bayyinaat

Published time: 18 ,November ,2018      15:42:43
A gefe guda kuma Hajarul Aswad yana kasa a waje guda kuma. A wannan lokacin kuma bangarorin kuraishawa suna kai kawo
Lambar Labari: 307

RAWAR DA MANZON ALLAH (S.A.W) YA TAKA WAJEN KWANTAR DA RIGIMA AKAN HAJARIL ASWAD.

kafin aiko Manzon Allah (s.a.w) da Risala babu wani dogon gini da yake ya kewaye dakin ka’aba, bangwayen dakin kuma kwata kwata basu wace tsayin mutum a tsaye ba. Lokacin Manzon Allah (s.a.w) yana da shekaru 35 ne, gashi kuma duk jefanta kasar tsaunukan da ke kusa dakin ka’aba duk ta gangaro kusa da Dakin ka’aba sosai. A baya saboda gajartar da katangar dakin ka’aba take dashi hakan yasa cikin sauki ana shiga a sace kayan dakin ka’aba din . wannan dalilin yasa masu kula da Dakin ka’aba kwana kusa da ita, saboda ihsasin da suke dashi na aikin su.

A gefe guda kuma Hajarul Aswad yana kasa a waje guda kuma. A wannan lokacin kuma bangarorin kuraishawa suna kai kawo akan wace kungiya ce ya kamata ta dora Hajaril Aswad a wajensa na asali, Saboda abin alfahari ne ga duk wata kabila da tayi wannan aikin, shi yasa ma cikin hanzari ko wace kungiya tayi saurin zuwa wajen domin samun wannan alfaharin, hakan kuma ya haifar da rashin fahinta ta yadda ko wane bangare yaki yadda ya barma wani bangaren ya samu wannan alfaharin na dora Hajarul aswad a wurinsa na asali.

A karshe dai wani bangare da bangarorin kuraishawa ya zo domin kawo maslaha akan al’amarin, domin gudun zubar da jinni, sunyi yarjejeniya akan cewa duk wanda ya fara fitowa daga Masallacin Haram to shine zai yi masu hukunci tsakaninsu, saboda haka gaba daya sai idanuwansu suka koma kallon Masallacin Haram suna jiran ganin wanda zai fito daga nan bada dadewa ba sai ga Manzon Allah (s.a.w) ya fito daga Masallacin inda a dai dai wannan lokacin kowa ya fara fadin ai wannan Muhammadul Amin ne! kowa na cewa mun yadda da hukuncin sa.

Bayan da Manzon Allah (s.a.w) ya duba abinda suke rigima a kanshi da kuma yanda kowa yake son ganin shine yafi dayan bangaren dacewa da samu wannan alfaharin sai Manzon Allah (s.a.w) ya shimfida wani kyalle sannan ya dora Hajaril Aswad din akai, sannan ya zabi mutam dai-dai daga ko wane bangare yasa su kama kyallen su daga shi sama, inda bayan haka Manzon Allah (s.a.w) ya dora Hajaril Aswad din a wurinsa da hannunsa mai albarka. Ta hakane ko wane bangare ya tafi yana alfaharin shi ya dora Hajaril Aswad a wajensa, inda Manzon Allah (s.a.w) ya yi nasarar kawar da yaki mai girma(1)[1].

D HAIHUWAR IMAM ALI (A.S).

A shekara ta 30 da Amul fili, wato bayan shekaru 30 da haihuwar Manzon Allah (s.a.w) ne aka haifi Aliyu bn Abi Dalib (a.s) a garin Makka a cikin dakin ka’aba. A wadannan shekaru saboda matsaloli da Abu Dalib yake fama dasu Manzon Allah (s.a.w) ya dauki Aliyu zuwa gidansa, ya kuma bashi duk wata kulawa da tarbiya ta musamman, da taimakon sayyida Khadija Manzon Allah (s.a.w) yaci gaba da kulawa da Aliyu bn Abi Dalib (a.s). Akan haka Imam Aliyu (a.s) yana cewa: Manzon Allah (a.s) ya dauke ni kusa da shi lokacin da nake yaro, yakan sani akan kirjinsa kuma yana zuwa dani wajen hutawarsa ke bantacce, ya kan hada jikina da nashi, kamshinsa mai tsarki nake shaka koda yaushe. Yakan tauna abinci abakinsa sannan ya saman a bakina. Ko kadan karya bazata fito daga bakina ba kuma ba zanyi kuskure ba ko kadan …

Koda yaushe ina tare dashi shi kuma yana koyar dani kyawawan dabi’unsa a fili, ni kuma ina yin biyayya gareshi ina dora kafa duk inda ya cire tashi…ina ganin hasken wahyi kuma ina jin kanshin Annabta(2)[2].

FARKON WAHAYI

A baya munyi bayanin cewa kafin aiko Manzon Allah (s.a.w) da Risala Ubangiji ne da kanshi ya yi masa tarbiyya, sannan kuma Mala’iku ne ke kula dashi duk inda yasa kafa, sannan munyi bayani akan yanda larabawa da kansu suke kallonsa mai amana kuma mai tsarki tsakanin larabawa wanda hakan yasa suke kiransa da Muhammadul Amin, sannan mu kawo yanda Manzon Allah (s.a.w) yakan fita wajen gari domin ganawa da Ubangijinsa saboda katsantar dake tsakanin larabawa ya kanje kogun hira don bautar Allah da kuma addu’o’i, wannan shi ne abinda yake yi duk lokacin da yaje kogun hira.

Farkon saukar mala’ika wajensa duk dai a wannan kogun ne na hira. Inda aka saukar masa da ayar farko a kur’ani mai girma, wannan al’amari ya faro ne 27 ga watan Rajab, Manzon Allah (s.a.w) kuma a wannan lokacin yanada shekaru 40 ne(3)[3].

Manzon Allah (s.a.w) ya shagaltu da bautar Allah madaukakin sarki da kuma addu’o’i mala’ika Jibrilu Amintaccen Allah ya sauka gareshi, sannan ya sanar da shi sakon da aka bashi ya kawu daga wajen Allah mai girma da daukaka, sannan ya karantawa Manzon Allah wannan aya. (wato suratu Alak) aya ta farko har zuwa aya ta 5.

Akan haka Imam Ali (a.s) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya kasance a cikin kogon hira tsawun wasu watanni kuma babu wanda ya yadda yaje wajensa saini kadai nake ganawa da shi a wannan lokacin, bayan ni ba wanda ya yadda yaga da shi. Ni ina ganin hasken wahayi dana risala sannan kuma ina jin kamshin Annabta. Lokacin da aka fara saukarwa Manzon Allah (s.a.w) wahayi naji karar shaidan; sai na tambayi Manzon Allah (s.a.w); wannan karar ta miye? Sai ya ce: wannan shaidan ne yake kara saboda mutane zasu bar bautar shi. Kana jin abinda nake ji kana ganin abinda nake gani banbanci na da kai kawai shine kai ba Annabi bane, sai dai kai waziri na ne sannan kana kan hanyar alkhairi(4)[4].

Imam Sadik (a.s) yana cewa: lokacin da Allah Ta’ala ya aiko bawansa a matsayin dan aike sai ya tausasa masa inda yake cewa: Abinda ya zo maka da waurin Allah madaukakin sarki kamar abinda kake gani da idanuwanka ne.

Bayan saukar masa da wahayi ne da kuma ijaza da aka bashi ta yin bayanin kur’ani, Manzon Allah (s.a.w) cikin cikakkiyar natsuwa day a samu na abinda ya zo masa daga wajen Ubangiji mai girma da kuma kwanciyar hankali ya koma gida. Sayyida khadija tayi matukar farin ciki da jin wannan labari wannan labari yanada matukar muhimmanci sosai sai ta cewa Manzon Allah (s.a.w): tsawun shekaru nasan kai Annabi ne bayan haka sai tayi Imani dashi(5)[5].

Zamuci gaba insha Allahu Ta’ala, Allah yasa mud ace.



[1] Tarikul Yakubi, J na 2, shafi na 19-20. Da kuma Biharul Anwar, J na 15, shafi na 337.

[2] Asahihi min sirati Nabiyyil A’azam, J na 33, shafi na 351-356. Da kuma Nahjul Balaga, kuduba ta, 119.

[3] Suratul Alak aya ta 1-5. Da kuma Manakib Ali abi Dalib, J na 1, shafi na 150. Dama Tarik Siyasi Ismai, J na

1, shafi na 233-234.

[4] Biharul Anwar, J na 18, shafi na 262. Kamar yadda ya zo a Sahihul Bukari da Muslim.

[5] Assahihi min siratil Nabiyil A’azam, J na 2, shafi na 41.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: