bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:39:53
Ko da an dawa da lokacin, tare da cewa an yi jima'i ko ma ba a yi ba, babu abin da ya shafe ta tun da rage ko janye lokaci dai-dai yake da yafe bashi daga wajan mijin zuwa matar
Lambar Labari: 315


Amma sheikh Muhammad Hassan ya ce biyan dukkan sadakin ko rabi ya dogara ga shin an sadu ko ba a sadu ba? amma janyewa dai-dai yake da amfani da lokacin gaba xaya. Abin nufi idan mijin ya ba ta ragowar lokacin saboda ya ga cewa wannan lokacin da suka yi ya ishe shi, don haka yana da damar bar mata ragowa. Kaga wannan ba yana nufin wai ta karvi rabin sada kinta ba. A nan ya yi kama da a ce mace ta dawo da dukkan sadakinta a auren da'imi, idan matar ta nuna cewa sadakinta ne, haka ne saboda barin lokacin ya nuna cewa wannan mijin na ta ba mijinta ba ne gaba xaya, don haka rage mata lokacin (auren) ba shi da alaqa da rage sadaki zuwa rabi. Abin lura shi ne, shin an sadu ko ba a sadu ba a auren? Idan an sadu sannan ya janye ko ya rage lokacin to matar ta ci dukkan sadakinta tun da an riga an sadu kafin rage ko janye lokaci..  
Ko da an dawa da lokacin, tare da cewa an yi jima'i ko ma ba a yi ba, babu abin da ya shafe ta tun da rage ko janye lokaci dai-dai yake da yafe bashi daga wajan mijin zuwa matar.  
Idan kuwa matar ce taga damar janye ko yafe lokacin mutu'a a nan ko da saduwa ko babu za ta biya shi sadakin dai-dai da lokacin da ta rage, misali:  idan sun qulla auren kwana talatin (30) a kan sadaki N3000 (Naira dubu uku) sai matar ta yanke auren bayan kwana ashirin mijin zai ba ta N2000 (Naira dubu biyu) kuxin kwana ashirin na kwanakin da suka yi tare. Idan da matar taqi bada lokaci ko kaxan ta rasa sadakinta gaba xaya, saboda gwargwadon lokacin da ta bayar gwargwadon sadakinta. Auren mutu'a yana nufin mace tana matsayin 'aro' ko 'haya'.
Vangare ba biyu: na waxanannan hadisai sun yi magana a kan abubuwa masu kama da hakan:- Misali an tambayi Imam Ja'afar (a.s) yiwuwar mutum ya rage wani abu daga sadaki idan matar ta qi ta miqa kanta ga mijin sai ya amsa da cewa: 'An yarda ka riqe abin da zaka iya riqewa ,(ma’ana abin da baka riga ka ba ta ba). Dan haka, idan ta canja maganarta to ka karva wani adadin  kuxi na lissafin kwanakin da ta sava'.  
Amma kuma idan matar tana hana mutumin kanta saboda wani dalili wamda shari’a ta amince, kamar jinin haila ko tsoran wani azzalimi to ba za a rage sadakin ba. Wani mutum ya zo wajen imam Ja’afar (a.s) ya ce:  'Na qulla auren mutu’a da wata mata na tsawan wata xaya amma matar ta zo gare ni a wasu kwanaki, wasu kwanakin kuwa ba ta zo ba. Sai Imam ya ce: 'ka rage wani kaso na kudin sadakinta wanda ya yi daidai da kwanakin da ta qi zuwa, amma ban da kwanakinta na haila, domin su mallakinta ne'.
Idan ta bayyana cewa auren bai haltta ba, saboda dama can matar tana da miji , ko kuma tana iddar auranta na baya, ko kuma ta haramta ga mutumin saboda dangantaka ta jini, ko dai saboda wani dalili, to za a xauki xaya daga waxannan matakai masu zuwa:-
Idan har an gabatar da jima’i a auren, kuma matar ba ta da masaniyar cewa auren bai halatta ba a lokacin jima’in, to za a ba ta sadakin da ya dace da ita', dalili shi ne dole ne a mutunta jima’in ta hanyar ba da sadaki, tun da auren bai halatta ba, sadakin da suka yi yarjejeniya ya rushe, don haka sai dai a ba ta sadakin da ya dace da ita.  
Amma Magana kan dewa shin sadakin da ya ba ta dai-dai yake da wanda ake bayarwa a auren da’imi ko kuma za a yi la’akari da tsawan auren mutu'ar ne! hukuncin da ya fi rinjaye wanda ya fito daga Shehul Ansari da Shekh Muhammad Hassan. Sun tafi a kan cewa abin da ya kamata na sadaki” dai-dai yake da na aure da’imi. Taba-taba’i  ya sava a kan hakan da cewa: abin da ya kamata na sadaki yana fansar jima’in da aka yi bisa kuskure ne. Tun da aure ya vaci ba tare da sanin mijin da matar ba, jima'in nasa kuskure ne, don haka dole mijin ya biya abin da ya kamata a aure da’imi, wanda shi ake buqata yayin duk wani kuskuren yin jima’i.  Ba a la’akari da tsawan lokacin da matar ta yi da mijin, kamar yadda ba bambanci tsakanin jima’in sau xaya ne ko da yawa, matuqar dai kuskure aka yi.  
Idan ta bayyana cewa auren bai haltta ba tun kafin jima’i ya kasance, matar ba za a ba ta sadaki ba, abin da ke sa a ba da sadaki shi ne halaccin aure ko samuwar jima’i. Shahid Sani ya ce: malamai sun haxu a kan wannan maganar.  
Idan an sami jima’i a cikin auren kuma ta san cewa auren haramtacce ne matar ba ta da haqqin sadaki da zarar ta bayyana cewa auren haramtacce ne, tun da babu sadaki in a ka yi zina.
A cikin waxannan yanayoyin guda uku da aka ambata a baya, idan mijin ya riga ya ba ta sadakin gaba xaya, dole ta dawo masa da sadakin ko wani vangare daga ciki da zarar ta gano rashin ingancin auren. Idan ba ta da abin da zata biya, to ana binta, kuma ba a la'akari da hanyar da ta kashe kuxin, misali, kashe kuxin ta yi ko kuma sace wa aka yi.  
Idan da matar zata mutu lokacin da suke cikin auen mutu'a, ko da kafin su san juna ne, to ba za a rage mata sadakinta ba kamar yadda yake a auren da’imi.

*_Ibrahim Muhammad Sa'id_*
*whatsApp, Telegram, Viber, etc*
_+2348068985568_
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,
Ibraheemsaeedkano@yahoo.com


*HAIDAR CENTER*

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: