bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:12:22
Kuma ba dukkanin Malaman Sunna ne suke riqo da ita ba, akwai da yawa waxanda suke inkarinta
Lambar Labari: 336
Kamun qirji wanda ake ce masa"Qabalu", wato xora hannun dama a kan hannun hagu akan Qirji ya yin sallah.

Cikin yaren Larabci kuwa a janibin Sunna suna kiran wannan aiki da "Al-qabdhu". Amma a vangaren Mazhabin Ahlul-baiti (A) ana kiran wannan kamun qirjin da suna                      "At-takfiir, At-takattuf, At-taktiif fis-salaat".

Lallai idan muka yi duba cikin litattafan magabata a wannan janibi na Mazhabobin Sunna baki xayansu zamu riski cewa suna riqo da wannan lamari ne na Qabalu bisa hujjojinsu na samun wasu maganganu masu kama da Hadisai, sai dai ba Hadisan Annabin ba ne, ma'ana ba maganar da ta fito daga bakin Annabin tsarki Muhammad xan Abdullahi (S) ce ba, maganganu ne na wasu mutane daban, kamar yadda hakan ya zo cikin litattafn Sunnan. Kuma ba dukkanin Malaman Sunna ne suke riqo da ita ba, akwai da yawa waxanda suke inkarinta. Amma cikin ikon Allah za mu xan taqaice mu kawo wasu daga hujjojin na su, sannan mu yi musu duba na Masana, sai mu ga menene kuma makomarsu.

           MAGANGANUN DA SU KA ZO A VANGAREN SUNNA
                          DA SUKE RAVA SU DA QABALU

1-    A cikin babban Littafin Sunna kuma magabaci daga Litattafan Sunna na farko, wato Littafin Imam Maalik, mai suna Al-muwaxxa' za mu ga ya kawo a cikin juzu'insa 2, shafinsa na 62:

"Mutane sun kasance ana umartarsu a kan xayansu ya sanya hannunsa na dama a kan hannunsa na hagu a cikin sallah. Sai Abuu Haazim ya ke cewa: Kuma ni ban sani ba (Ma'ana bai san ma maganar ba), sai dai shi Imam Maalik yana nuna daga Manzo ne (S)" (To ashe shi bai san ma maganar ne daga Annabi ba kenan).

2-    Haka nan ya zo a cikin Littafin Abuu Abdur-Rahmaan Ahmad bn Shu'aib mai suna Sunanun-Nasaa'iy a cikin Juzu'insa na 3, shafinsa na 452:

"Daga Zaa'idata ya ce, Aasim bn Kulaib ya labarta mana cewa, Babansa ya faxa masa cewa, haqiqa Waa'il bn Hujrin ya ba shi labari yace: Na ce lallai sai na duba na ga yadda Manzon Allah (S) ya ke Sallah, sai na dube shi, sai ya tashi ya yi Kabbara ya xaga hannayensa har suka kai saitin Kunnuwansa biyu, sannan ya xora hannunsa na dama a kan tafin na hagu, tare da wuyan tafin hannun da dantsen, ya yin da ya so yin Ruku'u sai ya xaga hannayensa ……". Mun zo "Muhallush-shaahid". Hakanan za a iya dubawa cikin littafin Musnadus-sahaabah fii kutubut-tis'ah a musnadin Waa'il bn Hujr.

3-    Malam Sulaimaan bnul-Ash'ath Abuu Daawud a cikin Sunan xinsa (Sunan Abu Daawud) Juzu'insa na 1, shafinsa na 274, ko kuma a wani xaba'in juzu'insa na 1, shafinsa na 260:

"Daga Zur'ata bn Abdur-Rahmaan ya ce, na ji Ibn Zubair yana cewa: Haxa sahu da sanya hannu kan hannu yana daga cikin Sunna". A wannan Hadisin Nasiruddiin Albaniy ya yi Tahqiiq ya ce wannan Hadisin Raunanna ne. Kunga shike nan ma ba sai mun ce komai a kansa ba.

4-    Hakanan dai a cikin Sunan Abii Daawud xin juzu'insa na 1, shafinsa na 274:

"Daga Ibn Mas'uud ya kasance yana sallah sai ya sanya hannunsa na hagu a kan na dama, sai Manzon Allah (S) ya gan shi – sai (Manzon) ya sanya hannunsa na dama a kan na hagu". Albaaniy yace wannan Hadisin Hasanun ne.

5-    Malam Buhari kuwa a cikin Sahihin littafinsa juzu'insa na 3, shafinsa na 251, ko kuma a wani Xaba'in juzu'insa na 1, shafinsa na 16:

"Daga Sahl bn Sa'din ya ce: an kasance ana umartar Mutane da namiji ya sanya hannunsa na dama a kan dantsen hagu a cikin Sallah. Sai Abuu Haazimin ya ce; ni ban san wannan ba (Daga Annabi), sai dai shi yana jingina abin ga Annabi (S). Sai Ismaa'il ya ce; suna jinganawa, bai ce yana jinginawa ba". To ga dai Hadisin Buhari mafi inganci a wajen Sunna ana ta dabal-dabal – amma duk da haka a qa'ida wannan yana tabbatarwa ne da ba Annabi ne ya ke umarnin ba, ina jin su Halifa Umar xan Haxxabi ne.

6-    Malam Muslim kuwa a cikin Sahihinsa shi ma wanda Malam Nawawiy ya yi masa sharhi – na Muhyiddiin bn Sharafun-nawawiy a juzu'insa na 4, a Kitaabus-salaat, shafinsa na 39, a wani Xaba'in kuwa a juzu'insa na 1, shafinsa na 301, duk dai a "Babin ya xora hannunsa na dama a kan na hagu ……":

"Daga Waa'il bn Hujr ya ce: ya ga Annabi (S) ya xaga hannayensa biyu ya yin da ya fara yin Sallah, ya yi Kabbara, ………………, sannan ya xora hannunsa na dama a kan na hagu".

Waxannan sune daga mafi girman hujjojin da Malaman Sunna suke kawowa a cikin Litattafansu na ba su damar yin Qabalu a cikin Sallah, inda wasu suke cewa Sunna ce mai qarfi, wasu kuwa cewa suke wajibi ce, wasu kuwa masu sauqin ra'ayin da fuskantar abin da suka fuskanta game da wannan maganar da kai tsaye ba bu mai cewa Maganar Manzo ce (S), sai suke cewa babu laifi ka iya aikatawa.


                  HADISAN SUNNA DA SUKA ZO A KAN YIN SADALU
                                     (SAKIN HANNU A SALLAH)

1-    Ya zo a cikin littafin Malam Xabaraaniy mai suna Al-Kabiir da lafazinsa kamar haka:

"Manzon Allah (S) ya kasance idan ya zamo yana cikin Sallah yana xaga hannayensa har zuwa kusa da kunnuwa, idan ya yi kabbara sai ya sakesu" (Al-mu3jamul-Kabiir: 20/74).

2-    Haka nan ya zo a cikin Hadisin Abiy Hamaidus-saa'idiy wanda Malam Buhariy ya fitar da shi da Abu Dauda, kuma na cikin Abu Daudan wanda a ka fitar ta hanyar Ahmad bn Hanbali ya ce: Abu Humaid da wasu Mutane guda goma daga cikin Sahabbai sun yi ijma'i, daga cikinsu akwai Sahal bn Sa'ad, sai suka ambaci sallar Manzon Allah (S), sai Abu Humaid ya ce: ni na fi ku sanin Sallar Manzon Allah (S), sai suka ce: don me? Wallahi kai dai ba ka fi mu yawan kasantuwa da Shi ba (S), haka nan ba ka gabace mu wajen tarayya da Shi ba (S). Sai ya ce: haka ne, sai suka ce: to faxi mu ji, sai ya ce: Ya kasance idan ya tashi yin Sallah yana xaga hannayensa har sai ya kai su kafaxarsa, sannan ya yi kabbara har sai dukkanin Qasusuwansa ko wanne ya koma mazauninsa, sannan ya yi karatu sai ya yi ruku'u – lokacin da ya gama faxa sai suka ce ka yi gaskiya. Wanda sanannen abu ne mazaunin hannaye ya yin da mutum ya ke tsaye shine varukan sa biyun (Wato dama da hagunsa a saki hannayen qasa) ba wai Qirji ba. Hakanan shi Sahal bn Sa'ad maruwaicin Hadisin "An kasance ana umartar Mutane a kan Namiji ya xora hannunsa na dama a kan na hagu" yana cikin mahalarta wajen, da kuma bai kasance ya san shi Hadisin ya bar riqo da aikin da shi ba, da sai sun ce masa ka bar xora hannu kan hannu, sai dai kawai cewa suka yi da shi ka yi gaskiya, ba su ce: ba ka faxi Annabin (S) ya xora hannun a kan xaya ba. (Sunan Abiy Daawud Juz. 1, Shafi 194, da kuma Ibraamun-naqdh na Muhammad Khidr bn Maayaabiy Al-jakniy Ash-shanqiixiy shafi na 18-32).

Haka nan dai Abii Humaid ya na da wata ruwayar daban wajen bayyana yadda SallarSa ta ke (S) a aikace, wanda a cikinta ya bar hannayensa a sake a inda suke, kuma wannan ruwayar ta aiki wacce Xahaawiy ya ambace ta da Ibn Hibbaan kuma Muhammad Khidr bn Maayaabiy Al-jakniy Ash-shanqiixiy ya naqaltota a cikin Ibraamun-naqdh shafi na 27.

3-    Yana daga ciki abin da Al-Haafiz Ibn Abdul-barr ya naqalto a cikin "Kitaabul-ilm" cewar ya ce:

Haqiqa Maalik ya naqalto Hadisin Sadalu daga Abdullaahi bnul-Hasan, (A duba cikin littafin Ibraamun-naqdh shafi na 39).

4-    Yana daga ciki abin da aka ruwaito na samun Malamai sun tabbatar da samuwar Abdullahi bnuz-Zubair ya kasance ba ya Qabalu, kuma ba ya tava ganin wani mutumin yana yin qabalun sai ya kama hannun ya warwaresu ya miqesu. Wanda kuma Al-Khaxib ya naqalto a cikin "Taariikhu Baghdaad" cewar shi Abdullahi bnuz-Zubair ya karvi siffar Sallarsa daga kakansa Abu Bakar Siddiq, wanda wannan yana bayyanawa daga gareshi ne cewa Halifa Abubakar ba ya Qabalu. (Ibraamun-naqdh shafina 3, Al-qawlul-fisal shafina 24).

Aminci ya tabbata ga waxanda suka bi shiriya har ya zuwa ranar sakamako.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: