bayyinaat

Published time: 04 ,December ,2018      11:00:04
Wannan ayar ta koyar mana da taƙiyya tare da iyakance mana ma'anarta cewa imani nada rukunnai uku; ƙudurcewa a zuciya, bayyanawa a harshe da aikin gaɓɓai, wannan shine abinda imani ya hukunta a halin ya kamata na ɗabia
Lambar Labari: 323
TAƘIYYA CIKIN SHARIAR MUSULUNCI
Taƙiyya abar la'akari ce cikin jumlar farkon aiki da al-ƙurani mai girma ya kawo, nassi yazo kan halascinta cikin faɗin sa maɗaukakin sarki: «kada muminai su ɗauki kafirai matsayin majiɓinta maimakon ƴan uwansu muminai duk wanda ya aikata haka ba da yawun Allah cikin wannan, saidai bisa matsayin taƙiyya iya taƙiyya, Allah na muku gargaɗin kan sa makoma na ga Allah» (Suratu A-li Imran, 28).
Da faɗarsa maɗaukakin sarki cewa: «wanda ya kafircewa Allah bayan yayi imani indai ba wanda aka tilastashi zuciyarsa na nutsuwa cikin imani ba duk wanda ya yalwatu da kafirci a ƙirjinsa waɗannan suna tare da fushin Allah, zasu haɗu da azaba mai raɗaɗi» (Suratun Nahl, 106).
Wannan ayar ta koyar mana da taƙiyya tare da iyakance mana ma'anarta cewa imani nada rukunnai uku; ƙudurcewa a zuciya, bayyanawa a harshe da aikin gaɓɓai, wannan shine abinda imani ya hukunta a halin ya kamata na ɗabia.
Yadda cewa musulunci shari'a ce wacce ke duba zuwa waƙi'iyya tare da magance dukkan matsalolin yau da gobe yana daga ɗabi'a buɗewa tare da fayyace dukkan abubuwan da ke kan mukallafai ainihin yadda ake sauke nauyi tare da abubuwan da kan kai su komo na yau da gobe na ɗabi'a da wanda bana ɗabi'a ba, kamar idan mutum ya wayi gari yana mai zaɓi tsakanin mutuwa ko baƙar wahala ko sauka daga wani ra'ayi da ya shafi imani ko wani abu na zahiri, sai wannan aya mai girma tazo don ta fayyace cewa rukunin farko shine ƙudurcewa a zuciya wanda sauka daga matakin da take kai na haƙiƙa ba zai yiyu ba daga ɗayan cikin halaye domin shine asalin imani kuma jauharinsa, ɓoyayyen rukuni ne a kan kansa, amman rukuni na biyu da na uku sai aya ta sauka ga muminai tana mai basu damar rashin bayyana musulunci na wani ayyanannen lokaci idan ya zama zai iya tseratar da rai sannan hakan ba zai kai ga rusa addini ko illatar dashi ba, inda aya ta zo da falalar Ammar ɗan Yasir yayin da mushrikai suka takurashi da zagi Manzon Allah (S.A.W) ya yabi gumaka ya aikata hakan ƙarƙashi baƙar azaba, lokacin da yazo wajen Manzon Allah (S.A.W), Manzon Allah (S.A.W) yace dashi: «me ya sameka?» yace: sarri ya Manzon Allah, basu barni ba har saida na zambaceka na yabi gumakansu da alheri, Manzon Allah (S.A.W) yace: «ya abin yake a zuciyarka?» yace: tana cikin nutsuwa da imani, sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa: «idan goma haka ta ƙara faruwa ka kuma yin hakan (don ka tsira)» (Mustadrak na Hakim 2, 357. Sunan na Ibni Maja 1, 150 babi na 11. Da tafsirin Mawardi 3, 192 bugun Beirut. Tafsirur razi 20, 121 da sauran tafsirai, da wasun waɗannan na daga masadir).
Malaman musulunci na kafa dalili da wannan a matsayin farkon taƙiyya a musulunci da ayoyin da muka ambata suka kawo a sama, Muragi ya sanya wannan a tafsirinsa cikin abubuwan da kansa taƙiyya: takurawar kafirai, zalunci, fasiƙanci, yi musu magana, murmushi a fusakunsu, basu dukiya don gujewa cutarwarsu da kare kai daga manufarsu, Ɗabarani ya fitar da faɗinsa (S.A.W) cewa: «abinda mumini yayi don cinma burinsa sadaƙa ne», (Tafsirin Muragi 3, 136 bugun Egypt)
Ba a la'akari da wannan a matsayin munafuncin da ƙurani ya nuna ba tare da ɗaukarsa mafi tsanani daga kafirci, shi munafunci shine ɓoye kafirci ko ƙiyayya, tare da bayyana imani ko soyayya, amman taƙiyya shine ɓoye imani da bayyana abinda ya saɓa masa, da taƙiyya munafunci ce ta yaya Allah ya halasta ta a matsayin nassi, sannan ya yabi mumini mumini a-li fir'aun ya ambaci aikinsa da aiki mai kyau: «wani mutum daga mutanen Fir'auna yana ɓoye imanin sa ...» (Gafir, 28), ya yabi matar Fir'auna tare da sanyata misali ga waɗanda sukayi imani – ta rayu tare da Fir'auna tare da taƙiyya – cikin ayoyi biyu na littafinsa?
Kamar yadda a lokaci ɗaya taƙiyya ta saɓawa sallamawa wanda akewa ita sallamawa ta haƙiƙa, domin sallamawa shine bin abinda akewa taƙiyyar tare da sauka daga asalin abinda ake tun farko da i'itiƙadi da sabon, ta yadda taƙiyya ke nufin haƙurin ɓoye manufa don a jefar da na biyun, tare da rashin nuna imani da na farkon zuwa wani ɗan lokaci, da bayanar da haƙiƙanin juya baya har zuwa lokacin sa rauni zai kau sai a dawo da na farko, taƙiyya salon gyaran zamantakewa da haƙuri ba tare da sallamawa ba, a bishi saɓanin zahirinsa ta tsayar zahirinsa don gyara alaƙar lahira, don kiyaye shiga cikin mafi girman ƙasƙancin imani, shine duba da ainihin aiki don gyara gaba da canjawa bayan samun damar fita daga wannan ƙangi, ta hanyar fakewa da sallamawa abubuwan da suke zahirin lamari don cinma burin aiki kan fikirar gaskiya wacce itace ta farko.
A wata kalmar taƙiyya na nufin bayyana yarda da yanke ƙauna da cire rai da saranda, ba kuma na nufin rauni ko gazawa bane ga maƙiyi da ya tilasta mumini, domin sanya maƙiyi ya fahimci cewar mumini ya karɓi abunda yake buƙattana taƙiyya na kuɓutar da mumini daga shiga tsaurin zuciya, tana tsallakar da mumini daga wannan hadafi.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: