bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:30:12
Don haka ne ma samuwar wasu hadisai marasa yawa a cikin wasu litattafansu ba ya damunsu sakamakon cewa a wurinsu ba su inganta ba kamar yadda malamansu suka yi nuni da hakan
Lambar Labari: 313
RA’AYOYIN ‘YAN SUNNA
Tayiwu wasu ruwayoyi su zo a littattafan Shi’a da zamu ga kamar suna da wata ma’anar bayar da jiki ko yiwuwar gani ga mahalicci da muke iya gani a Buhari da Muslim da sauran litattafan ‘yan Sunna, don haka wasu zasu iya cewa ke nan abin bai keBanta da malaman ‘yan Sunna ba. Sai dai akwai muhimman abubuwan da za a yi la’akari da su a nan kamar haka:
1. SaBanin Mahanga kan Ruwayoyi
Daya daga cikin muhimmin saBani tsakanin malaman ‘yan Shi’a da malaman ‘yan Sunna shi ne cewar malaman Sunna sun yarda da cewa duk abin da ya zo a cikin Buhari ko Muslim to ya inganta babu wani kokwanto. Kuma idan ma wani ya rantse kan cewa duk abin da yake ciki maganar annabi ce to babu kaffara kansa don rantsuwar ta inganta!. Amma malaman Shi’a ba su taBa yarda da samuwar wani littafi da duk abin da yake cikinsa ya inganta ba hatta da littattafai hudu nasu shahararru, don haka ne suke ganin wasu hadisan sun inganta wasu ba su inganta ba.
Don haka ne ma samuwar wasu hadisai marasa yawa a cikin wasu litattafansu ba ya damunsu sakamakon cewa a wurinsu ba su inganta ba kamar yadda malamansu suka yi nuni da hakan.
2. Hadisan Tauhidi
Idan mun duba litattafan hadisan Sunna zamu ga dukkansu suna da nuni zuwa ga sanya jiki ga Allah madaukaki kuma ba mu samu wani Hadisi daya ba wanda yake karyata wannan lamarin. Don haka ne zamu ga koyarwar da take cikinsu in ban da sanya jiki da gaBoBi ga Allah (s.w.t) babu wani abu da suke kunshe da shi. Amma a litattafan Shi’a akwai daruruwan hadisai da suke suka kuma suke kore duk wata magana da take nuni da samuwar jiki ko wata gaBa ga Allah madaukaki.
Akwai ma babobi da fasaloli da suke da "Take” kai tsaye kan wannan, kamar "Babin kore ganin Allah”, "Babin hani ga siffanta Allah da jiki ko wata sura ko motsi ko cirata”, "Kore kamantuwa”, da zamu ga irin wadannan kan bayanan fasaloli da babobi game da Allah madaukaki, (Kafi, Tauhidus saduq, Biharun anwar).
3. Hadisan Tauhidi gun Shi’a
Hadisan da suke kore duk wata sifa ta jiki ko gaBa ko kamantawa ga Allah (s.w.t) da suka zo a litattafan Shi’a sun bayani karara ta yadda babu wani kokwanto da ya rage ga wani daga malaman Shi’a kan wannan lamarin. Sun zo da sanadodi da bayanai masu karfi da dukkan maruwaita na ‘yan Shi’a suka sallama suka karBe su baki daya, kuma su ne kashin bayan tafiyar akidar shi’anci, kuma duk wata ruwaya da ta saBa musu to ba ta da wani matsayi ko kima gun malaman Shi’a balle har ma a yi magana kan ta.
4.Kirkirar Ruwaya
Idan muka duba ruwayoyin da suka zo da wani abu mai kama da hakan a cikin litattafan Shi’a zamu ga cewa ba su da wani sanadi mai kwari, wasunsu ma ruwaya ce ta wani malami daga malaman ‘yan Sunna mai imani da jiki ga Allah kamar Mukatil dan Sulaiman sai ya jingina ta ga jagororin Shi’a da suka gabata.
Don haka duk wani abu na akida game da sanin Allah da siffofinsa dole ne a koma wa maganar manyan malaman wannan mazhaba don tabbatar da me suke imani da shi. Kamar dai yadda ake koma wa litattafan Sunna da malamansu don sanin abin da suka yi imani da shi game da Ubangiji madaukaki.
Misalan Hadisan Shi’a
Hadisan shi’anci sun karfafa da yawan gaske cewa; ba a lissafa Allah da wuri da zamani, don haka bai halatta ba wani ya yi tambaya kan ina Allah yake ko yaushe ya kasance, domin wannan tambaya ce da za a iya yin ta ga wanda yake da dabaibayi da zamani da wuri. Haka nan ba a siffanta Allah da motsi ko tafiya, ko cirata daga wuri zuwa wani wurin domin Allah yana ko’ina da zatinsa, wani wuri ba shi da bambanci gunsa da wani wurin, sai dai ya sanya shamaki ga mutane gwargwadon yadda ya ajiye komai mahallinsa ne.
Don haka duk wani abu da yake siffantuwa da zamani, ko wuri, ko motsi, ko rashin motsi, ko cirata, duk suna daga cikin siffofin halittunsa ne masu iyaka masu bukatuwa zuwa wannan abubuwan. Domin zamani yana hawa kan abin da yake motsi ne, idan abu ba shi da motsi ba ya cirata to babu ma’anar zamani ko wuri gare shi. Allah kuwa ya barranta daga dukkan wadannan siffofin na masu iyaka masu bukatuwa zuwa wuri da zamani.
Abubasir ya karBo daga Imam Sadik (a.s) cewa: Ba a siffanta Allah madaukaki da zamani ko wuri, ko motsi ko cirata, ko rashin motsi, shi ne dai ya halicci zamani da wuri da motsi da rashin motsi, Allah ya barranta daga abin da masu zalunci suke fada, (Tauhid: Saduq; j 1, b 2, da b 8, sh 7- 31, da 9-107, da biharul anwar: b 13, da 14, sh 287, sh 309).
Hatta da ayoyin Kur’ani masu yawa da suka zo bisa ka’idar luga da aro da kinaya kamar yadda zamu gani suna da kyakkyawar fassara da Ahlul-baiti suka yi musu. Misalin ayar nan ta "… Al’arshinsa ya kasance kan ruwa…”. Zamu ga Imam Sadik yana cewa da Dawud Rakki, me suke cewa ne?. Sai Dawud ya ce: Suna cewa: Al’arshi yana kan ruwa, shi kuwa Allah yana kansa. Sai ya ce: Duk wanda ya raya hakan ya yi karya, domin ya sanya Allah abin dauka ke nan, kuma ya siffanta shi da siffofin abubuwan halitta, kuma ya lizimce shi cewa abin da ya dauke shi ya fi shi karfi ke nan, (Tauhid Saduq: Babul Arshi wal Kursiyyi).
Ya’akub Sarraj yana cewa da Imam Sadik (a.s) daga cikin abokanmu akwai wadanda suka dauka cewa Allah yana da kama da mutum, yana da fuska, wani saurayi ne mai nadadden gashi. Yayin da Imam Sadik ya ji wannan magana sai ya yi sujada sannan sai ya dago kansa ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, babu wani abu da ya yi kama da shi, idanuwa ba zasu iya riskar sa ba, ilimin mutum ba zai iya sanin hakikaninsa ba, ba ya haihuwa balle a samu kamarsa domin kowa yana kama da babansa. Ubangiji ba shi da uwa da uba balle ya yi kama da wasu da suka gabace shi, ba shi da wani tsara a cikin halittu baki daya, kuma ya fi karfin ya siffantu da siffofin ababan halitta, (Tauhid; Saduq: babu nafyul jism wassura).
Yusuf bin Zanyana ya kai kukan abin da ya ji a majlisin Maliku cewa: Wasu suna cewa; Allah yana da fuska da jiki. Wasu ma suna cewa; yana da hannaye saboda ya ce da Iblis: "… Me ya sa ka ki yin sujada ga abin da na halitta da hannayena…”. Wasu kuwa suna cewa; Allah saurayi dan shekara talatin ne. Me zaka ce game da wannan magana tasu.
Sai Imam Sadik (a.s) ya yi raddin dukkan wadannan maganganu daya bayan daya. Ya jingina ya yi yabo ga Allah sannan sai ya yi kakkausan suka kan wadannan ra’ayoyin yana mai neman afuwar Allah da barrantar da shi da siffantuwa da wadannan siffofin a cikin wani Hadisi mai tsawo.
Hadisai game da tsarkake Allah daga dukkan wasu siffofin tawaya na halittu suna da yawa, kuma imamai daga alayen manzon Allah (s.a.w) sun yi bayanai masu yawa da suka zo a ruwayoyi masu yawan gaske da ba sa kirguwa kan wannan lamarin. Don haka duk wata tawaya da take komawa zuwa ga abin halitta da siffarsa shi’anci ya barrantar da Allah daga gare ta.
 
 
Hafiz Muhammad Sa’id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram) (hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com).

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: