bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:39:14
Ubangiji ne da kanshi ya reni Manzon Allah (s.a.w) kuma ya yi masa tarbiyya; saboda babu wani wanda ya fada wa Manzon Allah (s.a.w) yanda zai bautawa Ubangijinsa
Lambar Labari: 306
Muhimman abubuwan da suka faru kafin Risalar Manzon Allah (s.a.w).
Manzon Allah (s.a.w) a sartakarsa ya tashi tsakanin wuri da yake da kazanta da kuma shirka da ake yi, ga kuma dilmiyewa a cikin inhirafi kai dama canfe-canfen Jahiliyya. Wannan Manzo mai girma haka ma iyayensa da kakanninsa suka rayu cikin al’ummar da take cikin irin wannan yananin, haka suka rayu cikin tsananin wahalar mutanen Jahiliyya da basu san komai ba sai shirka da bautar Gumaka. A wannan yana yin abu ne mai matukar wahala a iya fahimtar mutum shi yasa ma mafi yawan lokuta yake nesa da mutane ta yadda yake fita wajen gari domin anadarsa(1) .
Tabbas Abu Dalib ya kasance yana Bautar Ubangiji madaaukakin sarki ne, shi yasa ma Manzon Allah (s.a.w) idan yana cikin gidan yake samun ganawa da Ubangijinsa. Duk da cewa hakan baya isar Manzon Allah (s.a.w) gamsuwa, ta yadda hakan  yasa shi samun wani lokaci da kuma wuri kebantacce yake ganawa da Ubangijinsa wannan wurin shine inda ake kira da kogun Hira(2) .
Ubangiji ne da kanshi ya reni Manzon Allah (s.a.w) kuma ya yi masa tarbiyya; saboda babu wani wanda ya fada wa Manzon Allah (s.a.w) yanda zai bautawa Ubangijinsa. Duk da cewa Manzon Allah (s.a.w) yana fita wajen Makka domin nesantar dattin mutanen Makka, amma ko da yaushe yana taimakon mutane wajen tattalin arzikinsu  da kuma shiga cikin ayyukan yau da kunlum na al’umma kai harma kiwu yana tafiya cikin sahara tareda sauran makiyaya Dabbobi; bai taba kin halartar wani taro ko wani zama da kuraishawa suka shiryaba. Irin  Wannan tsarin da kuma tunani irin na Manzon Allah (s.a.w) tun yana yaro harzuwa girmansa ya wuce a ce bisa hatsari ya faru. Kamar yadda gaba daya mutane sun san shi ne da amana da gaskiya sannan tsarkakanke mai cika alkawari. Kai harma bayan aiko Manzon Allah (s.a.w) duk da cewar basuyi imani da  abinda ya zo  musu da shi ba suna I’itirafin cewa Muhammad amintacce ne. Dalilin da zai gasgata mana hakan kuwa shi ne, mutanen Makka su sukasawa Manzon Allah (s.a.w) suna Muhammadul Amin, suna kiran Manzon Allah (s.a.w) da Muhammadul Amin ne saboda amanarsa da cika alkawarinsa, sune suka zaba masa wannan suna da kansu, duk da wahalar rayuwa da yake sha a cikinsu da munin dabi’ar da suke da ita sai da kyawawan dabi’unsa suka bayyana a garesu(3) .
Labarin gaibu ya fara zuwa Manzon Allah (s.a.w) a baccinsa ne bushara da aka yi masa; haryanzu fa ba a aiko Manzon Allah (s.a.w) ba. Ubangiji mai girma haryan zu yana bayyana shaksiyyar Manzon Allah (s.a.w) da albarkarsa dama karamarsa a cikin mutane, saboda mutane da kansu su gane banbancinsa da sauran mutane wato so ake mutane suji cewa wannan mutumin ya banbanta da sauran mutane shi mutum ne na musamman.
Duk da cewa abubuwan da suka faru lokacin samartakar Manzon Allah (s.a.w) abubuwa ne masu yawan gaske kuma masu matukar firgitarwa wanda duk mai hankali yasan wannan abubuwa da ke zuwa daga wannan mutumin ba wai akwai  abu ne haka kawai ba, amma a nan ba zamu iya kawo wasu da yawa daga cikin abubuwan da suka faru ba, zamu kawo hudu ne kawai a matsain buga misali.
                              A   HALFIL FUSUL;
A lokacin samartakar Manzon Allah (s.a.w) wani mutum daga cikin kabilar ( bani Zubaid) ya shigo garin Makka sunyi ciniki da kuma daya daga cikin manyan kuraishawa mai suna ( As bn Wa’il), wannan mutumin ya shigo ne domin sayen wasu kayayyaki, inda bayan gama ciniki As ya karbi kudi kuma ya hana mutumin kaya. Sannan shi wannan mutumin Zubaidi ba zai iya karbar hakkinsa daga wajen As ba. A gefe guda kuma akwai wasu matasa da  suke zama a wajen garin Makka kan tsaunuka aikinsu shine kwatowa wanda aka zalunta hakkinsa daga hannun azzalumin, da kuma hana yin zalunci ga baki masu shiguwa garin Makka, domin gudanar da kasuwanci, sai wannan mutumin ya tafi wajen ( Abu Kabis) wanda shine shugaban wannan kungiya ta wadannan samarin a lokacin, akan wannan tsaunin domin kai kukansa da bayani akan damuwarsa. Saboda haka wadannan samari suka tafi gidan As bn Wa’il suka karbi hakkin wannan mutumin suka bashi, Manzon Allah (s.a.w) a wannan lokacinn yana saurayi ne dan shekara ashirin, kuma shine mutum  mafi muhimancin a cikin wannan kungiyar samarin(4).
  Wannan kungiya da Halfi Fusul tayi suna, kuma babban aikinta shine tai makon raunana da marasa karfi, sannan a tsakanin kuraishawa suna alfahari da ita. Saboda duk da irin zalunci da rashin aklak dake tsakanin larabawa wannan kungiyar ta banbanta da wacan zalunci da kuma miyagun ayyuka, bama barin wadancan munanan ayyukan kadai tayi ba a a tama yi fito na fito ne da irin wadannan ayyukan.
Wannan ita ka dai ce kungiya wacce kafin musulunci a cikin larabawa ta banbanta kuma take da mutuntaka, kuma ita ka dai ce kungiyar da Manzon Allah (s.a.w) ya shigeta domin taimakon raunana, sannan tsawun lokacin da Manzon Allah (s.a.w) yake cikin wannan kungiyar yan wannan gunjiyar suna alfaharin kasancewar Manzon Allah (s.a.w) tareda su a cikin kungiyar(5) .
B   AUREN MANZON ALLAH (S.A.W) DA SAYYIDA KHADIJA (A.S).
Abu Dalib ya yi shawara da Manzon Allah (s.a.w) akan mai zai hana ya yi aiki tareda Khadija yar Kuwailid mace mai arziki a cikin kuraishawa, ya rinka karbar kaya daga wajenta ya yi tijara ribar da aka samu sai surinka rabawa. Tabbas lokacin da Manzon Allah (s.a.w) sunansa na mai amana ya yadu da jarumtakarsa a cikin garin Makka Khadija ta nemi Manzon Allah (s.a.w) da ya rinka kula mata da dukiyarta. Manzon Allah (s.a.w) ya karbi wannan tayin nata kuma ya rinka bin yan kasuwa da dukiyar Khadija zuwa Sham, kuma a wannan tafiyar wasu yan watanni akayi inda aka samu riba mai yawan gaske.
Khadija mace ce mai imani  tsarkakakka kuma mai tarin dukiya sannan tana da labarin zuwan Manzon Allah (s.a.w) nan gaba, saboda haka tunda taga jarumtakar Manzon Allah (s.a.w) da kuma irin aklak dinsa sai ta nemi tayi aure da shi,  Manzon Allah (s.a.w) ya amsa mata wannan bukata tata. A karshe akayi aure tsakanin Manzon Allah (s.a.w) da kuma Sayyida Khadija (a.s)(6) .
 Khadija ita ce mace ta farko da tayi imani da Manzon Allah (s.a.w) sannan kuma ta daurewa duk wasu wahalhalu  da damuwa kala-kala da suka rinka bijirowa a wannan lokacin. Khadija tanada babban matsayi a wajen Manzon Allah (s.a.w) shi yasa harzuwa lokacin da khadija tayi wafati Manzon Allah (s.a.w) bai kara aure ba, bai auri wata mata ba, ita kadai ce, saboda bata da abokiyar hadi. Bayan wafatin ta Manzon Allah (s.a.w) ya zauna kusa da gawarta ya yi kuka sosai.
Zamuci gaba insha Allah, sai abiyo mu sannu a hankali, Allah ya bamu da cewa.
 

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: