bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:52:29
Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, ya rayayye ya tsayayye, da rahamarka nake neman taimako to ka taimaka mini
Lambar Labari: 320
أدعية فاطمة الزهراء (عليها السلام)
Addu’ar Fatima Azzahra (a.s)

لفاطمة الزهراء (عليها السلام) عدة أدعية عُرفت باسمها (عليها السلام)، ومنها ما ورد في كتاب مُهَجِ الدعَوَات:

Sayyida Zahra (a.s) tana da addu’o’i masu yawa da aka san su da sunanta (a.s), daga ciki akwai abin da ya zo a littafin Muhajid Da’awat:
الدعاء الأول:
بِسْمِ اللهِ الرَّحمنِ الرَّحيمِ، يَا حَيُّ يَا قَيُّوم، بِرَحمَتِكَ أستَغيثُ فأَغِثْنِي، وَلا تَكِلْنِي إِلى نَفسي طَرفَةَ عَينٍ أَبَداً، وأَصلِحْ لِي شَأنِي كُلِّه.
Addu’ar Farko:
Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, ya rayayye ya tsayayye, da rahamarka nake neman taimako to ka taimaka mini, ka da ka jingina ni zuwa ga kaina ko da qiftawar ido har abada, ka gyara lamarina gare ni dukansa.
الدعاء الثاني:
اللَّهُمَّ قَنِّعْنِي بِمَا رَزَقْتَنِي واستُرنِي وَعَافِنِي أبداً ما أبقيتَنِي، واغفِرْ لي وارحَمنِي، اللَّهُمَّ لا تُعيِنَنِي في طَلَبِ مَا لا تقدِّر لي، وَمَا قَدَّرتَهُ علَيَّ فاجعلهُ مُيَسَّرا سَهلاً؛ اللَّهُمَّ كافِئ عَنِّي وَالِدَيَّ وَكُلَّ مَن لهُ نِعمَة علَيَّ خيرُ مُكَافَأةٍ، اللَّهُمَّ فَرِّغنِي لما خَلقتَنِي لَهُ، وَلا تُشغِلنِي لما تَكَفَّلتَ لي به، ولا تعذِّبنِي وَأنا استغفرُك، وَلا تَحرِمني وَأنَا أَسأَلُك؛ اللَّهُمَّ ذَلِّل نَفسِي فِي نَفسِي، وَعَظِّم شَأنَكَ في نَفسي، وأَلهِمْنِي طاعَتَك، وَالعَمَلَ بِما يُرضِيكَ، والتجنُّبَ لما يُسخِطُك يا أرحَمَ الرَّاحِمِين.
Addu’a ta Biyu:
Ubangiji ka wadatar da ni da abin da ka arzuta ni, ka suturta ni, ka ba ni lafiya har abada matukar ka wanzar da ni, kuma ka gafarta mini ka ji qai  na. Ubangiji ka da ka taimaka mini neman abin da ba ka qaddara mini ba, ka kuma yassare mini abin da ka qaddara mini cikin sauqi; Ubangiji ka saka mini alheri ni da iyayena da duk wanda yake da wani haqqi a kaina fiyayyar sakawa. Ubangiji ka shagaltar da ni don abin da ka halitta ni don shi, ka da ka shagaltar da ni da abin da ka lamunce mini shi, ka da azabtar da ni alhalin ina neman gafararka, kuma ka da ka hana ni alhalin ni ina roqonka; Ubangiji ka qasqanta kaina ga kaina, ka girmama sha'aninka a raina, ka kimsa mini biyayyarka, da aiki da yardarka, da nisantar abin da zai sanya fushinka, ya mafi jin qan masu jin qai.

الدعاء الثالث:
اللَّهُمَّ بِحقِّ العَرشِ وَمَن عَلاَّه، وَبِحقِّ الوَحي وَمن أَوحَاه، وَبِحقِّ النَّبِي وَمَن نَبَّاه، وَبِحقِّ البَيت وَمَن بَنَاه، يا سَامِعَ كلَّ صَوتٍ، يا جَامِعَ كُلَّ فَوتٍ، يَا بَارئَ النُّفُوسِ بَعدَ المَوتِ، صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَأهلِ بَيتِهِ وآتِنَا وَجميعَ المُؤمِنينَ وَالمؤمِنَاتِ فِي مَشَارقِ الأرضِ وَمَغارِبِهَا فَرَجاً مِن عِندِك عاجلاً، بِشَهَادَةِ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ الله، وَأنَّ مُحَمَّداً عَبدُكَ وَرَسُولُك صَلَّى اللهُ عَليهِ وَعَلى ذُرِّيتِهِ الطَّيِّبِينَ الطَّاهِرِينَ، وَسَلَّمَ تَسْلِيماً .
Addu'a ta Uku:
Ubangiji don girman al'arshi da wanda ya xaukaka shi, da girman wahayi da wanda ya saukar da shi, da girman annabi da wanda ya yi masa annabci, da girman xaki da wanda ya gina shi. Ya mai jin kowane sauti, ya mai haxa duk mai tserewa, ya mai halitta rayuka bayan mutuwa. Ka yi tsira ga Muhammad da ahlin gidansa, ka zo mana da mu da duk muminai maza da mata a gabashin duniya da yammacinta da farin ciki daga gare ka cikin sauri, da shedar cewa babu abin bauta sai Allah, kuma Muhammad bawanka ne manzonka ne, amincin Allah ya tabbata gare shi da zuriyarsa tsarkaka masu tsarki, da aminci mai yawa.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: