bayyinaat

Published time: 09 ,December ,2018      12:49:27
MATAKAN ZABAN ABOKAN ZAMA A nan zamu xauki kowane xaya daga cikin su mu yi bayani a taqaice kuma mu kawo mahangar musulunci a kan haka, don musulunci ya bawa namiji dama ya nemi mace
Lambar Labari: 327
Bincike da tacewa wajan  zaven abokin zama, yana taimakawa wajan rage matsalolin da kan iya faruwa bayan an yi aure, sabida haka a bisa kowane hali bai kamata ba ga namiji da mace su yi wasa da zaven abokin zama.
Zavin abokin zama na da ma'auni, a nan kuma mun kasa shi zuwa gida uku :
1-    Kaso na farko ya qunshi sharuxxa da ake nema daga namiji a mace.
2-    Sharaxi na biyu ya qunshi abinda ake buqata daga wajan namijin shi kaxai.
3-    Na uku kuma ya kevanta ga mace ita kaxai.
A nan zamu xauki kowane xaya daga cikin su mu yi bayani a taqaice kuma mu kawo mahangar musulunci a kan haka, don musulunci ya bawa namiji dama ya nemi mace, sai dai kawai tushe da tsarin yin hakan waxanda wajibi ne a kula da su.


DALILAN DA SUKA SA DOLE A YI BINCIKE DA TACEWA WAJAN ZAVAR ABOKAN ZAMA.
Haqiqa aure da kafa iyali abu ne mai girma, saboda haka dole ne a yi bincike da tabbatarwa, misali : mutum zai je kasuwa don neman yadin da zai xinka ya sa kuma yana son wanda zai daxe, kaga yana buqatar yadi mai qwari da nagarta da kyau har ma ya samu masana yadi ya tambaye su, su bashi shawara kan yadin da ya kamata ya xinka.
To idan mutum ya xauki ra'ayin waxanda suka bashi shawara a kan siyan yadi, ya kuma batun neman aure da kafa iyali? A nan zamu kawo muhimman abubuwa waxanda ya wajaba a lura da su wajan zavar abokin zama.

1-     HANKALI DA ADDINI
Yana daga abinda ya zama dole kafin a qulla aure a tabbatar da shi, shine hankali da addinin wadda za a zava.
Wani mutum ya zo wajan imam Sadiq (AS) ya ce masa haqiqa mata ta ta halaka na samu dacewa a kan na yi aure, sai Imam (AS) ya ce masa : "kula da inda zaka sa kanka ka kula da wanda zaka yi taraiyya da shi a kan dukiyar ka, ka yi tsinkaye da shi a bisa addinin ka da sirrin ka, idan ya zama ba makawa sai kayi auren to ka auri budurwa,  domin tafi dacewa da al'khairi da kyakykyawan hali, su (mata) kala uku ne, mace mai haihuwa mai soyayya tana taimakon mijin ta kan zamanin sa, duniyar sa da lahirar sa, bata taimakon zamani a kan sa, mace mara haihuwa kuwa, marar kyau da hali, bata taimakon mijin ta a kan al'khairi, da mace mai wadatuwa da mai yawa bata karvar kaxan)1
Haqiqa qulla alaqar aure da kafa iyali  ba tare da lura da aqida  da tunanin juna ba, da rashin kula da wasu siffofi na zahiri, kamar : cikakken hankali da kyawawan xabi'u yana haifar da matsala, gajiyarwa ga ma'aurata wanda bazasu magantu ba.
2-    CUXANYA
Abokin zama shine abokin rayuwa wanda za a rayu da shi ana cakuxa da juna, idan ya zama an yi rashin sa'a da dacewa da shi  abokin rayuwa to za a qarar da rayuwa cikin qunci, raxaxi da haquri.
Manzon Rahama (SAW) na cewa : " ita mummunar mace na tsufarwa kafin tsufa"  saboda haka yake faxa cikin addu'ar sa "Allah ina mai neman tsarin ka daga matar da ke tsufarwa kafin tsufa"1.
3-    NEMAN TAIMAKON ALLAH
Akwai muhimman abubuwa masu tasiri kan halaiyyar ma'aurata wajan qulla aure da kafa iyali, bayan an kula da hankali da addini sai a nemi taimakon Allah.
Akwai salla da addu'a da ake yi kan haka, za a yi salla raka'a biyu, bayan an idar da sallar  a yi godiya ga Allah da yabo a gareshi, sannan a karanta wannan addu'ar    " أللهم إنى أريد أن أتزوج   " ga yadda take a hausar boko " Allahumma inni uridu an atazawwaja, Allahumma fa qaddir li¬ minannisa'i ahsanu hunna khalqan wa khulqan, wa affa hunna farjan, wa ahfazuhunna li fi nafsiha, wa mali wa ausa'u hunna rizqan, wa'a a' zamuhunna barakatan, wa qaiyyad li min ha waladan, xaiyyiban, tajaluhu li khalfan salian, fi haiyyin wa ba a du mauty"2.
Da waxannan abubuwan da zamu ambata mu lura da su da basira, da so, hankali dafatan taimakon Allah, da dogaro da shi, da wannan ne za a toshe kuskure, a samu dacewa da jin daxi.
4-    'YANCI DA ZAVI
Dole ne mace da namij su zamto 'yantattu wajan zavin abokin zama, ba wanda yake da haqqin zavar miji ko mata ga wani, idan ba da yardar sa ba ko ya tilasta a zavar masa, koda kuwa mahaifa ne (uwa ko uba).
Dole ne mu yi magana a kan wanna domin wani lokaci iyaye na shiga lamarin auren 'ya'yan su ba tare da yardar su ba, wani lokacin ma sukan xauki mataki da hankali ba zai yarda da su ba ballantana shar'a.
Haqiqa tilastawa saurayi ko budurwa a kan wanda basa so ana xaukar sa zunubi, kai idan ma suka qi yarda auren bai qullu ba, haka kuma bai halatta a karvi yardar budurwa da qarfi ba, kamar : tilastawa, duka ko azabtarwa a kan auren wanda bata so.
5-    XAUKAN RA'AYIN IYAYE WAJAN ZAVAN ABOKIN ZAMA
Ya kamata ga saurayi ko budurwa su xauki shawara, nunarwa ko ra'ayin iyayen su a kan al'amarin auren su, saboda su amfana da qwarewar iyayen su wajan sanin al'amuran rayuwa.
Abinda ya fi muhimmanci ga matasa su sani shine, iyayen su suna tunani ne game da abinda yake al'khairi ne da jin daxi ga 'yayan su, sai dai akwai yiyuwar su iya kuskure a kan tunanin nasu, wannan kuskuren ba da gangan bane, sabida haka ya zama wajibi ta kowane hali a lura da matsayin su a kuma girmama su, domin sun tarbiyyantu a kan lamarin aure.
Manufa  a nan shine samari da 'yan mata, su kasance masu xaukar lamarin iyaye da hangen su, a bisa waxanda zasu zava a matsayin abokan rayuwa na aure.
6-    LURA DA ZURIA TA QWARAI
Kula da zuri'ar kwarai da sanin asali da tarihin zuria yana da muhiummancin gaske wajan kafa iyali, domin idan baka san zuri'ar mutum ba sosai aka qulla alaqar aure ba a cika dacewa ba, saboda haka musulunci ya yi wasiyya da cewa zuri'ar da ake so a qulla alaqar aure da ita ta kasance kamila  tsarkakakkiya, mutuntacciya ta hanyar hankali, tsari da mutunci a tushen ta, kai har ma da aqidar ta, domin waxannan  abubuwan na da tasiri wajan ginin sabuwaer al'umma.
Saboda cakuxay maniyyin uwa da uba, wanda shine farko wajan samuwar jariri, idan ya kasance ba nagartacce ba galibi yana tasiri a kan 'ya'yan da za a haifa da wannan maniyyi.
Manzon Rahama (SAW) ya ce : "ku auri 'yar kyakykyawan xaki haqiqa jijiya na bin jijiya" .
Wannan abu da malamai suka tabbatar mana domin ana gadon varna da cututtuka daga iyaye da kakanni, waxanda ke curuwa zuwa 'ya'yan su, wanna al'amari ba wai yana curuwa bane ga ma'aurata kawai har ma ga al'umma.
Ta wani vangaren kuma musulunci ya yi wasiyya kan tsarkake zuri'a, wani mutum ya zo wajan Imam Sadiq (AS) ya tambaye shi cewa : (amman xanta ba zai auri 'yar zina ba)1, ma'ana xan zina ba zai auri 'yar zina ba.
7-    IMANI DA TSORON ALLAH
Imani da tsoron Allah, in ya haxu tsakanin ma'aurata to an fi shaquwa da juna, duk iyalin da suka kasance an samu raunin imani da taqawa ana samun raunin tarbiyyantarwa, da bada tarbiyya sahihiya, koda kuwa suna da wadata da arziqi, kyakykyawar soyayya da tsarkaka da aka samu sakamako kyawawan xabi'u da halaiyyar kwarai suna daga sharaxi na asali ga rayuwar aure da ma'aurata.
A cikin wasiyyar Amirul Muminin Ali Xan Abi Xalib (AS) ga wani mutum da ya nemi shawarar sa a kan mace ma'abociyar addini da imani sai ya ce : "idan ka nutsuda haka to ka aura"2.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: