bayyinaat

Published time: 02 ,February ,2017      07:55:45
An yi amfani da wasu ruwayoyi domin nuni da cewa; dole ne mu kawo mutane masu yawan gaske a wannan duniya ko da kuwa ba mu dauki wani mataki kan hakan ba lamarin da suke ganin yana nuni da rashin halaccin kaiyade iyali. An yawaita amfani da hadisan da idan muka duba babu ko daya daga cikinsu da yake hana kaiyade iyali da tsara su ko da a matsayin karahiya balle kuma ya kai matakin haram, maimakon haka ma sai dai akwai hadisai da muke da su wadanda kai tsaye suke halatta kaiyade iyali da tsara su.
Lambar Labari: 33
An yi amfani da wasu ruwayoyi domin nuni da cewa; dole ne mu kawo mutane masu yawan gaske a wannan duniya ko da kuwa ba mu dauki wani mataki kan hakan ba lamarin da suke ganin yana nuni da rashin halaccin kaiyade iyali. An yawaita amfani da hadisan da idan muka duba babu ko daya daga cikinsu da yake hana kaiyade iyali da tsara su ko da a matsayin karahiya balle kuma ya kai matakin haram, maimakon haka ma sai dai akwai hadisai da muke da su wadanda kai tsaye suke halatta kaiyade iyali da tsara su. 
1- "Ku yi aurataiya kwa hayaiyafa, hakika ni ina yi wa al’umma alfahari da ku ranar kiyama" . Idan muka duba wannan hadisin zamu ga yana da bangarori masu dadin gaske kamar cewa "Ku yi aur ataiya kwa hayaiyafa, hakika ni ina yi wa al’umma alfahari da ku ranar kiyama . Da farko dai kalmar "Ku yi aurataiya kwa hayaiyafa” tana nuna mana aure ana yin sa ne tsakanin mutum biyu, ba ya kasancewa sai da yarda bangaren namiji da mace, don haka sai ya zo da kalmar taraiya da aikin da yake daga bangarori biyu a larbci تناكحوا ku yi aurataiya, ko da yake ana iya cewa yana nufin ku yi aure wato ku biyu ke nan miji da mata, bisa yardar juna ba tare da yi wa wani bangare tilas ba. Sannan a wannan ruwayar babu wani abu da yake nuna ana nufin a auri mata da yawa kamar yadda wasu suke nuna cewa wai ana nufin; A yi ta yin auren mata da yawa ana kawo ‘ya’ya barkatai ko da kuwa babu wani abu da zai iya na daukar nauyin rayuwarsu!. 
Sannan fadinsa ma’aiki "Ku yi aurataiya” yin aure a nan umarni ne na mustahabbi kamar yadda malamai suka yi nuni da shi, kuma aikatau ne na umarni a ka’idar nahawun larabci wanda a Hausa yake bayar da umarni, don haka ne a hausa muke fassara shi da umarni domin ma’anarsa ke nan. Amma bangaren wannan jumala mai cewa; "kwa hayaiyafa”, yana nuna mana dalilin yin auren ke nan. Kamar yadda zaka ce da wani mutum ne, ka yi kasuwanci ka samu riba, ko ka yi karatu ka samu ilimi, wanda yake nuna sai an yi wadannan aiyukan sannan ake iya samun natija wato bangaren karshe. 
Don haka hadisin yana nuna mana idan muna son haihuwa da hayaiyafa to sai mu yi aure, amma idan ba ma son mu hayaiyafa to ba zamu yi auren ba. Sai dai ma’aiki mai daraja ya kwadaitar da yin auren domin da shi ne zai yi alfahari ga sauran al’ummu. Domin idan hayaiyafa ta kasance ta tsaya cik, ko kuma idan hayaiyafa ta hanyar fasadi ne kamar zina, to babu wani abu da zai yi wa sauran al’umma alfahari da shi. 
Amma fakarar da take cewa: "Hakika ni ina yi wa al’umma alfahari da ku ranar kiyama”, wannan fakarar tana nuna mana dalili na biyu na yin aure wanda yake nuna cewa; idan kuka yi aure kuka hayaiyafa to zan yi alfahari da ku ke nan. Wannan yana nuni da cewa; idan kuwa ba ku yi aure kuka hayaiyafa ba to babu wani abu da zai yi wa wasu al’umma alfahari da shi na salihan bayin al’ummata, domin samuwarku ta katse ke nan. Sannan alfahari yana yiwuwa ne idan akwai abin da za a nuna na azo-agani kamar salihan bayi da babu kamarsu a cikin wata al’umma, don haka wannan yana nuna cewa idan taci-barkatai ne wannan al’ummar take kyankyasowa take hayaiyafarwa babu wani abin alheri da za a iya yin alfahari da shi!. 
Masu kafa hujja da wannan hadisin don su nuna rashin halaccin kaiyade iyali ko kusa ba su dace ba idan muka duba ma'anarsa a fili. Don haka babu wani abu a cikin da yake nuni da rashin halaccin kaiyade iyali sai dai nuni da cewa yin aure da kawo zuriya wani abu ne wanda yake mustahabbi a shari'a. 
2- An sake amfani da ruwayar nan da take cewa "Babu wani abu da ya fi soyuwa wurin Allah madaukaki a musulunci fiye da gidan da ake raya shi da aure, kuma babu wani abu da ya fi kiyuwa gun Allah madaukaki a musulunci fiye da gidan da yake rushewa saboda saki” . 
Masu kafa dalili kan kin kaiyade iyali suna son cewa ne tun da ana son raya gida da aure kuma ana kin saki ya faru a ckinsa to babu wani amfani a yi aure sai bayar da damar samuwar 'ya'ya, kuma kange faruwar hakan ke nan bai dace da raya gida da aure ba. Sai dai wannan ruwayar ma tana koma wa abin da muka kawo a ta farko kan cewa tana kwadaitar da yin aure ne a matsayin wani lamari da Allah madaukaki yake son sa, da saki kuma a matsayin lamarin da Allah mai girma da daukaka yake kin sa. 
Masu dogaro da ruwaya ba su iya samun ruwaya daya ba kai tsaye da take iya haramta ko ma hanawa ko da karhantawa ne ga kaiyade iyali da tsara su, lamarin da yake nuna mana cewa shari'a ta halatta yin sa. Ba a samu wani abu kan lamarin kaiyade iyali ba sai akasin abin da suke son tabbatarwa yayin da a fili muka samu ruwayoyi masu nuni da yin azalu tun lokacin mai shari'a mai tsira da aminci ba tare da hana wani mutum yin hakan ba. Muna iya koma wa ruwayoyin mu ga duk abin da suka kunsa bai wuce kwadaitar da yin aure ba kawai. 
3- Ruwayoyi ne kamar mai fadin cewa; "Kaskantattun matattunku su ne marasa aure” . Da ruwayar: "Babu wani amfani da mutum zai samu bayan musulunci da ya fi mata musulma da take faranta masa rai idan ya kalle ta, take biyaiya gare shi idan ya umarce ta, take kare mutuncinsa ga kanta, da dukiyarsa idan ba ya nan” . Amma idan ana neman ruwayoyi masu halatta kaiyade iyali to ana iya samun su kai tsaye kamar fadin nan na Imam Ali (a.s) wanda da takobinsa ne musulunci ya tsayu kuma kofar birnin ilimin Annabi (s.a.w) yayin da yake cewa: "Karancin Iyali dayan Yalwa ne guda biyu . A nan a fili yake cewa Imam Ali (a.s) yana nuni da cewa wanda ya fi karancin iyali nauyin da yake kansa zai fi raguwa, kuma wannan yana nufin zai fi samun yalwar iya tattalinsu da kula da su fiye da wanda ya tara su birjik ba shi da yalwa. Sai dai mu gane cewa wannan lamari yana da alaka da yanayin mutane da bambancinsu ta fuskacin iko da yalawa, ta yadda wani yana iya kula da 2, wani kuwa 5, wani kuwa 12, wani sama da hakan. Don haka zamu iya fahimtar cewa Allah madaukaki ya dora lamurran wannan duniyar bisa sabubba da dalilai ne, ba ya yin wani abu bisa wasa, ba ya wani aiki sai da hikima, Allah Ka girmama Mai Hikima!. 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: