bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:56:13
kuma ya san hakan batacce ne saboda wasu dalilai kamar haka: a- Akidun Shi'a sun cika litattafai masu yawa wadanda su ne madogara, kuma kowa ya na iya dauka ya karanta,
Lambar Labari: 321
SHI’ANCI FARISAWA
Akwai kuma wani abu daban cikin tasawwurin Farisancin Shi’anci kuma shi ne cewa dukkan ko galibin Shi'a Farisawa ne, kuma Farisancin su ya yi galaba a kansu har sai da ya mamaye Shi’anci kuma wannan yakan kai ga karo da shari’ar musulunci saboda sabawar sa da wadannan akidoiji na musulunci kamar yadda suka raya, kuma wasunsu ma sun shelanta hakan a fili kamar yadda nan gaba zamu kawo hakan cikin wasu ra’ayoyi a kan wannan, kuma da sannu zaka ga wannan ra'ayi cewa barna ne ba daidai ba ne, kuma dukkan wanda ya san tarihin musulmi da akidunsu ya san ba haka ba ne, kuma ya san hakan batacce ne saboda wasu dalilai kamar haka:
a- Akidun Shi'a sun cika litattafai masu yawa wadanda su ne madogara, kuma kowa ya na iya dauka ya karanta, kuma suna hannun marubuta da masu bincike a dukkan laburorin duniya, kuma madogarar akidun Shi'a su ne: littafin Kur'ani da Sunna da ijma’I da hankali kamar yadda ya gabata, kuma mun yi nuni zuwa ga litattafai da suka yi bayanin hakan dalla-dalla hada da littafin ‘awa’ilul makalat’ na sheikh Mufid, da aka’id na Saduk da durar da gurar na sayyid murtadha, da a’ayusshi’a na sayyid Muhsin al’Amin, da kuma litattafan hadisai da kuma litattafai hudu wadanda Shi'a suka dogara kansu a jumlace wadanda suka hada da "Man’la’ yahdhuruhul fakih", na Saduk, da "Usulul Kafi" na Muhammad kulaini, da "Tahzib" da "Istibsar", na sheikh Dusi, tare da cewa ba duk abin da yake cikinsu ba ne ya inganta gunmu.
b- Sannan kuma farisawa wani yanki ne kankani na yawan Shi'awan da suke wannan duniya tamu, wadanda suka hada da Larabawa, da Indiyawa, da Turkawa, da Afganawa, da Kurdawa, da Mutanen kasar Sin, da mutanen Tibet, da sauransu, don haka ke nan Farisawa wani bangare ne kawai.
c- Sannan kuma inda aka kafa dashen irin Shi’anci duk ya na yankin Larabawa ne na jazirar Larabawa, kuma a ‘yan shi’ar farko babu wani daga wanda ba balarabe ba sai mutum daya wanda yake shi ne salmanul muhammadi kamar yadda Annabi (S.A.W) ya ambace shi wanda shi bafarise ne. kuma an ambace shi a cikin dabaka ta farko na Shi'a wadanda suke daga kabilu daban-daban, kuma idan ka bi dabaka ta biyu da ta uku na Shi'a duk zaka samu mafi galibinsu duk Larabawa ne, kuma ba na son tsawaitawa a wannan wurin don akwai shi a litattafan tarihi kuma zamu kawo maka abin da zai tabbatar maka da hakan a karshen wannan fasali.
Tare da dukkan abin da muka riga muka kawo na bayani to mene ne, kuma ta ina ne Shi’anci ya kasance Farisanci har ma ake daukar wannan kamar wani abu da aka riga aka tabbatar da shi. Don haka ne domin mukawo duk abin da ya shafi wannan maudu’i to ya zama dole ne mu shiga yin bayanai dalla-dalla da kawo ra’ayoyi masu yawa da kuma dalilan da aka kawo don kafa dalili da nuna ingancin wadancan ra’ayoyi.
Kuma ina tabbatar maka idan ka karanta abubuwan da suka zo raunin abin da suka kawo zai bayyana gare ka, kuma zaka yi mamakin yadda irin wadannan marubuta duk da suna da ilimi da ba a rena shi amma suka gamsu da abin da suka kawo balle kuma har suna kawo shi domin su gamsar da wanin su saboda son rai da kuma bangaranci, Allah ya tsare mu daga wannan. Wannan kuwa ya na daga gamsuwa da wata akidar danne gaskiya da rashin ba wa haske damar haskaka masa akidarsa da abin da ya riga ya dogara a kai har ya ga irin abin da yake haifarwa sakamakon mummunar makauniyar biyayya, sai ya ci karo da dalili mai inganci sai ya watsar da shi, ba ya duba ma’aunan shari’a ya yi riko da su.
FASALI NA BIYU
Maganganun Masu Ganin Farisancin Shi’anci
magana kan danganta Shi’anci da Farisanci ta kasance ne a zamunan baya-bayan nan ne, kuma saboda wasu dalilai da yanayin siyasa wadanda mafi muhimmcinsu su ne:
Saboda kasancewar Farisawa suna da bakin jini gun Larabawa saboda wasu dalilai daban-daban, kuma saboda Shi'a sun kasance jama’a ce wacce take mai gaba da hukumar lokacin da ya gabata na farkon musulunci a lokacin Umayyawa da Abbasawa.
Kuma ta wata fuska wannan ya faru ne domin ganin an taskace Shi’anci da wanda ake ganin ya na da bakin jini gun Larabawa, musamman ma domin ganin Larabawa ba su karbi wannan mazhabi ba, kuma wannan da’awa da ake yi ta taskace Shi’anci da Farisanci daya ce daga cikin kokarin da ake yi na ganin yin zagon kasa ga Shi’anci. Amma dalilan da su masu wannan kage kan Shi’anci suka kawo a matsayin dalilan da suka kai ga kyamar juna tsakanin Larabawa da Farisawa su ne kamar haka:
1- Farisawa ba su kasance suna banbancewa ba tsakanin musulunci da Larabci, kuma tun da musulunci ya kawar da daularsu kuma ya gama da su, to sai suka kasance bayan sun musulunta suna son dawo da martabarsu, kuma suka dauki hanyoyi biyu mai kyau da maras kyau, sai mulkin Umayyawa ya zo ya nemi taimakonsu wajen tafiyar da hukuma domin tsara lamuran daularsu sakamakon ci gaban da suke da shi na zamani, wani lokaci kuma a kan nemi taimakonsu domin fuskantar abokan gaba yayin sabani, kuma wasu daga cikinsu sun kama manyan mukamai a wadannan lokauta biyu abin da ya sanya su suka samu damar kutsawa cikin daula, kuma wannan ya sanya gaba tsakanin larabawan kansu da kuma Farisawa a daya bangaren, domin Larabawa suna ganin su ne suka dauki sakon musulunci zuwa ga al’umma, kuma su ne wadanda musulunci ya doru ya kafu bisa kafadunsu da wahalarsu domin su shiryar da al’ummu, to don me za a shugabantar da wani a kansu? a gabatar da shi a kansu tauraruwarsa ta yi sama ta filfila a kan tasu? Su sami matsayi mai girma da ba su da shi?
Sai Farisawa suka ga cewa su ne suke da ci gaba mai dadewa kuma sun fi sanin lamarin siyasar tafiyar da mulki fiye da Larabawa, da tafiyar da lamarin hukunci da daula, to don me za a gabatar da wanda ba shi da wannan siffofi na cancanta a kansu?. Sai wannan ya kai ga jayayya da gaba tsakanin al’umma, kuma wannan ya bar kufai mai muni a zukata na gaba da juna da kiyayya da mugun kulli tsakanin wadannan al’ummu biyu kamar yadda ya kai ga yin zagon kasa ga juna.
2- Bude wannan fage da samun wannan kafa da sabani da tsagewar bango da Farisawa suka shigo ta cikinsa, ya kai ga shigar wasu mutane da ba Larabawa ba kamar turkawa da wasunsu cikin mukaman daula, kuma wannan ya haifar da mummunan sakamako mai muni kwarai da gaske, kuma sai Sunan Farisawa ya fi baci kan wannan lamari domin da su ne aka fara wannan asakala, domin su ne farkon wanda ya bude wannan kofa abin da ya kai ga lalacewar halifanci daga baya.
3- ‘Yan mulkin kama karya sun iza wutar wannan matuka da gaske wacce suka azuzuta ta, domin tabbatar da maslaharsu ta hanyar bude wannan kofa da fadada ta da kuma kawo kage da karairayi domin karfafa wanan sabanin tsakanin wadannan jama’u biyu da suka dade suna asakala da rashin jutuwa da juna, kuma suka yi amfani da mustashrikai (Turawa masana gabas musamman kasashen musulmi da addinin musulunci) a kan wannan, sai ga shi an samu jama’ar musulmi da suka rayu a kan teburin nan na koyarwar mustashrikai da suke da karancin tunani da hankali sun kama sun fi mai kora shafi, suna tabbatar da wannan da’awowin karyar su. Sai suka sanya irin wadannan musulmi kamar wata wuka ce da ake dukan duk bangarorin musulmi da su domin rusa akidunsa da kawo tashin hankali da fadada sabani tsakanin mabiyansa, har wannan ya bar kufai mai muni mai girma da yake neman ganin bayan duk kokarin da aka yi, a yau ana bukatar wani kokari mai girma domin kawar da wannan asakala.
Dalilan gaba sun kasance suna daga cikin dalilan da ake riko da su domin ganin an kawo kiyayyar Shi'a da kuma kyamarsu. Don haka ne ma ba za ka ga irin wannan tuhuma ga Shi'a a gun yan Sunna na farko ba sakamakon cewa babu irin wadannan dalilai a can baya a wancan zamani. Kuma wani abin mamaki shi ne: harsunan da suka fi kowa zagin Shi'a a wancan zamani -kafin su kansu Farisawa su zama Shi’a- zaka samu harsuna ne na Farisawa kamar yadda zamu kawo maka nan gaba kadan.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: