bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:46:43
Misra kuwa a cikin bahsinsa a kan wahabiyanci yana da wani nazari wanda yake bayyanar da hakikanin wahabiyanci, wanda yake bayyanar mana da bambancin
Lambar Labari: 317
Neman Canza Ra’ayi A Cikin Akidun Wahabiyanci
Wahabiyanci ya ginu ne a kan salafiyya wanda yake fito-na-fito da dukkan wani canji da dan Adam zai samu a rayuwa. A shekara ta 1344 ranar da Abdul aziz Bn Abdurrahaman ya hau karagar mulkin Sa’udiyya sai ya zama tilas a gare shi a kan canja salon mulkinsa ta yadda zai yi daidai da zamanin da yake ciki, ta yadda zai canza rayuwar wahabiyawa wacce take tafiya a kan rayuwar mutanen kauye. Sakamakon shigowar abubuwan zamani ne fa kamar su telfon mota da keke da makamantansu, sai ya yarda da a yi amfani da su, a nan ne fa ya gamu da fushin masu tsattsauran ra’ayin wahabiyanci inda aka zubar da jini ta hanyar (Ikhwan) kamar yadda aka sani a tarihi.
Ahmad Amin marubucin nan na Misra kuwa a cikin bahsinsa a kan wahabiyanci yana da wani nazari wanda yake bayyanar da hakikanin wahabiyanci, wanda yake bayyanar mana da bambancin da yake akwai tsakanin wahabiyanci na zamanin da, da wanda yake akwai yanzu, ga abin da Ahmad Amin yake cewa:
Wahabiyawa ba su yi tunani da kyau ba dangane da cigaban zamani, mafi yawa daga ciki, ban da garuruwan da suke rayuwa a cikinsu ba su dauki sauran garuruwan da sauran musulmin suke rayuwa ba a matsayin garuruwan musulmi ba, domin su a wajensu suna cikin Bidi’a, sannan suna ganin dole ne a yake su.
Amma lokacin da Bn Mas’ud ya hau karagar Mulki, ya fuskanci barazana daga sassa guda biyu ta yadda ya sanya shi dole ya sasanta da su. Na farko su ne shugabannin addini a Najad wadanda suke tsananin biyayya ga Muhammad Bn Abdulwahab, sannan suna tsananin gaba da dukkan sabon abu. Na biyu kuwa suna fuskantar guguwar sabon ci gaba na tsarin hukuma ta yadda yana bukatuwa zuwa ga wadan su na’urori na zamani.
A wannan lokaci sai hukuma ta tsaya a tsakiya wato tsakanin wannan tsanani na mutanen Najad da kuma Guguwar cigaban zamani, ta yadda suka dauki sauran musulmin da suke rayuwa a wasu garuruwa a matsayin musulmi sannan suka dauki ilimin addini da na zamani a matsayin cewa dukkansu abin koyo ne, sannan suka gina tsarin hukumarsu dai-dai- da na zamani (Zua’maul iskah fi asril Hadisi Ahmad Amin. Shafi na 20-21).
Amma abin farin ciki shugabanni sa’udiyya sun canza salo a kan wancan tunaninsu na kin yarda da sauran musulmi da fito na fito da dukkan wani sabon abu da sunan gujewa bidi’a, wannan kuwa ya faru ne sakamakon wasu dalilai masu yawa, daga cikinsu kuwa su ne kamar yadda ya kasance Amerika ta yi kaka gida a cikin saudiyya da yadda jamhuriyar musulunci ta Iran take jagorantar fito na fito da sahayuna, wannan ya janyo Sa’udiyya ta canza ra’ayoyinta dangane da Jamhuriyar musulunci ta Iran, sannan suka dawo daga tunaninsu na kafitrta sauran musulmin da ba sahu daya suke ba, Musamman kasancewar hukumar saudiyya ta yanzu wacce ta sanya wa kanta suna da mai hidimar harami guda biyu, ka ga ke nan babu wani mai abu mai kyau wanda ya fi sai su dawo su canza ra’ayinsu na da, ta yadda zasu karbi bakuncin dimbin sauran al’ummar musulmi da suke bakuntar Makka da Madina domin aikin Hajji a kowace shekara.


Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: