bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      20:52:53
Bayan haka tabbas Allah maxaukakin sarki bai halicci wannan duniya don wasa ba
Lambar Labari: 332
WANE NE HALIFAN ANNABI (S.A.W)?
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ake ga ne shi idan anyi duba zuwa ga halittunsa, wanda ikonsa da iliminsa ke hukunta rashin gajiyawarsa, wanda ya girmama daga masu siffantashi zuwa ga jiki, wanda ya girmama daga naqasa ko wace iri, wanda yake gigitar da masu tunani a kansa, wanda idanuwa basa iya riskarsa, muna gode masa godiya irin ta bayi managarta, muna godiya akan ni’imominsa wanxanda basu da iyaka, muna gode masa a kowanne  hali.
Tsira da aminci su qara tabbata ga Annabinsa Muhammad (s.a.w) ma’abocin ayoyi da bayanai cikakku wanda ya tabbata akan hanyarsa da shari’arsa cikin kamala, da kuma iyalen idansa masu shiryarwa daga vata zuwa gaskiya, waxanda Allah ya tsarkake su daga dukkan datti tsarkakewa, ya Allah kayi salati garesu har ya zuwa ranar sakamako.
     Bayan haka tabbas Allah maxaukakin sarki bai halicci wannan duniya don wasa ba, balantana ya kasance daga cikin masu wasa, sai dai abin sani yayi halitta ne saboda gayar hikima tabbatacciya ga masu tunani kuma ya yi bayani akan haka a cikin littafinsa mai tsarki, inda yake cewa: {{ وماخلقت الجن والانس الا ليعبدون }{ Ban halicci Mutum da Aljani ba sai don su bauta mini}(1) .
    Sai dai karan bani gigiwa da rashin sanin maslaha irin ta Mutane tasa mun shiga wani  abu daban savanin haqiqar manufar halittar mu, haka kuma mutum ya kasa gane Ubangijinsa da yayi masa ni’ima balantana ya gode masa akan ni’imar da yayi masa, mai makon haka ma sai ya jefa kansa cikin halaka. Daga cikin abu mafi wahala a rayuwar xan Adam shine karvar gaskiya wacce a mafi yawan lokuta maslahar rayuwarsa ce .
   Xaya daga cikin mas’ala dake sa kai ruwa rana a tsakanin al’ummar musulmi a lokuta daban-daban ita ce mas’alar khalifanci bayan Annabi, haqiqa al’ummar musulmi sunada savani sosai akan wannan batu na halifanci bayan Manzon Allah (s.a.w), kamar cewa: shin wane ne Halifan Annabi? A wannan rubutun zamu kalli wannan mas’ala da kyau don gane haqiqanin gaskiyar wannan magana tsakanin vangarorin al’ummar musulmi, zamu duba muga shin wa ya kama ta ya zama Halifan Annabi?  Zamu nemo dalilai na hankali da na ruwaya akan wannan batu. Kuma  bana nufin sava kowa akan abin da nake kiran ku zuwa gareshi, bana nufin komai face gyara gwargwadon damar da na samu. Bana neman da cewa ga kowa sai ga Allah, A gare shi na dogara kuma zuwa gare shi na ke tawakkali.
                   ALI NE HALIFA BAYAN ANNABI (S.A.W).
                     Dalili na hankali a kan halifancin Aliyu (a.s).
        Wani abu  da dukkan mutum mai hankali zai iya  hukuntawa shine, a duk lokacin da wata ma’asla ta ta so, ana neman wanda yafi sani yake kuma da tajjiriba akan abu, misali kamar mara lafiya yana neman  likitan da yake qwararren ne a kan sauran likituci wanda yake da qwarewa sosai, ba yanda za a yi yana kallon qwararren likita sai ya barshi  ya tafi wajen wanda bai kai shi qwarewa ba, wannan ya sava wa aikin mai hankali a ko ina. A wani bayanin na daban kuma zamu iya cewa: dole ne a gabatar da wanda yake da fifiko akan komai domin gabatar da wanda bai kai shi ba wannan rashin hankali ne.
       Yadda qur’ani ya gabatar da ma’abocin falala akan wanda bai kai shi ba. Wannan bato yazo a qur’ani dama ruwayoyi misali ga wannan ayar da take cewa:
         { أفمن يهدي الي الحق أحق أن يتبع أم من لايهدي الا أن يهدى فمالكم كيف تحكمون  }
{{ Shin wanda yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi shi, ko kuwa wanda baya shiryarwa face dai shi a ke shiryarwa? To minen a gare ku yaya kuke yin hukunci?}}(1) .
   Ko kuma wannan ayar mai girma da ke cewa: {{ Shin waxanda suka sani zasu yi dai dai da waxanda basu sani ba. {هل يستوى الذين يعملون والذين لا يعلمون}.
  Da kuma ruwayoyin da suke nuni a bisa gabatar da wanda yafi falala:
        A littattafan shi’a da sunna akwai ruwayoyi da daman gaske da suke nuni akan gabatar da ma’abocin falala, misali ga wata ruwaya da ibnu Abbas ya naqalto:
{ من ولي من المسلمين شيئا من أمورالمسلمين وهو يعلم أن فى المسلمين من هو خير للمسلمين منه, فقد خان الله ورسوله وخان جماعةالمسلمين }(3) .
(( Duk wanda ya jagoranci musulmai wani abu daga cikin al’amuran musulmai alhali tabbas yasan cewa daga cikin musulmai akwai wanda yafi shi alkairi ga wannan abun, haqiqa ya ha’inci Allah da Manzonsa ya kuma ha’inci al’ummar musulmai)).
     FIFIKON IMAM ALI (A.S) A KAN SAURAN SAHABBAI.
          Idan muka ce zamu  kawu siffofin Imam Ali (a.s) tufa sauran sahabbai zasu zamo fanko waxanda suka gaza, sannan zamu gane cewa tabbas Ali (a.s) shi ne ya cancanci jagorantar al’ummar musulmai bayan Annabi (s.a.w), saboda haka a nan zamu kawu wasu daga cikin siffofin Imam xin waxanda a hankalce zasu tabbatar mana da cancantar sa wajen al’amuran musulmai.
    Na farko: Ilimin Ali (a.s)
   Dangane da ilimin Imam Ali (a.s) ga wasu daga cikin hadisai mutawatirai da wasu daga cikin littattafan Sunna suka ruwaito: An naqalto daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ( Ni ne Birnin ilimi Aliyu kuma qofarsa duk wanda yake son ilimi to yazo ta qofar shi)
                         [ أنامدينة العلم وعلي بابها فمن أرادالعلم فليأت من بابها](4) .
Ibnu Abbas yana cewa: haqiqa kaso casa’in (90) cikin dari 100 na ilimi (90% ) an bawa Ali (a.s) ne, kaso goma 10%  kuma sauran mutane, ina rantsuwa da Allah tabbas Aliyu ya yi tarayya da sauran mutane a cikin  kaso goman.
Da kuma dai wata ruwayar duk dai daga Ibn Abbas xin ya ce: ( Ilimi na da ilimin Sahabban Annabi idan aka haxa su da ilimin Ali  kwatan kwacin xugo  ne daga cikin Tekuna bakwai.
 [ لقد أوتي علي تسعة أعشارالعلم, و أيم الله لقد شار كهم فى العشر العاشر](5) .من ابن عباس قال :  وأيضا[ وما علمي وعلم اصحاب محمد فى علم علي الا كقطرة فى سبعة ابحر ](6) .
    Haka ma xaya daga cikin matan Manzon Allah (s.a.w) ta yi shaida a kan ilimin Ali (a.s), (A’isha) ta ce: { Aliyu ne mafi sanin mutane Sunna}{ علي أعلم الناس بالسنة}(7) .
    Sa’id xan Musaiyab yana cewa: {  Babu wani daga cikin Sahabbai da ya ke cewa ku tamyeni sai Aliyu bn Abi Xalib (a.s).
               { لم يكن أحد من الصحابة يقول سلوني الا علي ابن ابى طالب (ع)}(8) .
     Tabbas ilimin Aliyu bn Abi Xalib sannan abu ne a tsakanin Sahabban Manzon Allah (s.a.w) wanda baya buqatuwa zuwa yin wani sharhi ko qarin bayani ta yanda a gurare da daman gaske Aliyu (a.s) ya warware matsalolin halifufi da man gaske ta yadda wasu daga cikin ruwayoyin Ahlussunna suka tabbar da cewa sama da sau saba’in 70 aka na qalto wannan jumala daga bakin halifa na biyu inda yake cewa:{ لولا علي لهلك عمر}( Ba don Ali ba da Umar ya halaka)(9) .  Da kuma sananniyar magnarsa cewa: ( Ina neman tsari ga Allah  kada yasa a bijiro min da wata tambaya mai wahala Baban Hasan baya nan(10) . {اعوذ بالله من معضلة ليس لها ابوالحسن }.
        Wannan jumala ta Umar tana tabbatar da cewa Aliyu bn Abi Xalib shi ne wanda yafi dukkan Sahabban Annabi ilimi.
    Haka kuma idan muka kalli ayar mubahala zata tabbatar mana da cewa Aliyu shi ne gaba a kan dukka nin Shabban Manzon Allah (s.a.w) miyasa saboda siffan ta shi  da aka yi da irin siffar Manzon Allah (s.a.w)  cewa shi da Manzon Allah (s.a.w)  duk abu guda ne, sannan  sananen abu ne cewa duk wanda zai gaji Annabi tabbas ilimin sa da na Annabi abu guda.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: