bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:10:56
Bayan nazari akan isma da ilimin saninin Allah wanda Imam ya mallaka ko kuwa mu’ujizozi- karamomi-wacce ta kasance ta bayyana a wajensa, ba waninsa ba
Lambar Labari: 335
GABATARWA:
Ba’a iyakance wasu dalilai na shari’a ba wajen yaxuwar fifikun Imam Aliyu bn Abi Xalib (a.s) ta vangaren kevewar Manzon Allah (s.a.w) da maganar da tazo daga gareshi akan haqqin Ali (a.s) abin sani dai ayoyin Alqur’ani masu yawa waxanda suke bayyana taklifin matsayin Ali (a.s).
  Da kuma mulahaza ga kuwanne nassi da aka samu haqiqanin ko wanne dau’in  fifikun Ali (a.s) akan sahabai ba wai ta vangaren kwatantasu kawaiba, abin sani dai mafi yawan nassusi da wannan ma’anar ya tattaro maqasudin ta cear tabbas girman tsarkin Aliyu (a.s) shine mutum madai daici Imami wanda za abi bayan Manzon Allah ba waninsa ba.
  Bayan nazari akan isma da ilimin saninin Allah wanda Imam ya mallaka ko kuwa mu’ujizozi- karamomi-wacce ta kasance ta bayyana a wajensa, ba waninsa ba, yarage Aliyu (a.s) da ikonsa da iliminsa da siffofinsa shi yafi falala akan sahabbai, kai harma a kiyasin makarantar Halifofi wwaxanda suke ganin Imam Aliyu (a.s) sahabine kawai ba waniba.
     Anan zamu kawo maudu’in fifikon Imam Aliyu (a.s) akan sahabbai wanda ya tattaro al’amura:
AL’AMARI NA FARKO: BAYYANAR KEVANTAR IMAM ALIYU (A.S)
     Tabbas nutsewar Imam Aliyu bn Abi Xalib (a.s) da sanin Ubangiji tana alamta jarrabawar Ubangiji da qarfin kyawanta.   
   Ba zai yiwu mukai ga asraran da taxaukaba akan wannan jarabawa wajen ciratowar wani sashi na bayyanar ilimi ko kuma suluki ba.
     Sai dai muna da shaida har tsayuwar wani sashi na zahiri ya isar shi dalili akan falalar Imam Aliyu (a.s) akan sahabbai ba wai iyakan taccen fageba kawai, harma a ko waxanne fagage, ta yanda baya isar da wancan shakkun cewar tabbas Aliyu bai dai daita da ko wanne sahabi ba, akwai wasu bayya nannun kevance kevancansa (a.s):
1    kevantar Imam Aliyu (a.s) ta fagen ilimi a fili
Tabbataccen abune tabbas Imam Aliyu (A.S) ya kasance mafi Ilimin sahabbai, haqiqa akwai cikakken ilimi a wurin Aliyu (a.s) wanda darajarsa takai cewar Manzon Allah (s.a.w) yace dashi: (( Nine birnin ilimi Aliyu kuma qofarsa))(1). Manzon Allah baiyi kwatankwacin wannan maganar ga xaya daga cikin sahabbai ba.
  Wannan kuma yana qarfafa maganarsa (A.S): (( Manzon Allah (s.a.w) ya sanar dani kofofi dubu na ilimi kowace qofa tana buxenman qofa dubu))(2).
    Aliyu ya qarfafa da ilimin ubangiji wanda ya kevanta dashi, yana da’awar cewa: (( da za a ya yenman hijabi da banqara yaqiniba))(3).
   Ya bayyana a fili cewar tabbas iliminnsa (a.s) da yake xauke dashi babbane ba wani sahabi da yake xauke da kwatan kwacinsa: (( yakan nuna qirjinsa yace: a nan kam akwai ilimi mai yawa))(4).
Waxannan magan ganu suna nuni da dukkan bayyana akan cewar tabbas  matsayin ilimin Aliyu  ba wanda yake dashi a cikin face Manzon Allah (s.a.w).
   Da wannan ne (a.s) yake nuni da maganarsa: (( kabar wannan akan fannuni na ilimi da za a )).
 An karvo daga Abi Xafil yace: Naga Aliyu yana cewa: (( ku tambayeni wallahi bazaku tambayeni akan wani abuba sai na baku labarinsa ku tambayeni akan Littafin Allah ina yimuku rantsuwa da Allah ba wata aya data sauka a cikin dare ko rana sai na santa, a kan tudune ko a kwari))(5).
    An karvo daga sa’idu xan Musib yace: (( Ba wani daga cikin sahabban Manzon Allah (s.a.w) da yake cewa ku tambayeni sai Aliyu (a.s)(6).
Haqiqa naga Manzon Allah (s.a.w) da mafi yawan lokuta akan fifikon falalar ((Aliyu))  da wucewar iliminsa akan sahabbai.
   Manzon Allah (s.a.w) yace da Faximat Zahara’u (a.s): (( Ba zaki yadda in aura maki wanda shi ya gabaci al’ummata muluntaba, mafi yawan iliminsu, mafi yawan haqurinsu))(1).
   Manzon Allah (s.a.w) yace: (( mafi sanin al’ummata bayana Aliyu bn Abi Xalib))(2).
  Manzon Allah (s.a.w) yace: (( Aliyu shine mai kiyaye ilimina kuma wasiyyina kuma shine  qofar da za a zo man ta ita ))(3).
  Manzon Allah (s.a.w) yace: (( Aliyu shine qofar ilimina kuma shine mai bayanin saqon da aka aikoni da shi ga al’ummata a bayana))(4).
   Manzon Allah (s.a.w) yace: (( mafi sanin al’ummata sunna da Hukunci a bayana Aliyu bn Abi Xalib))(5).
   Manzon Allah (s.a.w) yace: (( kai wanda zaka bayyanawa al’ummata savaninsu bayana))(6).
   Manzon Allah ( s.a.w ) yace: (( Ayi mamakin iliminka ya Abul Hasan, haqiqa kasha ilimi sha )).

KEVENTAR IMAM ALIYU (A.S) TA BANGAREN IMANI A FILI.
    Wannan siffar daga rayuwar Imam Aliyu (a.s) haqiqa akwai don qulallayar ma’ana a cikinta ta vangaren qololuwar xaukaka da kuma yan kankiyar hujja matsayinsa akan Sahabbai.
   Qarfin imanin Aliyu (a.s) kuma haqiqa a wajen ibada shi misaline, haqiqa yazo a cikin Tafsiri maganar Allah (T.A): {{ Zakagansu suna Ruku’u da sujjada}}  wannan ayar ta sauaka ne akan Aliyu (a.s).
Da irin wannan ne yake cewa (a.s): (( Nayi sallah tareda Manzon Allah (s.a.w) shekara bakwai kafin mutane nine farkon wanda yayi sallah tareda shi )).
   Yace (a.s) Bansan wani mutum xaya a cikin wannan Al’ummar daya bautawa Allah ba bayan Manzon Allah  face ni )).
 Yace (a.s)(( Na musulunta kafin mutane su musulunta nayi sallah kafin suyi sallah)).
   Imam Aliyu (a.s) ya kasance wannda yafi mutane bauta ya kuma fisu yawan sallah da Azumi, daga gareshi ne mutane suka koyi sallar dare da Lazimi da wurididika, da tsayuwa akan Nafila, me kake tsammani ga mutumin da yakai gaya wajen kiyaye waridinsa wanda yayi shinfixa a tsakiyar mayaqa a daren harir a yaqin siffin, yana sallah yana wiridi kibiyoyi na wucewa ta ko wanne vangarensa hagu da dama, bai ko damu da hakan ba, bai kuma tashi ba har saida yagama wasifarsa? Me kake tsammani ga mutumen da in yasa goshinsa qasa yake doguwar  sujjadarsa?
   Ancewa Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin (a.s) ya kasance wanda ya kai qololuwa wajen Ibada-: ya Ibadarka take in an kwatanta da Ibadar kakanka?
Sai yace (a.s): (( kwatan kwacin Ibadata data kakana kamar Ibadar kakanace data Manzon Allah (s.a.w) )).
   Amma awajen bayyanar wani  Imani zaka samu Imam (a.s) ya kai qololuwa a cikin halittun Ubangiji, shi kamar qur’ani ne wanda ma’anarsa ta bayyana,  haqiqa Allah (T.A) yana cewa: {  Waxanda sukayi Imani da Allah da Manzanninsa waxannan sune masu gasgatawa}.
   Wannan ayar Ahmad bn Hanbali ya ruwaitota cewar ta sauka ne akan Aliyu bn Abi Xalib (a.s).
   Akwai ayoyi dayawa dasuke shaida kan cewa tabbas Aliyu (a.s) shine misalin Rai da ma’anar Imani haqiqa Allah Ta’ala yana cewa: { Ace mai shayar da mahajjata da makunlin masallacin makka sunyi dai dai da wanda yayi Imani da Allah da Ranar Lahira kuma yayi Jahadi saboda Allah ba za a haxusuba a wajen Allah, Allah baya shiryar da Azzalimai }.
    Wannan ayar da wacce take bayanta sun sauka ne saboda (( Aliyu)) lokacin da Xalha bn Shaibatu da Abbas sukeyin Alfahari, Xalha yace: Nine wanda yafi  domin makullin Xakin Allah yana Hannu na, Abbas kuma yace: Nine nafi domin nine nake shayarwa kuma nake kula da ita, Aliyu yace (a.s): (( Nine farkon Imani a cikin mutane kuma nafisu yin Jihadi )), sai Allah Ta’ala ya saukar da wannan ayar yana bayani akan fifikon falalar  Imamu Aliyu bn Abi Xalib (a.s) akan su biyun.
 Allah yake cewa: (( Shin  wanda yake Mumini Kamanr Fasiqi ne ba zasuyi dai dai ba.} Mumini shine Aliyu (a.s) Fasiqi kuma Walid.
   Da wannan ayar ne Alqur’ani mai Girma yake kwatantawa  mutane irin Imanin Aliyu (a.s).
{ kuma ba’abota muzunci waxansunsu sunfi waxansu a cikin littafin Allah a kan muminai da muhajirai} Gaba xaya masanan Tafsiri suntafi kan cewa wannan ayar akan Aliyu (a.s) ta sauka domin shine ma’abocin zumunci kuma  muhajiri.
   Kamar yadda manzon Allah (s.a.w) ya bayyanawa mutane a mafi yawancin wuraren isar da saqonsa da koyarwarsa, da wanda ya riga shiga musulunci, shine mutum mai karfin imani akan kawar da matsaloli a lokacin da suka taso. An ruwaito daga Abi Zarrar, inda yake cewa: Munshiga wagen manzon Allah (s.a.w) sai mukace: wanda yaso sahabinka da kai, idan lamarin ya kasance muna tareda shi, ko kuma idan baka nan muna tareda waninsa? Sai yace: Ali ya gabaceku shiga musulunci da kuma imani)).
Ya ishemu wannan dalilin daya bayyana na iko akan karfin imani nin Aliyu (a.s) da kuma falalarsa bari kuma muga vangaren jihadi.
3    Bayyanar kevantuwar Imamu Ali (a.s) ta vangaren Jihadi.
Amma jihadi a wajen Aliyu (a.s) ya tabbata ya kutsa ya gudana cikin magudanar  fita sarari da tabbatuwar abinda yake kowa ya sani, Lallai shi ba savani tsakanin musulmai da wa sunsu tabbas Ali awajen jihadinsa ya kasance mafi sadautakar sahabai bayan manzon Allah (s.a.w) da gabatawa ga mafi yawansu, koda kuwa ya kasance sauki da wajibcin jihadi a wurin sahabbai ya fito fili a rayuwarsu, sai Ali (a.s) kimarsa ta fara ga mafi yawan abubuwa masu wahala a wajen komawa qarshe, da barin ikonsu akan halaccinta, to sai Ali (a.s)
 


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: