiza shi ya shiga matukar damuwa, saboda haka bayan haihuwar Manzon Allah (s.a.w) ganin dan Abdullahi a gabansa wannan yasa shi farin ciki sosai, saboda murnar haihuwar Manzon Allah (s.a.w) Rakumi ya yanka a matsayin abin hakika yasa kuma aka shiryawa kuraishawa abinci da naman wannan Rakumin duk saboda murnar haihuwar Manzon Allah (s.a.w), sannan bayan nan yasawa jikansa suna Muhammad(2)
    LOAKACIN  SHAYAR DA MANZON ALLAH (S.A.W).
A lokacin da aka haifi Manzon Allah (s.a.w) a tsakanin manyan kuraishawa a kwai wata al’ada rubutacciya ko kuma mu ce yardarjiya cewa yayansu da aka Haifa ba za a shar dasu agida ba, za a rinka bawa matan kauye ne su shayar dasu, sannan su renesu har zuwa girman su.
Tabbas mutane suna ko Karin tora yayansu wajen kabilar banu Sa’ad. Saboda ita wannan kabila a tsakanin kabilun larabawan Makka, Mutanen wannan kabila sunfi Magana da larabci fasihi. Shisa ma matan wannan kabila ta banu Sa’ad duk shekara suke zuwa Makka saboda karbar renon yara suna Magana da mutane sukan tambaya ko akwai wanda zai bada raino.
Wani bangare daga cikin matan banu Sa’ad da suka zo Makka domin neman renon yara. Abdul Maddalib ya bawa matan su gwada bawa Manzon Allah (s.a.w) nono, amma Manzon Allah (s.a.w) ba wacce ya karbi nata ya sha. Daga karshe dai wata mata mai suna Halimatu Sa’adiyya ta zo wajen Abdul Maddalib inda da kanshi ya kama nononta yana sha. Saboda haka Abdul Maddalib ya bawa wannan matar Manzon Allah (s.a.w) domin ta tafi dashi ta shayar dashi. Haka Halimatu Sa’adiyya ta tafi da Manzon Allah (s.a.w) cikin kabilarta ta banu Sa’ad. Ta haka ne Manzon Allah (s.a.w) ya fita daga garin Makka har tsawu shekaru hudu ya rayu a gaban Halimatu Sa’adiyya(3) .
Shigar Manzon Allah (s.a.w) cikin rayuwar Halimatu alkhairai da albarka masu yawa ne suka chanza rayuwarta da ma mutanen kyauyen su gaba daya , saboda albarkacin Manzon Allah (s.a.w) Dabbobinsu sun ya waita gonakinsu sunyi kyau sosai albarka ta yadu cikin kasa wanda kafin wannan lokaci suna fama da talauci da yunwa ne a kauyensu(4) .
  YARINTA  DA  SAMARTAKAR  MANZON  ALLAH .
Manzon Allah (s.a.w) wata rana yake tambayar Halimatu ya ce: Ya Baba miyasa mutum biyu daga cikin yan uwana kunlum bana ganinsu? Halimatu ta ce: kunlum suna fita da Dabbobi ne suna zuwa wajen kiwu dasu, washe gari bayan Halimatu ta gyarawa Muhammad gashinsa tasa masa mai a gashin sannan tasa masa kwalli a idonsa sai ta dauko wata laya saboda tsari tasa masa a wuyansa. Muhammad duk da cewar yaro ne shi a lokacin yayi fito na fito da wannan kurafat din nasu, inda ya cire wannan layar sannan ya ce wa Halmatu: saurara ya mama tabbas tare da ni a kwai wanda shi yake kareni(5) .
Daga karshe dai bayan shekaru hudu Halimatu Sa’adiyya ta dawu da Manzon Allah (s.a.w) Makka, inda ya koma gaban Mahaifiyarsa, Sayyida Amina taci gaba da kula da Danta, amma a wannan ranar da aka dawu dashi tayi matukar farin ciki, saboda tsawun lokacin da ta dauka ba tare da shi ba. Bayan shekara 2 ne  da ko mawar Manzon Allah (s.a.w) gaban mahaifiyarsa, ita kuma Sayyida Amina ta yanke shawar zuwa ganin danginta da kuma kaiwa mujinta Abdullahi Ziyara a kabarinsa da ke kusa da Yasrib. A wannan tafiyar tata tare da Manzon Allah (s.a.w) ta tafi, amma a hanyarta ta dawuwa daga Yasrib rashin lafiya ta kamata wanda daga karshe sanadiyyar wannan rashin lafiya  a wani yanke wanda ake kira da ( Abwa ) tayi wafati. A wannan lokacin Muhammad yanada shekaru shida ne kawai. Ummu Aiman mai yiwa Amina hidama itace ta dawu da Manzon Allah (s.a.w) ga rin Makka cikin tsananin rashin lafiya saboda girgizar rasuwar mahaifiyarsa(6).
Bayan wafatin sayyida Amina, nauyin Abdul Maddalib ya nauyaya sosai; tunda kulawa da karamin yaro ya same shi sannan kuma ya san cewa goben wannnan yaron nashi abune mai mahimmanci matuka, sannan a gefe guda kuma maraici Manzon Allah (s.a.w) na rashin mahaifinsa Abdullahi dana mahaifiyarsa Amina yana matukar girgiza shi, saboda haka domin samun nasara madaukakiya ta goben wannan yaro dole ne ya karfafa ruhinsa.
Allahu Akbar; wafatin sayyida Amina bai cika shekaru biyu ba kawai sai rashin lafiya ta kama Abdul Maddalib shima kuma sanadiyyar wannan rashin lafiya ne yayi wafati, sai dai kafin rasuwarsa da kanshi ya damka shi a hannun Abu Dalib; miyasa yayi haka, saboda yanda Abu Dalib ke matukar kaunar Manzon Allah (s.a.w).
Daga shekara 8 ne Abu Dalib ya fara kulawa da Manzon Allah (s.a.w) harzuwa lokacin da aka aiko Annibi da sako yaci gaba da kulawa dashi, ta yanda duk abinda ya taso Abu Dalib na kula dashi, zamu iya cewa ko bayan da Manzon Allah (s.a.w) ya auri sayyida Khadija bai rabu da gidan Abu Dalib gaba daya ba har zuwa wafatin Abu Dalib din.    Zamuci gaba insha Allah.
Aliyu Abdullahi Yusuf: Media Number: +2348037493872.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: