bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:27:12
Akidar da aka samu daga alayen manzon Allah (s.a.w) ta yi matukar kore wa Allah samuwar wuri domin yana lizimta masa siffantuwa da siffofin bayinsa masu iyaka.
Lambar Labari: 311
BA WA ALLAH WURI
Duk abin da yake jiki ne yana bukatar wuri da zai ci, halittun da suke da jiki sakamakon suna da iya don haka suna bukatar wurin da zasu kasance a cikinsa. Don haka ne suke iya zama suna da jihar da suke da ita idan an danganta su da wurin ko dai su kasance a samansa ko a cikinsa ko kasansa ko gefensa da sauran jihohi. Siffantuwar abu da cin wuri yana nuni kai tsaye da cewar wannan abin yana da iya da ta iyakance shi, don haka zai karBi nuni da mariskai domin dan yatsa zai iya nuna shi, idanuwa zasu fuskance shi.
Akidar da aka samu daga alayen manzon Allah (s.a.w) ta yi matukar kore wa Allah samuwar wuri domin yana lizimta masa siffantuwa da siffofin bayinsa masu iyaka. Iyaka kuwa tana sanya shi mai bukatar wanda zai kammala shi domin duk mai iyaka yana da tawayar da yake bukatar wani abu daban ya kammala shi. Wannan kuwa yana sanya shi mai tawaya, tawaya kuwa tana kore ubangijintakarsa, sai ya tashi ke nan ba Ubangiji ba alhalin shi ne Ubangiji madaukaki.
Buhari da Muslim sun ba wa Allah iyaka ta hanyar samar masa da wuri, sun sanya shi wani abu ne da ake dauke da shi, ake kewaye da shi, domin idan ya kasance a kan gadon mulki da iko ne kamar yadda suke kawowa to wannan yana nufin yana da iyaka da abin da ya iyakance shi. Kuma yana nuni da cewa shi abin da dauka ne don haka akwai abin da ya dauke shi.
Allah a gaban mai Salla!
Wannan akida mai ba wa Allah wuri ce ta kai Buhari da Muslim imani da cewar Ubangiji yana tsayawa gaban mai salla don haka ke nan da bukatar a sanya wani abu da zai kare mutum daga gittawa ta gaban mai salla, kuma aka samu ruwayoyi a kan hakan da suke neman mai salla ya yi fada da mai gittawa ta gabansa a matsayin cewa shi shaidan ne.
A ruwayar Abdullahi dan Umar zamu ga wasu abubuwa da ba zasu karBu ba ga matsayin manzon daraja (s.a.w) yayin da ruwayar take nuni da cewa manzon Allah (s.a.w) ya ga wani tofin yawo a gaban wurin da ake salla sai ya fusata ya ce: Idan mutum yana salla to ka da ya yi tofi ta gabansa domin Allah yana tsayawa gabansa yayin da yake yin salla. Kuma ruwayar ta nuna cewa manzon Allah (s.a.w) da aka fi sani ya fi kowa tsafta sai ya sanya wannan tofin cikin rigarsa ya share da ita, (Buhari: j1, ba 33, h 397, 398. Muslim: j 2, h 547. Ibn Majah: kitabus salah, b 61).
Bari in yi nuni da wani muhimmin lamari kan hakan: A lokacin da Abuhanifa ya halarci wurin Imam Sadik (a.s) sai ga Imam Musa Kazim yana salla mutune suna wucewa ta gabansa, sai Abuhanifa ya dauka cewa ya samu hanyar da zai samu tawaya a gidan alayen manzon Allah (s.a.w) don haka sai ya ce yaya haka! Sai Imam Sadik ya yi masa nuni da cewa ya tambayi yaron. Sai ya jira sai da yaron wato Imam Musa Kazim ya gama salla, sai ya tambaye shi cewa: Kai yaro yaya ka bari mutane suna wucewa ta gabanka da ubangijinka. Sai Imam Musa Alkazim (a.s) ya gaya masa shi babu wani abu da ya ke wucewa tsakaninsa da ubangijinsa domin ubangijinsa ba jiki ba ne kuma ba shi da wuri.
Wannan muhimmin lamari yana nuna mana cewa ke nan ruwayoyin da suka zo kan sutura gaban mai salla ba su da wani asasi na inganci domin duk sun dogara kan cewar Allah yana da wuri ne wacce akida ce Batacciya, don haka ke nan duk wata ruwaya da ta ginu sakamakon Batacciyar akida da ta ci karo da Kur’ani ko Sunna da aka yi ittifaki kanta, ko wani dalili na hankali yankakke to ya zama dole a yi wurgi da ita kwandon shara, domin wannan yana nuna ke nan ba daga annabi take ba, kuma barin ta cikin addini zai zama ke nan sanya wani abu cikin addini alhalin ba ya cikinsa!.
Allah a Sama!
Kamar yadda ya gabata cewar duk wani abu da ake dauke da shi to ba Ubangiji ba ne, domin yana nuna bukatarsa ga wannan abin da yake dauke da shi, hada da cewa hankali yana hukunci da cewar wanda ake dauke da shi bai kai karfin mai dauke da shi wanda yake rike da shi ba, don haka idan Allah ya kasance a sama ke nan wannan yana nuni da karfin sama da yalwarta fiye da ubangijin talikai, wannan kuwa lamari ne da yake rushe akidar Tauhidi kai tsaye.
Amma duk da haka zamu ga ruwayoyi masu yawa da suke nuni da cewa Allah yana sama, masu ingantattun litattafai uku da wasunsu sun ruwaito hadisin da yake nuni da cewa manzon Allah (s.a.w) ya tambayi wata mata baiwa cewa: Ina Allah yake? Sai ta ce: Yana sama!. Sai ya ce: Ni waye? Sai ta ce: Kai ma’aikin Allah ne!. Sai ya ce da mai ita: Ka ‘yanta ta domin ita mumina ce! (Muslimi: j 2, h 537. Abu Dawud; j 1, kitabus salah, babu tashmitul atishi. Nisa’i: j 2, kitabul Iman).
Allah a Al’arshi!
Akwai hadisai masu yawa da suka zo suna nuni da cewar Allah yana kan al’arshi kuma a can yake rayuwa, kuma al’arshin nasa ya kasance kan ruwa yake. Kusan kalmar al’arshi tana daga cikin kalmomin da masu ruwaya suka munana amfani da ita, domin kalma ce da take nufin "karagar mulki” da hausa. Idan aka ce sarki ya hau karagar mulki a shekara ta 2000 ana nufin sarki ya amshi tafiyar da mulki da juya lamurran kasa a shekara ta 2000. Karagar mulki a nan ba ta nufin wani gado ne da za a ga sarki ya dare kansa wanda gani na mariskan zahiri yake riskarsa. Sai dai lamari ne na luga da yare da aka munana amfani da shi, kuma masu kirkiro ruwayoyi suka samu dama kan hakan musamman masu ruwaya daga Yahudawa da Kiristoci da ma’abota kissoshi da suka yi tasiri a koyarwar ma’abota litattafai shida.
A fili yake cewa sau tari zamu ga wasu wurare masu yawa da aka samu irin wannan lamarin mai rudarwa ga wadanda ba su san addini ba, don karkatar da al’umma daga tafarkin sanin shari’a ta gaskiya da akida mai inganci. Kalmomi ne da hadisan manzon Allah (s.a.w) suka yi bayaninsu ta hannun wasiyyansa na gaskiya da suka yi nuni da su bisa yadda suka sauka amma sai aka samu wasu masu kauce wa tafarkinsu suka karBi ma’anarsu daga wadanda ba su san sakon manzon Allah ba. Idan muka duba sosai zamu ga kalmar "al’arshi” da ubangijin talikai ya yi nuni da ita kan cewa al’arshensa yana kan ruwa, zamu ga yana nuni kuma a wani wurin da cewa: "Kuma muka sanya komai yana rayuwa daga ruwa”!. Ashe ke nan al’arshi a nan yana nufin tafiyar da rayuwar komai a wannan duniyar daga ruwa yake. Kuma shi kansa ruwan ba ruwa ne da muke sha yayin kishirwa ba sai dai ruwa ne da yake nuni zuwa ga asasin da komai ya tsayu da rayuwarsa a kansa.
Amma sai ga wasu ruwayoyi masu nuna cewa Allah yana kan wannan al’arshin shi kuwa wannan al’arshin yana kan bayan wasu shanu masu tsananin girma. Wasu ruwayoyin kuwa suna nuni da cewa yana kan al’arshi, shi kuwa al’arshi yana kan wani kogi. Wasu kuwa suna nuni da cewa al’arshi yana kan sammai bakwai, kuma Allah ya yi masa nauyi kamar yadda mahayin rakumin da yake lauta masa kaya yakan sa shi wani kara, to haka ma al’arshi yake samun wannan karar alamar jin nauyi. Wasu kuwa suna nuni da cewa mala’iku hudu ne suke dauke da wannan al’arshin, kuma zai yi musu nauyi don haka zasu komai su takwas a ranar lahira saboda nauyinsa, (Abu Dawud: j 4, babul Jahmiyya. J 1, babi 13. Ibn Majah: j 1, b 13. Da wasu littattafai masu yawa).
Allah a Gajimare!
A lokacin da kuma tambaya ta taso cewa to ke nan kafin Allah ya halicci al’arshi ina yake kuma?. A nan ne kuma sai aka samu wata hanyar da za a amsa wannan tambayar maimakon yarda da cewa wadannan ruwayoyin ba su da wani inganci. Sai masu amsawa suka kawo wasu ruwayoyin da suke nuni da cewa yana kan wani gajimare!.
Sai dai masu bayar da amsa sun mance abu guda cewar tambaya ba zata kare ba kuma ba zata gushe ba, domin wata tambayar zata sake fuskantar su cewa to ina Allah yake kafin kuma ya halicci wannan gajimaren. Idan sun kawo wani abu daban ba zasu tsira ba domin shi ma tambaya zata hau kansa. Amma idan sun tsaya kan akidar gajimare to ya lizimta musu ko dai su karBi cewa gajimare fararre ne don haka tambaya zata ci gaba ke nan. Ko kuma su bayar da amsar cewa gajimare maras farko ne wato azali ne kamar Allah sai wannan ya lizimta musu samun alloli da ubangizai masu yawa da ya wuce daya. Da wannan ke nan sun rusa akidar tauhidi mai kadaita Allah tilo.
Don haka matukar masu akidar ba wa Allah wuri suna riko da akidarsu to suna da abubuwa biyu a gabansu; wato tambayar da ba ta iya karewa har abada abin da muka fi sani da tasalsul, ko kuma yarda da kididdigar Allah wanda lamari ne wanda ya rushe Kadaitakarsa kai tsaye. Kuma duka wadannan akidoji guda biyu mustahili ne ga ubangijin talikai!.
***
Da wannan ne zamu ga wadannan ruwyoyin da suka kawo sun nuna samuwar wuri ga Allah madaukaki. Kuma yana cikin gajimare kafin ya yi sauran halittu, sai dai wannan gajimaren Ubangiji ne shi ma? ko kuma shi ma abin halitta ne? Wannan ne lamarin da ba su yi bayaninsa ba.
Kuma ruwayoyin sun nuna cewa bayan Allah ya yi halitta ne ya zaBi al’arshi a matsayin wurin zamansa. Kuma da ya zauna kan al’arshi saboda nauyinsa sai ya rika yin wata kara. A cikin wannan akwai ba wa Allah nauyi alhain ba shi da nauyi kuma ba shi da rashin nauyi duka baki daya.
Sannan wadannan ruwayoyin sun nuna cewa Allah ya canja wuri bayan ya yi halitta daga gajimare zuwa al’arshi. Kuma duk lokacin salla yana canja wuri ya taso daga kan al’arshi ya zo ya tsaya gaban masu salla. Ke nan Allah ko da yaushe yana cikin zirga zirga ne daga wuri zuwa wani wuri.
Wadannan abubuwan baki daya suna nuna mana cewa Allah jiki ne domin al’arshi yana kan kahonin shanu, ko kan kayar kifi, ko kan sarari, ko a hannun mala’iku, ko kuma a kan sammai. Kuma a kan kome ma yake to lallai shi jiki ne ke nan, kuma ubangijin da yake bukatarsa yana zama shi ma jiki ne ke nan.
Malaman ‘yan Sunna daga ma’abota mazhabobi hudu sun tafi a kan cewa Allah yana kan al’arshi abin da yake tabbatar masa da iyaka da jiki da sauran siffofin halittu. Hatta da Ahmad dan Hambal lokacin da ake tambayarsa kan ayar nan da take cewa: "Yana tare da ku duk inda kuke…” sai yake nuni da cewa Ubangiji yana kan al’arshi sai dai wannan ayar tana nufin yana kewaye da komai ne domin dai ya tabbatar da cewa Allah yana kan al’arshi ke nan.
Abuhanifa ma yana karfafa cewa Allah ba ya kasa yana sama ne, kuma Baihaki ya karfafi wannan maganar ta Abuhanifa yana mai karfafa cewa lallai Ubangiji ba ya kasa, kuma lallai yana sama ne, (Al’uluwwu lil’aliyyil gaffar: sh 101, 103, 120). Haka nan Maliku da Shafi’i suna karfafa wannan lamarin na cewa Allah yana sama yayin da suke karfafa cewa Allah yana kan al’arshi ne.
Asalin wannan akidar ta taso ne daga dogaro da ruwayoyin da suka zo da wannan akidar, ruwayoyin da suka zo da yiwuwar ganin Allah da wadanda suka ba shi wuri da suka karBo daga Abuhuraira da waninsa su ne suka haifar da wannan akidar. A bisa asalin da suke dogara da shi maimakon duba ayoyin Kur’ani da koyarwarsa da abin da ya zo daga alayen annabinsa (a.s) sai suka shiga dogaro da wadannan ruwayoyin da tawilin ayoyin Kur’ani don su yi daidai da abin da ya zo a ruwayoyin da suka nakalto (Fathul majid: aya 67; kitabut tauhid: sh 213).
 
Hafiz Muhammad Sa’id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram) (hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: