bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:06:03
Haka ma munsan cewa Annabi (s.a.w) a yaqi daban-daban ya tabbatar da jarumtar Aliyu (a.s) misali a yaqin khandaq inda Imam Ali ya kara da Amru
Lambar Labari: 333
JARUMMATAR IMAM ALI (A.S).
      Ahlusunna ma sun tabbatar da jarumkatar Aliyu bn Abi Xalib (a.s) a kan sauran Sahabbai, domin kuwa sun naqalko ruwaya a kan jarumtar Aliyu daga bakin  Halifa na biyu inda yake cewa:
(( والله لولا سيف علي لما قام عمود الدين)) ya ce: ( Ina rantsuwa da Allah ba don takobin Ali ba da addini bai tabbata ba)(11) .
     Haka ma munsan cewa Annabi (s.a.w) a yaqi daban-daban ya tabbatar da jarumtar Aliyu (a.s) misali a yaqin khandaq inda Imam Ali ya kara da Amru bn abdul wuddi ya kuma yi nasara a kansa a nan ne Manzon Allah (s.a.w) ya ce: (( ضربة علي يوم الخندق أفضل من عبادةالثقلين)) ( Dukan da Ali yayi a ranar khandaq falalarsa tafi ibadar aljanu da mutane)(12) .
        Bayan da yawan Sahabbai sun kasa tarar wannan qasurgumin jarumin  saboda sun san cewa duk wanda ya yi gaba da gaba da Amru bn Abdul wuddi sai dai labarinsa, sau uku Manzon Allah yana yiwa Sahabbai tayi cikin ku akwai wanda zai tari wannan kafirin ya yi mubaraza da shi a Aljanna yana tare da ni amma kowa cikin su sai dai ya sunkuyar da kansa qasa, a irin wannan halin ne duk lokacin da Annabi (s.a.w) ya yi magana sai Aliyu (a.s) ya xaga hannunsa sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce masa ya zauna sai da a ka yi haka sau uku sannan Annabi ya bawa Ali dama. Manzon Allah (s.a.w) ya ce: kafircin duniya da kuma imanin duniya ne zasu gwabza inda daga qarshe bayan Annabi ya yi wa Imam Ali addu’ar ya kuma xauko rawanin sa  mai albarka ya xora mashi a kanshi, haka Ali (a.s) ya tari wannan qasurgumin kafiri kuma Allah ya ba shi nasara a kansa ya halaka shi wanda bayan ya kai shi qasa anga Imam Ali (a.s) kamar zai sare kansa sai ya fasa ya juya sai bayan wani xan lokaci kaxan sannan ya dawu ya sare kan kafirin, an tamye shi miyasa da farko bai sare kan Abdul wuddi ba? Sai ya ce: ban ya kai shi qasa ya tofa masa yawu ne sai ya yi fushi to shi ne ya xan tafi kaxan fushin sa ya sauka domin ba ya son ya yi wani abu a kan fushin sa yana so ya yi don Allah ne, shi yasa sai da ya bari fushin sa ya sauka sannan ya dawu ya sare kan kafirin, ka ji masu yi don Allah da Manzonsa.
       Haka ma ta faru a yaqin Uhdu inda sanadiyyar shagala da kuma savawa umarnin Manzon Allah da wasu daga cikin sahabbai suka yi, ya jawu mummunan yanayi tsakanin Musulmai inda hatta Manzon Allah (s.a.w) sama da ciwu saba’in 70 ne a jikin sa mai albarka harma wasu sun fara yaxa  qaryar cewa wai an kashe Annabi (s.a.w), wannan qaryar da aka yaxa tasa musulmai sunyi rauni sosai, saboda haka su kuma kafirai suka sami qarfin gwuwa, ta yadda aka kashe da yawa daga cikin Musulmai wasu kuma aka ji musu mummunan ciwu waxanda suke jefan Annabi sunyi rauni sosai suna cikin firjici da tsoro daga qarshe duk suka watse suka bar Annabi shi ka xai, wani daga cikin Musulmai ya zo yana tambayar wani sahabi mai suna Sa’ad bn Rabi’i wanda an ce akwai ciwu a jikinsa sama da sha biyu 12 ya tsallako wajen sa yana cewa naji an ce an kashe Manzon Allah (s.a.w) ? yana  tambayar Sa’ad xin ne. sa’ad ya ba shi amsa da cewa amma ai Ubanjigin Annabi rayayye ne kuma shi ba zai tava mutuwa ba, miyasa kai ba zaka yi wani aiki ba shin ba zaka kare addinin Allah ba? Aikin mu ba shi ne kare Manzon Allah (s.a.w)  kaxai ba, da za a ce idan an ka she shi shikenan aikin mu ya qare, dole ne mu kare addinin Allah kuma wannan ne ai kin mu koda yau she.
     Akwai ruwayoyi da yawa da suka tabbar da firjicin da tsoro da Sahabbai suka shiga a yaqin Uhdu, kuma da yawa daga cikin banya bayan sahabbai sun gudu sun bar Manzon Allah (s.a.w) ga  ma wasu daga cikin waxanda suka gudu xin kuma suka yi bayani da kansu:
(( خطب عمر بعد رسول الله يوم الجمعة, فقرأ ال عمران, فلما انتهي الى قوله: ان الذين تولوا منكم يوم التقى المجعان , قال: لما كان يوم أحد هزمنا هم ففررت حتّى صعدت الجبل, فلقد رأيتنى انزو كأننى اروى (13) .                           
•    وفرّعثمان بن عفان وعقبة بن عثمان وسعد بن عثمان رجلان من الأنصار ثم من بنى زريق حتّى بلغواالجلعب جبلا بناحيةالمدينة فأقاموابه ثلاثا ثم رجعوا الى رسول الله صلى الله عليه واله وسلم (14) .                                                               
•         Umar yayi huxuba bayan Manzon Allah (s.a.w)  [ ma’ana bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) ]  a ranar wata Juma’a, sai ya karanta Ali imrana, lokacin da ya kai wannan ayar: Inanal lazina tawalau minkum yaumal taqal jam’ani. Sai ya ce: Na kasance a ranar Uhdu da muka afka masu, na gudu ina tsalle  a kan dutse haqiqa na tsinci kai na kamar Bunsurun arwa.( wani Bunsuru ne da yake rayuwa a daji ya iya hawa da sauka akan duwatsu).
       Da kuma yanda su Usman suka gudu: Usman bn Affan ya gudu da Uqba xan Usman, da Sa’ad xan Usman, suna daga cikin Ansar, sanan daga cikin qabilar zuraiq, har sai da suka kai wani wuri mai suna jal’aba a cikin garin Madina suka yi kwana uku a wurin sannan sai suka koma wajen Manzon Allah (s.a.w).     
       A irin wannan yana yin ne Aliyu bn Abi Xalib (a.s) ya tsaya tsayin daka wajen kare Annabi (s.a.w) inda harma sai da aka ji Muryar Mala’ika Jibrilu daga sama tana cewa: (( لا فتي الا علي لا سيف الا ذوالفقار)) ( Ba wani saurayi sai Ali ba kuma wata takobi sai zulfiar)(13) . [zulfiqar takobin Imam Ali ce] haka Imam Ali (a.s) ya kasan ce yana bawa Manzon Allah (s.a.w) kariya a ko ina har zuwa wafatinsa (s.a.w).
Muhaxu a kashi  na biyu ciba daga inda muka tsaya.

  Aliyu Abdullahi Yusuf:
  Whatsapp,     Telegram, Facebook Number: +2348037493872.
            



comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: