bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:32:00
Babu wani yanayi ko buqata da zata sanya sadakin ya zama wani abu me kama da ba ni gishiri in baka manda sai dai idan ma'auratan sun qulla yarjejeniyar
Lambar Labari: 314

4.  Sadaki
A wajen qulla aure ya zama dole a ambaci sadaki na wata sananniyar dukiya ta kuxi ko na wani aiki, a bisa adadin da ya kuvuta daga qaruwa ko raguwa. Matar na iya tantace dukiyarta ta hanyar gani, wannan na wadatarwa, amma ba lallene sai ta auna ta ba, ko kimanta ta ko qirga ta ba, qulla auren mutu'a ba wai ya taqaita ga musayar abubuwa kawai ba ne, a a shi ma aure ne. Ko da kuwa an xauke shi a matsayin 'haya', wannan ba yana nufin dai-dai yake da siyayya ko musanye ba. Don haka duk wata matsala da ka iya tasowa a dalilin rashin ganin sadaki an kawar da ita. Amma dangane da dukiyar da ba ta kusa, ya wadatar a siffanta sadakin ta yadda matar zata kawar da jahiltar ta, wato dai a siffanta ta yadda take (Matajir 11, 300 Sharhul Lum'a 5, 284).
Babu wani yanayi ko buqata da zata sanya sadakin ya zama wani abu me kama da ba ni gishiri in baka manda sai dai idan ma'auratan sun qulla yarjejeniyar a kan hakan ko da kuwa abin bai wuce tsabar alkama ba (Wasa'il x4 467 Hadiss 5), akwai hadisin da ya zo a kan hakan bayan sanannen hadisin nan mai cewa; 'duk matar da ta xaura auren mutu'a (matajir 11, 300, Masalik 1 538) idan ba a ambaci sadaki ba auren ya kusata ya zama vatacce', kamar dai yadda ya gabata mun kawo hadisai kan wannan lamarin to a nan ma akwai hadisai da yawa da suka kawo hakan (Wasa'il x4 465 – 66 hadiss 1).
Mace kan iya karvar sadakinta a farkon xaura aure a nan miji ba shi da damar hana ta sadakinta ta ko wane hali sai da dalili, kamar vacin aure tun a farkonsa (bayani zai zo nan gaba) hadisai da yawa sun yi magana a kan abin da ya shafi hakan (Ibid 482 Hadiss 1 – 2, 483 hadiss 1).
A inda kuma zai zama an kulla auren kafin ayyana tsawon lokaci (mudda) sai mijin ya fasa auren ta ta hanyar janye auren, a nan wajibi ne ya bawa matar rabin sadakinta da aka ambata, saboda janyewar da ya yi, dalili shi ne yanayin ya yi dai-dai da sakin mace kafin saduwa da ita a auren da'imi (Sharhul Lum'a 5, 285, Shara'i ii, Matajir 11, 300, Malik 1 538).
Amma idan ace mijin rage lokacin ya yi (ba dukan lokacin ya janye ba) a nan malamai sun tafi a kan ra'ayoyi mabanbanta, a wajan Shehul Ansari da Shahidus Sani; a nan ba zai tava zama xaya da na farko ba (wato janye lokacin gaba xaya) wanda shi fasa auren ne, tun da a nan (na biyun) abin la'akari shi ne auren da suka yi na mutu'a ne abin da zai yi shi ne, ya ba ta sadakinta duka (Matajir ii, 30, Sharhul Lum'a 5, 285. Masalik I, sh538).
Shahidus Sani ya warware ban-banci da ke tsakanin maganar farko da ta biyu ta hanyar kawo tambayoyi, yana mai cewa; me ya sa aka ce a bawa mace rabin sadaqi bayan an janye aure? A nan akwai yiyuwar abubuwa biyu.
Na xaya daga cikin su:-  Akwai hadisi da ya yi Magana a kan rashin saduwa a auren mutu’a, ya bayyana cewa yin hakan dai dai yake da saki a auren da'imi, wajibi ne a bayar da rabin sadakin matuqar ba a sadu ba, amma idan an sadu dole a bada gaba xayan sadakin, wannan haka yake. Dalilin da ya sa ake ba da rabin saboda rashin saduwa.  Akwai tambaya da ke cewa me ya sa ya zama dole a biya sadakin? Amsa: A auren da’imi abin la'akaari shi ne saduwa, shi kuwa auren mutu'a ya banbanta saboda qaiyadajjen lokacinsa wannan ne ya sa dole ayi la'akari da lokaci (a auren mutu'a) (Masalik 1 sh538).
Shahidus Sani ya qara da cewa waxannan abubuwa biyu sun fayyace mana cewa mijin dolene idan zai rage lokacin ya rage kasa da rabi, ba wai maganar saduwaba, dangane da maganar farko matar zata karvi sadakinta ne duka, amma a magana ta biyu zata karvi rabin sadakin ne kawai a qarshe ya kawo cewa magana ta biyun tafi inganci da zama dai-dai matuqar zamu karvi hadisin da aka rawaito daga imam Hassai (a.s) lokacin da aka tambayeshi game da wanda ya yafe ragowar lokacinsa game da matarsa ta mutu'a kafin saduwa, sai ya bada amsa yana cewa; 'matar dole ne ta dawo da rabin sadakin idan an ba ta tun farko' (Wasa'il x4 483, Hadiss 1).



Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: