bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:23:03
A addinin Musulunci bisa koyarwar Ahlul-baiti Allah ba jiki ba ne, kuma ba shi da siffofin masu jiki, “babu wani abu da yake kama da shi” ingantattar koyarwar
Lambar Labari: 309
WASU MAS’ALOLI A BUHARI DA MUSLIM
Yanzu lokaci ya yi da ya kamata mu leka cikin Buhari da Muslim don mu ga wasu mas’aloli a mahangar koyarwar musuluci sahihiya musamman abin da ya zo daga gidan Ahlul-baiti zuriyar annabi (s.a.w). Wannan mas’aloli sun hada da na akida da na furu’a kamar haka:
TAUHIDI A BUHARI DA MUSULIM
A addinin Musulunci bisa koyarwar Ahlul-baiti Allah ba jiki ba ne, kuma ba shi da siffofin masu jiki, "babu wani abu da yake kama da shi” ingantattar koyarwar Musulunci ta nesanta Allah madaukaki da dukkan kama da wani abu daga bayinsa, don haka ba shi da jiki ko sura ko shakali ko kala ko halaye na bayinsa. Kura’ni ya karfafi wannan koyarwar ne kuma ya yi umarni da riko da ita saBanin litattafan da suka gabata da suka samu munanan fassara kan siffofin Allah. Idan mun duba zamu ga akidar sanya jiki ga Allah a littafin "Attaura” (Attaura: Kitabut Takwin, fasali 32, jumla 26-30). a matsayin wata halitta mai jiki da yake saukowa duniya ya shiga hemar Yakub (a.s) don ya yi fada da shi, irin wannan akida ce Musulunci ya kore da harshe mai kaifi.
Amma sai ga shi muna samun akidar bayar da wuri da zamani ga Allah a Buhari da Muslim, har ya kasance Ubangiji yana rayuwa kan al’arshi ne kuma yana saukowa a wani yanki na dare zuwa wannan duniyar. Ga akidar yiwuwar ganin Allah da idanuwa, yana da siffofi irin na mutum kamar idanuwa, kunne, kafa, hannu, kuma wadannan siffofi nasa ba sa karBar wani tawili balle a yi musu wata fassarar a bisa mahangarsu.
Hadisin da yake nuni zuwa ganin Allah da idanuwa yana da yawa da sanadodi daban-daban, wannan hadisin ya zo a babobi masu yawan gaske da Buhari, duba kasa ka ga bayanansu masu yawan gaske, (Buhari: j 1, h 529, h 547. J 6, h 4570, j 9, h 6997, 6999. Muslim: j 2, h 633. Da wasu babobi masu yawa).
1-Wannan hadisin ya kunshi abubuwa masu yawa da suka hada da Allah yana jirkita da wata siffa ba ta sa ba har muminai su yi musun sa shi kuwa sai ya fito musu da siffarsa ta gaskiya, wannan lamarin a bias gaskiya wasa ne da Allah ya barranta daga gare shi.
2-Ana ganin Allah da shakalinsa har ma ya yi hira da bawansa da zai ta jayayya da shi har da wayo ya shiga aljanna.
3-Ganinsa ga kowa zai zama mai sauki kamar yadda ake ganin wata a duniya, kuma dukkan al’umma da ‘yan wuta da aljanna duka zasu gan shi. Ba mu sani ba don me ya sa sai a can ne za a gan shi alhalin ko’ina ba shi da bambanci gare shi inda ana ganinsa!.
4-Yana sanya mayafin Takama da zanin Jiji-da-kai, kuma sai ya yaye zaninsa har sai an ga kaurinsa. Wannan yana nuna yana sanya tufafi ke nan kuma yana da kwauri da kafa da sauran gaBoBi.
5-Sannan wannan ruwayar tana nuna cewa Ubangiji yana cirata daga wuri zuwa wuri, yana da zamani, motsi, tsayi, kwauri, canji, da sauran abubuwan da suke siffofi ne na bayinsa.
Ruwayoyin yiwuwar ganin Allah da idanuwa su ne asasin da malaman ‘yan Sunna suka dogra da su wurin imani da hakan da sanya shi cikin wata mas’ala ta lalurar addini. Kusan dukkan malaman mazhabobin Sunna na furu’a suna karfafa wannan akida ta yadda ya kai ga shafi’i yana ganin idan da ba shi da yakini a wannan duniyar kan cewa zai ga Allah a ranar lahira to ba zai bauta masa ba, (Tabaqatus shafi’iyya: j 2, sh 17). Kamar yadda zamu ga a lokacin da Ash’habu ya tambayi Maliku game da kalmar "naazira” da Ahlul-baiti suka tafi a kan cewa tana nufin sauraro, sai Maliku ya ba shi amsa da cewa tana nufin gani ne, domin ya tabbatar da cewar kowane mutum zai ga Allah a ranar kiyama.
Mas’alar ta samu saBani mai yawa a cikin rassanta ta yadda wasu suna ganin cewa ganin Ubangiji ya takaita ne da lahira, wasu kuma suna ganin annabi ya gan shi a duniya a Mi’iraji, wasu kuma sun kawo cewa malamai ma suna iya ganin sa, wasu sun tafi a kan cewa ana ganin sa amma a mafarki har ma suna kawo wadanda suka gan shi a mafarki, wasu sun kawo ruwayoyin ayyukan da mutum zai yi idan yana son ya gan shi a mafarki, da sauran lamura masu ban al’ajabi. Mafi mamaki a nan yadda da yawa suka nuna mata da yara su ba zasu gan shi ba, idan ma zasu gan shi to a lahira ne kawai, wasu kuma suna ganin zasu gan shi duk shekara ne kawai kamar ranakun idi na lahira.
Wasu kuwa sun shiga cikin bahasin cewa shin ganin sa ya takaita da al’ummar annabi ne ko kuwa har da sauran al’ummu, wasu kuma sun shiga mas’alar cewa ‘yan jahannama zasu iya ganin sa ko kuwa sau daya kawai zasu gan shi a ranar lahira. Wasu kuma sun tafi a kan cewa har da muminai ba zasu gan shi ba sai ranar lahira kawai, amma bayan nan to sai dai annabawa kawai su gan shi. Mas’alar ta kasu gida-gida da kowa ya ga dama sai ya kawo ra’ayinsa da tunaninsa a matsayin addinin Allah. Wannan kuwa shi ne sakamakon da yake samun mas’alar da tun farko ba ta da asasi daga Allah ko manzonsa.
Wannan akida ta ganin Allah ta samo asali daga kuskuren tafsirin kalmar "naazira” ne, sai dai kuma kamar yadda muka sha nanatawa duk sa’adda aka samu wani ra’ayi to cikin sauki akan samu wasu su yi masa ruwaya don karfafarsa wanda yake son ya ga wannan lamari ya bincika mas’alolin Musulunci masu yawan gaske don ya gano asalin saBaninsu sannan kuma sai ya koma ya ga ruwayoyin da aka kirkira don kare wadannan ra’yoyin. To wannan mas’alar ta ganin Allah da idanuwa ita ma ta samu wannan yanayin ta yadda aka kirkiro mata hadisai don kare ta.
Mafi munin abu shi ne dokar da suka lizimta wa kansu ta cewa idan Hadisi ya saBa wa ayar Kur’ani to ana jefar da ayar Kur’ani ne a dauki Hadisi. Da wannan dokar ne aka bar mafi yawan ayoyin Kur’ani aka yi watsi da su a jujin tarihi. Idan mun duba zamu ga yadda Kur’ani ya soke duk wani gani na Ubangiji yayin da Allah madaukaki yake gaya wa annabi Musa (a.s) cewa: "Ba zaka taBa ganina ba” kuma ya sanya ganinsa ya ta’allaka da mustahilin abu don dai ya tabbatar da ganin sa cewa mustahili ne. Wato idan lamari na ya bayyana ga dutse na umarnin ya fashe sai kuma dutsen ya ki bin umarnina sai ya ki fashewa to zaka gan ni, sai kuwa Allah ya yi umarni ga dutse kuma ya bi umarnin ya tarwatse don ya tabbatar wa annabi Musa (a.s) cewa ba zai yiwu ya gan shi ba. Wani abu muhimmi a nan shi ne mu lura cewa annabi Musa (a.s) bai nemi ganin Allah da kansa ba, sai dai takurawar Banu Isra’ila da barazanar cewa idan an koma zasu gaya wa mutane babu wani Allah don ba su gan shi ba, wannan ne ya sanya annabin Allah Musa (a.s) ya yi wannan neman don ya nuna musu cewa ganin Allah mustahili ne, amma in ba haka ba Musa (a.s) ya fi karfin ya jahilci hakan. Don haka ne Allah ya sanya tsawa ta gama da su, sai Musa (a.s) ya roki Allah ya dawo musu da ransu, domin idan ya koma wa Banu Isra’ila ya ba su labarin abin da ya faru ba zasu yarda ba, zasu tuhume shi da cewar sai da ya zaBi manyansu baki daya sai ya je ya kashe su don ka da a samu wasu masu fada a ji sai shi kadai kawai, don haka sai Allah ya tausaya masa ya dawo da su, kuma zaBaBBun Banu Isra’ila suka ga ayar da take nuna akwai Allah mai karfi mai iko don haka ba zasu iya musun sa ko da kuwa ba sa iya ganin sa.
Sannan ayar nan ta surar An’am: 103, kai tsaye ta yi magana da cewar "Marsikai ba sa riskar sa” wacce take nuni da duk wasu marsikai na zahiri kamar ji, gani, shaka, taBawa, dandano, ba zasu iya riskarsa ba, haka ma marsikai na badini ba zasu iya riskar sa ba, don haka babu yadda kwakwalwa da zuciya zasu iya sawwala shi. A yanzu akwai wata aya da ta fi wannan lamarin fitowa a fili ta kore ganin Ubangiji (s.w.t).
Sannan ruwayoyin da suka zo daga Ahlul-baiti (a.s) baki daya suna kore yiwuwar ganin Allah madaukaki. Kuma mun san cewa su ne wadanda manzon rahama (s.a.w) da ittifakin ruwayoyin ‘yan Sunna da ‘yan Shi’a duka sun kawo cewa idan al’umma ta yi saBani to su ne zata koma musu. Hasali ma dukkan al’ummar musulmi sun ruwaito cewa manzon Allah (s.a.w) ya bar mana littafin Allah da alayensa a matsayin wasiyyarsa, don haka ke nan babu wani mai hakkin ketare wannan koyarawar tasu.
Idan da wani zai ce an samu karo da juna ke nan tsakanin ruwayoyin wasu malaman ruwaya daga malaman ‘yan Sunna da kuma ruwayoyin da suka zo daga Ahlul-baiti ta yadda ya yi shisshigi ya ketare fadinsu, to sai mu ce sai a koma wa Kur’ani mai daraja da yake nuni da cewa ba za a ga Allah ba. Idan muka koma Kur’ani zamu ga karara ya furta da cewa ba za a iya ganin Allah ba, amma masu cewa za a gan shi suna masu dogaro da ayar Kur’ani zamu ga duk suna riko da tawili ne, idan kuwa akwai bayyanannen dalili to babu wani mai hujjar da zai yi tawilin kalmar da ake saBani kan ma’anarta wanda ya dogara da akidar masu saBani ne don tabbatar da ganin Allah madaukaki. Don haka natija ke nan tana nuni da cewa ba za a iya ganin Allah ba bisa dokar ilimi.
Idan mun duba zamu ga kalmar "naazira” tana nufin mai sauraro, kuma akwai irin ta da yawa a Kur’ani da fadin Allah yake nuni da ita kamar a fadin Bulkis "… ni mai sauraro ce in ga me ‘yan sako zasu dawo da shi…” sai ta yi amfani da kalmar "naazira”. Haka nan zamu ga kalmomin da aka ciro su daga wannan kalmar su ma suna nuni da haka kamar fadinsa "… hal yanzuruna ill ta’awilah…” da fadinsa "… ma yazuruna ill saihatan wahidatan…” da sauran kalmomi masu yawa da zamu ga suna da ma’anar sauraro ne, sai ya zama ke nan wadannan fuskokin suna jiran ni’imar Allah ne, kamar yadda na kafirai suke jiran azaba ne a bisa dokar "mukabala” da masana ilimin Fasaha da Balagar larabci sun san wannan.
Idan mun duba ayoyin guda hudu zamu ga na azaba suna cewa ne "Wasu fuskoki kuwa a wannan ranar sun turBune. Suna da yakini azaba mai karya tsatso za a yi musu”. A mukabalar wadannan ayoyin zamu ga Allah ya rigaya ya kawo fadinsa madaukaki cewa: "Wasu fusaku a wannan ranar suna masu sheki. Suna masu sauraron ubanigjinsu”. Don haka idan da fuskokin muminai zasu ga Ubangiji ne to da sai fuskokin kafirai ya zama su ba zasu ga Ubangiji ba ke nan. Don haka tun da azaba fuskokin kafirai suke sauraro, to fuskokin muminai ma suna sauraron ni’imar Allah ne ba ganin sa ba.
Hada da cewa idan masu wannan ra’ayin suka ce muminai ake nufi zasu ga Allah a wannan ayar, ai kuma sun manta sun ce kafirai ma zasu ga Allah a wannan ranar, ke nan wannan bai keBanta da muminai ba. A nan sai mu tambaye su yaya zaku warware wannan maganar mai karo da juna da kuke yi. Don haka ko dai ku koma wa hakikanin zahirin Kur’ani da ya bayyana a fili na rashin yiwuwar ganin Allah da yin imani da koyawar manzon Allah ta hannun alayensa (a.s), ko kuma ku zama kuna magana mai warwarar juna da ba ku da amsar da zaku iya bayarwa.
Sannan me ye kuma na karfafar wannan mas’alar da mafarkin malamai, idan kuka ce manzon rahama (s.a.w) ya na farki da Allah (s.w.t) yana ganawa da shi a cikin mafarki to wannan yana bukatar dalili ingantacce da idan ya inganta to wani abu ne da za a sallama da shi. Amma da bai inganta ba me ye kuma zai karfafi mas’alar da wasu malamai zasu ce suna ganin Allah a mafarki, yaushe mafarkin da yake saBa wa asasin Kur’ani zai zama gaskiya, don haka mafarkin malamai na cewar sun gan Allah ba zai iya taimaka wa wannan mas’alar ba. Kamar yadda mafarkin Ahmad dan Hambal da Allah ba zai iya samar da wani dalili kan cewa za a iya ganin sa ba, kuma babu wani sako da zai ba wa Ahmad dan Hambal da zai zama hujja kan al’umma sai dai idan masu dogaro da sakon sun ba shi annabta sai su yi mana bayani, (Manaqibu ahmad: sh 434).
Sannan raba wa kowa wuridi da zai yi duk sa’adda yake son ganin Allah (s.w.t) shi ma wasa ne da shari’a kawai, (Sunan Darumi: j 2, sh 126). Ubangijin da za a bayar da wuridi don ganin sa wannan wane irin Ubangiji ne? Sannan wadanda suka gan shi zuwa yau ko da wuridi ko ba wuridi wacce siffa ce da shi. Idan suka ce sun gan shi suka ba shi wata siffa guda daya ga take nuni ga iyakarsa, kalarsa, yanayinsa, girmansa, tsayinsa, fadinsa, da duk wata siffa da zasu ba shi, to kai tsaye mun san wadannan masu kage ne masu neman dulmiyar da al’umma da kautar da su daga shiriyar manzon Allah (s.a.w). Idan kuwa ba su ga komai ba sun rusa kansu, domin gani yana lizimta abin gani, idan kuwa babu abin gani to babu gani ke nan, sai ya zama wasa da harshe ne kawai da haifar da rudani cikin al’umma.
Don haka dalilin Kur’ani da ruwayoyin Ahlul-baiti da hankali duk suna goyon bayan cewa mustahili ne a ga Ubangiji madaukaki da mariskai sai dai gani da ma’anar yakinin rai mai haske da yake risker samuwarsa wannan ba ya koruwa gare shi madaukaki. Don haka ne zamu ga lokacin da wani malamin yahudawa ya zo wurin Imam Ali (a.s) yana tambayarsa cewa: "Shin ka ga ubangijinka da ka bauta masa? Sai ya ce: Kaiconka! Ai ba na bauta wa ubangijin da ba na gani. Sai ya ce: Yaya ka gan shi? Sai ya ce: Kaiconka! Idanu (mariskan gani) ba sa riskarsa da ganin kallo, sai dai zukata ne suke ganin sa da hasken imani” (Kafi: j 3, babu ibtalur ru’uya).
Don haka natijar wannan bahasin tana tabbatar mana bisa yakini cewa ganin Ubangiji kamar yadda ake ganin sauran abubuwan halitta masu jiki mustahili ne ba zai yiwu ba. Idan kuwa ya yuwu to ba Ubangiji ne aka gani ba, domin duk abin da aka gani sai yana daurantar mai gani, da iska a tsakaninsu, da haske da zai sanya hoton abin da ake gani, da fasila, da kasancewarsa jiki mai iyaka, da sauran sharudan gani tsakanin abin gani da mai gani.
Idan kuwa aka ba shi iyaka to a nan an ba shi dukkan siffofin halitta na Bangarori da gaBoBi, da dukkan wata siffa ta abin gani, sai ya tashi ba Ubangiji ba ke nan. Don haka ta kowane hali ba yadda za a yi a ga Allah madaukaki. Allah madaukaki ka girmama karfin mai ido ya gan ka ko ya sawwala ka a tunaninsa. Tsarki ya tabbata ga Allah.
 
Hafiz Muhammad Sa’id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram) (hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: