bayyinaat

Published time: 09 ,December ,2018      12:31:56
Don haka ne tarihi ya rawaito mana cewa; Yahudawa da yawa sun kasance suna kaiwa da komowa a Madina kafin zuwan addinin Musulunci domin jiran bayyanarsa
Lambar Labari: 324
ANNABAWA MAGABATA SUN BADA LABARIN ANNABAWA MASU ZUWA:
Tabbas mun sakankance cewa Annabawa da yawa sun bada labarin zuwan Annabawan da ke bayan su, tabbas Annabi Musa (A.S) da Isa (A.S) sun bada labarin zuwan Annabi Muhammad (SAW) har da bada bishara, domin wasu littattafan su sun qunshi hakan har ya zuwa yau: (Su ne waxanda suke bin Manzo na Ummulqura wanda suka same shi a rubuce a cikin Attaura da Injila, waxannan su ne masu rabauta).( )
Don haka ne tarihi ya rawaito mana cewa; Yahudawa da yawa sun kasance suna kaiwa da komowa a Madina kafin zuwan addinin Musulunci domin jiran bayyanarsa; saboda littattafansu sun bada labarin zuwan sabon addini a cikin wannan qasar mai tsarki, tabbas wasu sun yi imani bayan bayyanar addinin a lokacin da wasu suka yi tawaye kuma suke ganin ci bayan su ya zo.

ANNABAWA DA GYARAN AL’AMURAN RAYUWA:
Lallai mun qudurce cewa addinan da Allah ya saukarwa da Annabawa, musamman addinin Musulunci, ba fa wai kawai sun zo ne domin gyaran rayuwar xai-xaikun mutane ba ne kawai, ba su kevanta ba a cikin wasu al’amura da gyaran xabi’u ba kawai, su waxannan addinan suna yunqurin gyara al’amuran duniya ne gaba xaya, haqiqa mutane da yawa sun koyi wasu ilumummukan rayuwar yau da kullum daga wajen Annabawa, wanda wannan shi ne abin da wasu ayoyin Qur’ani suka nuna.
Mun gamsu da cewa tsayar da adalci shi ne babbar manufar Annabawa a cikin al’umarsu: (Tabbas mun aiko Manzanni da hujjoji, sannan mun saukar musu da littafi da ma’auni domin mutane su tsaida adalci).( )

WATSI DA QABILANCI:
Tabbas mun qudurce cewa Annabawa (AS) musamman Annabi Muhammad (SAW) sun kasance suna watsi da qabilanci da fifita dangi, suna yiwa mutane gaba xaya kallon abu xaya, duk da cewa sun banbanta a yare da jinsi; littafin Allah mai girma yana yiwa dangogin mutane magana: (Ya ku mutane! Haqiqa mun halicce ku maza da mata, kuma mun sanya ku dangogi da qabilu don ku san junan ku, haqiqa fiyayyen ku a wajen Allah shi ne wanda ya fi tsoron Allah).( )
An rawaito a wani sanannen hadisi, an karvo daga Manzon Allah (SAW) yayin da yake magana a Mina lokacin aikin Hajj mutane kewaye da shi: "Ya ku mutane! Haqiqa Ubangijin ku xaya ne, mahaifin ku ma xaya ne. babu fifiko ga balarabe akan ajami, babu fifiko ga wanda ba balarabe ba akan balarabe, haka nan ma baqi bai fi fari ba, kamar yadda fari bai fi baqi ba sai dai wanda ya fi tsoron Allah. Shin na isar da saqo?”, sai suka ce: Qwarai, sai ya ce: "Wanda ya ji ya isar da saqon ga wanda bai ji ba”.( )

MUSULUNCI DA FIXIRAR XAN’ADAM:
Tabbas mun qudurce cewa tsiron iri na imani da Allah da tauhidi da koyarwar Annabawa tabbataccen abu ne tare da kowane mutum, Annabawa ne suka shayar da su da ruwan wahayi kuma suka nisantar da su daga cutarwar shrika da lalacewa: (Fixirar Allah wacce ya halicci mutanen a kanta babu sauyi gamew da fixirar Allah wannan shi ne Addini madai-daici sai dai mafi yawan mutane ba su sani ba).( )
Saboda haka, mutum tun asalinsa yana tare da addini, amma tunanin rashin addi daga baya ya zo kamar yadda malaman tarihi suka faxa - lallai an gane cewa duk vangaren da aka takura masa dan ya bar addini, to da zarar ya sami sararawa zai dawo ya yi riqo da addininsa, a nan ba zai yiwu mu yi musun cewa lalacewar wayewar magabata ce ta jawo gurvatar tunanin addini har ya cuxanya da qaryace-qaryace a wajen mutanen ba, Annabawa sun kasance suna bada gudunmawa mai muhimmanci don a kawar da qaryace-qaryace daga addini da kuma tabbatar da tauhidi wanda hankali ya amince da shi.

QUR’ANI DA SAURAN
LITTATTAFAI
(24): HIKIMAR SAUKAR DA LITTATTAFAI:
Haqiqa mun qudurce Allah (SWT) ya saukar da littattafai daga sama masu yawa saboda mutane su sami shiriya, akwai suhufu Ibrahim, Nuhu da Attaura da Injila, Qur’ani mai girma shi ne ya fi tattaro abubuwa, da waxannan littattafan da ba’a saukar da su ba da mutum ya kuskurewa hanyar sanin Allah da ibadarsa, da mutum bai gane tushen taqwa ba da xabi’un da tarbiyya kai harma da dokokin zaman takewa waxanda al’umma take buqata.
Tabbas waxannan littattafan an saukar da su ne domin rahama ga zukata, kuma sun haifar da irin taqawa da gyaran tarbiyya da ma sanin Allah da ilimi da hikima: (Manzon Allah ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa haka ma muminai duk sun yi imani da Allah da Mala’ikunsa da littattafansa da Manzanninsa).( )
Sai dai abin baqin ciki an canja da yawa daga cikin waxannan littattafai ta hanyar amfani da jahilai da masu mugun nufi, an shigar da abubuwa marasa kyau, sai dai littafin Allah wato Qur’ani masu canjawa sun kasa, saboda wasu dailai masu zuwa, har ya zamana ya wanzu kamar rana maxaukakiya yana haskaka zukata a kowanne zamani: (Tabbas haske daga wajen Allah ya zo muku kai har ma da littafi mai bayyanawa, Allah yana shiryar da wanda ya nemi yardar sa ga tafarkin aminci).( )

QUR’ANI SHI NE BABBAR MU’UJIZAR ANNABI MOHD (SAW):
Tabbas mun sakankance cewa Qur’ani shi ne mafi girman mu’ujizar Manzon Allah (SAW), ba wai don saboda balagar da ke cikinsa ba da faraha da cikar ma’anoninsa ba kawai, ai don saboda ya qunshi mu’ujizozi mabanbanta waxanda sharhinsu ya zo a littattafan aqida da ilmul kalam.
Don haka ne ba zai yiwu ga wani ya qirqiro irinsa ba ko ya zo da sura irinta Qur’ani ba, haqiqa Qur’ani ya gajiyar da wanda yake kokwantonsa a cikin ayoyi da yawa ta hanyar cewa ya zo da sura ko aya, kuma duk sun kasa: (Kace idan mutane da aljanu za su taru don su qago irin Qure’ani ba za su iya qago irinsa ba ko da suna taimakawa junansu).( )
(Idan kuna kokwanton abin da muka saukarwa bawan mu to ku kawo sura irin ta Qur’ani kuma ku kira masu yi muku sheda in kun kasance masu gaskiya).( )
Mun sallama cewa Qur’ani baya tsufa saboda tafiyar zamani, aima mu’ujizancin Qur’ani qara bayyana yake sannan girmansa yana fitowa fili.
Lallai hadisi ya zo daga Imam Ja’afarussadiq (A.S) ya ce: "Haqiqa Allah (T.W.T) bain sanya Qur’ani a wani zamani ba banda wani zamani ko ace na wasu ne ba na wasu ba ne; Qur’ani a kowanne zamani sabo ne kuma a wajen kowanne mutane sabo ne har zuwa gobe qiyama”.( )

QUR’ANI BAYA CANJAWA:
Lallai mun qudurce cewa Qur’anin da yake hannun mutane wato Musulmai shi ne haqiqanin Qur’anin da aka saukarwa da Sayyadin Muhammad (SAW), ba daxi ba ragi.
Tun farkon saukarsa marubata suke rubuta shi, a lokacin da Musulmai aka wajabta musu karatun ayoyin da suka sauka cikin dare da rana, haka ma a sallolin su biyar na yau da kullum. Saboda haka new wasu da yawa suka haddace shi; haqiqa mahaddata Qur’ani da makaranta suna da daraja ta musamman a cikin al’umar Musulmi; waxanda abubuwan da wasunsu su suka jawo rashin canjawar sa daga canjawar mai canjawa da mai gayyarawa. Bugu-da-qari, Allah (SWT) ya xauki nauyin kare shi har zuwa abada, saboda haka ba za’a iya canja shi ba: (Lallai mu muka saukar da Qur’ani kuma mune masu kiyaye shi).( )
Manyan malamai da masu bincike na shi’a da sunna sun haxu a kan cewa Qur’ani ba’a tava canjashi ba, ba waxanda suka yi da’awar canja Qur’ani sai ‘yan kaxan daga vangare biyun nan saboda dogaron su akan wasu ruwayoyin da malamai sukae ganin cewa riwayoyi ne ko dai su zama na qarya ko kuma riwayoyin suna fassara Qur’ani ne fassarar kuskure, ko kuma suna ganin masu da’awar cewa an canja Qur’ani sun cakuxa tsakanin tafsiri da nassin Qur’ani. A kula da wannan bayanin.
Haqiqa masu taqaitaccen tunani waxanda suke danganta aqidar canja Qur’ani ga ‘yan Shi’a ko wasunsu, to fa wannan maganar manyan malaman Shi’a da na Sunna sun koreta, waxancan masu taqaitaccen tunanin suna jawowa Qur’ani suka tare da jawo kokwanto a kan ingancin wannan littafin mai girma, kuma suna yiwa maqiya aiki da masu san ruguza addinin Mwusulunci.
Idan aka dubi tarihin haxa Qur’ani tun lokacin Annabi (SAW) da kuma himmantuwar da Musulmi suka yi don rubuta shi da kiyaye shi tare da karanta shi, bugu da qari ga marubuta wahayi tun farkon saukarsa, hakan yana nuni akan cewa ba wani wanda zai iya canja Qur’ani har abada.
Kamar yadda ya ke babu wani Qur’anin ‘yan Shi’a sai dai Qur’anin da Musulmai ke amfani da shi, ba abu ne mai wahala ba a iya tabbatar da haka; domin Qur’ani ya cika gidajen mu da masallatanmu kai har da laburori, haka nan ma gidajen ajiye kayan tarihi suna ajiye da kwafin Qur’ani tun na tuntuni, duk waxannan kwafi-kwafin Qur’anin iri xaya new ba qari ballantana ragi, idan tabbatarda haka nada wahala a baya to a yanzu abu ne mai sauqi, duk wanda ya bibiyi wannan maganar zai gano gaskiyar lamarin cewa qarya ce aka qirqiro ta: (Ka yi bishara ga bayina waxanda suke jin magana suke bin mafi kyawun ta).( )
A yanzu haka ana karatar da mutane ilumummukan da suka shafi Qur’ani (ulumul Qur’ani) a faxaxe a cikin hauzozin ilimi, kuma wannan fannin yana yin tsokaci a kan tahriful Qur’an.( )

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: