bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      10:57:59
Mustashriki Duzi ya na ganin cewa asalin Shi’anci mazhaba ce mai dauke da tunanin Farisanci, wannan kuwa ya kasance sakamakon cewa Larabawa suna rayuwa ne
Lambar Labari: 322
Masu hadafin cimma maslaharsu sakamakon iza wutar wannan lamari suna da yawa sai dai mun samu mustashrikai sun fi karfafawa kan iza wannan wutar, sannan kuma sai muka ga dalibansu masu daukar tunani daga gare su daga musulmi suna buga irin wannan gangar da su ma mustashrikai suke bugawa, wato: suna hura wannan wutar ta kyamar Shi’anci da kuma raba masa Farisanci domin cimma hadafinsu da manufarsu, kana iya duba ra’ayoyinsu kamar haka:
1- Mustashriki Duzi:
Mustashriki Duzi ya na ganin cewa asalin Shi’anci mazhaba ce mai dauke da tunanin Farisanci, wannan kuwa ya kasance sakamakon cewa Larabawa suna rayuwa ne da ‘yanci game da mulki, su kuma Farisawa suna da tunanin mulki da gado, ba su san ma’anar zabe ba, kuma tun da Annabi (S.A.W) ya tafi bai bar mai gado ba, to wanda ya fi kowa cancantar halifanci bayansa shi ne dan amminsa Ali (A.S), (Tarihul mazahibul islamiyya, Abu Zuhra, j 1, shafi: 41).
2- Mustashriki Pan Pulotin:
Wannan ma ya na ganin irin ra’ayin da ya gabata ne, kamar yadda ya kawo a littafinsa na "Siyadatul Arabiyya" sai dai ya na ganin cewa Shi'a sun riki wannan ra'ayi ne daga Yahudawa fiye da yadda suka karba daga Farisawa, da dokokinsu na asali, (Abin da ya gabata).
3- Mustashriki Brawon:
Yana ganin cewa: Ba a riki tunanin cewa jagoranci na Allah ne ba da karfi (Tsakanin musulmi) kamar yadda Farisawa suka rike shi, kuma sai ya yi nuni da cewa Shi'a sun samu wannan ne daga gare su, (Fajarul islam, shafi: 111).
4- Mustashriki Welhozan:
Wannan mustashriki ya na ganin cewa Farisanci ya kunshi wani yanki mai yawa na Shi’anci a cikinsa ta yadda ya ambaci cewa sama da rabin mazauna birnin Kufa na daga wadanda ba Larabawa ba duk Shi'a ne, kuma mafi yawansu Farisawa ne, (Fajarul islam, shafi: 92).
5- Mustashriki Brukle Man:
Yana cewa: Shi’anci ya kasance abu ne da ya hada dukkan jama’ar da take gaba da Larabawa, kuma a yau kabarin Husain (A.S) ya kasance wuri mafi tsarki gun Shi'a musamman farisawan da ba su gushe ba suna ganin zuwa wannan wuri da tarewa a wurin shi ne babban burinsu da suke son cimma sa, (Tarihus shu’ubil islamiyya, shafi: 128). A takaice dai idan mun koma wa bahasin mustashrikai a wannan lamari zamu ga mutane masu yawa daga cikinsu sun tafi a kan wannan ra'ayi saboda wasu dalilai da ba boyayyu ba ne (Ga mai hankali).
Kuma suka fitar da wata natija da suke so sakamakon damfara Shi’anci da Farisanci, kuma wannan sakamakon shi ne: Wato: tunda mafi yawan Farisawa Shi’a ne, kuma ana kiran su ‘yantattun bayi, kuma tun da Larabawa sun kwace musu daularsu, kuma tun da daular Umayyawa tana da tunanin Larabawa ne, sai su wadannan ‘yantattu suka yi kokairn ganin sun kayar da ita, kuma sun kafa daular Abbasawa wacce ta taimaki Farisawa, wacce tunanin Shi’anci ya shige ta kuma ya karfafa a cikinta sakamakon mulkin Abbasawa, kuma kana iya samun wadannan tunani gun mafi girman litattafan wannan zamani na musulunci musaman marubuta misirawa. Don haka muna iya fitar da natija kamar haka:
1- Sawwala kai harin nan na rundunar da ta zo daga Khurasan domin gamawa da daular Umayyawa da cewa na kabilanci ne, ba don al’umma ko mutuntaka ba ne, kuma wai jama’ar da ta taru mai kabilu masu yawa sun taru ne domin kawar da hankula daga hadafin nan da yake boye karkashin wannan harin.
2- Kuma cewa wuta uwar gami a wannan harin su ne Farisawa, domin su kawo hari na daukar fansa da yake son dawo da kima da martabar Farisawa ne wanda Larabawa suka kawar da shi, don haka ne da wannan sai a shafi babbar rawar nan da Larabawa suka taka wajen samun jagoranci.
3- Kasancewar tunanin Shi’anci ya na cikin kwakwalen wadannan makiya da suka ci nasara a lokacin Abbasawa.
Sai dai dukkan wadannan lamura ne da ba su faru ba, kuma ba za a yarda da su ba, kuma kokarin rufe abin da aka kasa tabbatarwa ne kawai.
Dorawa Kan Maganganun Farko
Ra’a yi Na Farko
Wannan ra'ayi bai inganta ba saboda cewa wadanda suka jagoranci mutane sun jagorance su ne domin kubutar da su daga zaluncin Umayyawa, kuma duk wani mai bincike ya na iya duba tarihin abin da ya wakana domin sanin gaskiyar abin da ya faru na halayen hukumomin Umayyawa wanda yake cike da zalunci tun farko har zuwa faduwarsa a lokacin Marwan dan Muhammad karshen sarakunan Banu Umayya, kuma ina ganin kuskure ne ma mukawo misali daya ko biyu a kan hakan domin dukkanin kwanakin hukuncinsu cike suke da zalunci, kuma ina neman mai karatu ya koma ya bi tarihin tun lokacin Mu’awiya na farko har zuwa karshen daular a litattafan da musulmi suka rubuta duka ba na Shi'a ba kawai. Tayiwu a ce Shi'a suna kin Umayyawa kuma suna jin haushinsu ne, amma sai ga litattafan da Dabari da Ibn Asir, da Ibn Kasir, da Ibn Khaldon, da duk abin da ka ga dama ka duba ka ga abin da suka rubuta inda lamarin ya kai ga mawaka suna cewa:
Yakinku dai yakinku dai ya ku alayen Harbu
Ya alayen Harbu daga gare ku yakinku dai
Daga gare ku a cikinku zuwa gare ku da ku
Akwai abin da, da mun fada da mun tozarta litattafai
Amma Ra’a yi Na Biyu
Shi ma ya tabbata cewa karya ne saboda dukkan wadanda suka jagoranci yakin Larabawa ne, kuma Jahiz ya kawo hakan a cikin littafinsa mai Sunan "Manakibul Itra" kuma ya ambaci jagororin yakin kamar: Kahdaba dan Shabib Atta’i, da sulaiman dan Kasir al’khuza’i, da Malik dan Haisam al’khuza’I, da Khalid dan Ibrahim az’zuhaili, da Lahzi dan Darif Almuzni, da Musa dan Ka’abul Muzni, da Kasim dan Mujashi’i Al’muzani, kamar yadda tarihi ya kawo Sunan kabilun Larabawa daban-daban wadanda suke a nan Khurasan wacce ta kasance ta haifar da mafi girma runduran da mafi yawancinsu daga Khuza’a, da Tamim, da Dayyi, da Rabi’a, da Muzaina, da wasunsu na kabilun Larabawa.
Kuma idan kana son ka san sama da haka sai ka duba dukkan jagororin kabilun Larabawa da suka zo domin kawar da hukumar Umayyawa, ka koma zuwa ga littafin Ibnul Fudi marubucin tarihin Iraki na Muhammad Rida Shabibi, ya fadada tarihin daga manyan litattafai kuma ya yi sharhin hadafofin kawo wannan hari da kuma nau’in rundunonin da suka yi tarayya wajen kawo hari da dukkan wasu bayanai, (Mu’arrikhul Iraki, Ibnul Fudi, j 1, shafi: 36, 37).
Bangare na biyu shi ne cewa rundunar da ba Larabawa ba ce ta so ne ta huce haushi da daukar fansa kan Larabawa don ba a ba ta mukamai ba a cikin hukumar Umayyawa wannan ma muna iya cewa ba ingantacce ba ne, domin da yawa daga wadanda suke ba Larabawa ba sun kama matsayoyi da mukamai masu girma a lokacin Umayyawa tun daga farko har karshe, kuma yanayin da suka samu a lokacin Abbasawa ba shi da wani bambancin azo-agani da wanda suke a kai lokacin Umayyawa, kuma Dakta Ahmad Amin ya yi nuni da hakan a cikin fadinsa: Jagorancin Farisawa ya dadu a lokacin Umayyawa musamman ma karshensa, kuma da ba su samu damar kafuwar Abbasawa ba to da sun samu wata damar daban mai wani yanayi da ya fi wancan, (Dhuhal islam, shafi: 3).
Wasu jama’ar da ba Larabawa ba ne sun kama mukamai masu girma: daga cikinsu akwai Sarjun dan Mansur mai bayar da shawara ga Mu’awiya, da kuma shugaban fayel din wasiku, da shugaban haraji, da Muradis Maulan Ziyad wanda yake shugaban wasiku, da Zaza Nafrukh wanda yake jagoran harajin Iraki, da Muhammad dan Yazid maulan Ansar, wanda yake gwamnan Misira karkashin Umar dan Abdul’aziz, da Yazid dan Muslim maulan Sakif wanda yake gwamnan Misira, da kuma wasu alkalai da gwamnoni da manyan jagororin haraji, kuma sun shiga duk wani matsayi na daula da jama’arta da fadadawa, (Al’Imam Sadik, Asad Haidar, j 1, shafi: 344).
Ta wani bangaren kuma yanayin Larabawa ba ya da wani tasiri sai daidai gwargwadon yadda zai iya tabbatar da maslahar Umayyawa ne, kuma idan suka ga ya saba da maslaharsu to sai su gwara kan Larabawa, su buga sashensu da wani sashen kamar yadda ya faru sau da yawa a lokacin jagorancin Umayyawa, (Murujuz Zahab, j 2).  Kuma Dakta Ahmad Amin ya kawo wannan ya na mai sharhinsa dalla-dalla kuma ya na bayyana yadda Larabawa suka rika dukan junansu: bangare-bangare sashe da sashe idan lamarin ya kai ga hakan ne maslaha, (Dhuhal islam, j 1, shafi: 3.).
Amma Ra’a yi Na Uku
Wannan ra'ayi ya na ganin Shi’anci ya yadu ne ta hanyar Mawali (wadanda ba Larabawa ba ne) kuma suka samu martaba da kima saboda haka. To wannan ma karya ne kuma bai inganta ba, domin an kaskantar da Farisawa a lokacin Abbasawa ba sau daya ba, ya na daga cikin lamarin Abu Muslim da mabiyansa a lokacin Mansur da lamarin Baramika lokacin Rashid, da lamarin Ali Sahal lokacin Ma’amun da sauransu. Sai dai a dunkule cewa haka ne mawali sun yi tasiri a wasu fagagen daban, kuma an samu kutsawa da kuma tasirin Farisawa lokacin Saffah zuwa Ma’amun. Kuma wannan ya na nufin babu wani tasiri da yake tabbata ga Farisawa wajen da’irar Abbasawa ta yadda zasu iya sanya su karkashinsu duk sadda suka so. Amma lokacin da Mutawakkil ya fara mulki har zuwa karshen mulkin Abbasawa to Abbasanci ya samu raunana har sai da ya rushe, wannan kuwa ya faru ne sakamakon raunin da wannan hukuma ta samu, kuma masu rubutu sun yi bayanai masu yawa kan dalilan rushewarta.
A bisa hakika abin da ake kawowa na tasirin Mawali a cikin daular abbasiyya ya kasance kambawa ne kawai domin al’ummu ba su samu wata dama mai karfi ba a wannan lokacin sai irin wacce suke da ita a lokacin Umayyawa, kuma idan Farisawa sun samu wani tasiri da samun shiga to bai kai ga yadda zai iya kange samun shigar Larabawa ba, sai dai kawai wani samun wuri da samun shiga ne da su larabawan da kansu suka ba su saboda wasu hadafofi da suke son su cim masu. A kan haka ne ma Falhozan yake cewa: Amma batun samun shigar Farisawa da kama wurinsu kamar yadda yake, ba wani abu ba ne da za a iya tabbatar da shi ba, (Azzandika wasshu’ubiyya, Samir allaisi, shafi: 81).


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: