bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:23:03
Kamar ina ganin Shugabannin Yahudu sun sanya hannayensu
Lambar Labari: 337
5-    Malam Ibn Abiy Shaibah ya naqalto daga Hasanul-Basariy da Ibrahiimun-Nakha'3iy da Sa3iid bnul-Musayyib da Ibn Siirina da Sa3iid bn Jubair, sai ya ce sun kasance ba sa yin Qabalu a cikin Sallah, kuma sun kasance daga cikin Manyan Tabi'ai ma su karvowa daga Sahabbai (R), waxanda a ka sansu da ilimi da qasqan da kai. (Ibraamun-naqdh shafi na 33). Kuma daga misalinsu akwai Abu Mijlaz da Uthmaanun-nahdiy da Abul-jawzaa'. Wanda kuma tabbas waxannan dukkansu sun naqalto a kan tabbas Qabalu ta kevantu ne ga Shugabannin Yahudawa da Kiristochi "Bishop". Wanda an tambayi Ibn Siiriina a kan xora hannun dama a kan na hagu a cikin Sallah sai yace: Lallai hakan ya faru ne ta sanadin Rum, Hasanul-Basariy ya ke cewa: Annabi (S) ya ce: Kamar ina ganin Shugabannin Yahudu sun sanya hannayensu na Dama a kan na Hagu a cikin Sallah (Ibraamun-naqdh shafi na 34 – wanda ya naqalto Ibn Abiy Shaibah).

6-    Yana daga cikin riqo da Sadalu, faxin Malamai cewa: Lallai Sadalu ko ta zamo abin qi ko kuma halas, kuma lokacin da xaya daga cikin Malaman Shafi'iyya suka yi qoqarin cewa Makaruhi ne, sai wasu suka yi musu Raddi da cewar Imam Shafi'iy a cikin Al'um ya ce ba bu laifi gareshi ga wanda ba ya wasa da hannayensa a cikin Sallah. Amma shi Qabalu a cikinsa tare da Magana a kan zargi, to ya karkata ne ga abin qi da kuma Magana a kan Hani.

Sai ya kasance (Qabalun) daga abu mai rikitarwa da a ke buqatar barinta da Hadisin da a ka yi ittifaqi a kansa shine; Faxinsa (S): "Ita Halas bayyananna ce, hakanan ma Haram bayyananna ce, kuma a tsakaninsu akwai lamura ma su rikitarwa". Wanda kuma haramcin Muhammad Sunusiy ya naqalto shi a cikin littafinsa mai suna: "Shifaa'us-sadr baarii masaa'ilul-ashr", haka nan Al-Haxxab da wasunsa suma sun naqalto shi ya yin Magana a kan Qabalu a cikin Sallah.

7-    Haka nan dai yana daga cikin dalilan da suke tabbatar da Sadalu Hadisin "Al-musii'u salaatahu" wanda ruwayar Al-Haakim ta ambace shi daga gareshi, wacce kuma tana kan gundarin "Sharxush-shaikhaini" – a wannan wajen ne sai na tuna lokacin da muke tattaunawa da Baban Hamdan (Dr. Mansur Sokoto) na kawo Hadisin Ibn Abiy Waqqaas wanda Hakim ya fitar shima ya ce "Qadit-tafaqash-shaikhaani", sai ya ke cewa wai ya duba cikin Buhari da Muslim xin ba bu Hadisin. Wanda ya bamu mamaki sosai na rashin sanin isxilahin Malamansa a kan wannan jumla, da maganarsa ta ke nuna sam bai sam me a ke nufi da ita ba. "Ash-shaikhaini" dai tana nufin Buhari da Muslim ne, kuma duk Hadisin da a ka fitar da shi ta irin hanyar da Buhari ko Muslim suka fitar ta vangaren ingancin Sanadin, to Sunna suna ce masa a bisa sharaxinsu. Misali: ya kasance masu naqalto Hadisin an yi ittifaqi a kan thiqarsu da isnadin da ya jone da wani Fitaccen Sahabin, ……………… - Wanda a cikin wannan Hadisin na Musii'u Salaatahu, a cikinta akwai farillan Sallar da Mustahabbai, amma ba a ambaci Qabalu a ciki ba. Kuma lafazinsa - bayan ya nemi mai vata sallartasa ya san yadda a ke yin Sallar – Sai Manzon Allah (S) ya ce masa: Lallai ya tabbatar da tsarki, sannan ya godewa Ubangiji ya girmama shi, sannan ya karanta daga Qur'ani abin da Allah ya yi izini a cikinsa, sannan ya yi kabbara ya yi ruku'u, sannan ya sanya tafukan hannayensa a kan gwiwoyin qafarsa har sai gavovinsa sun daidaita sun tsaya cak, sannan ya ce: "Sami'allahu liman hamidahu", sannan ya tashi ya tsaya kyam har sai kowane qashi ya koma mazauninsa ya tsaya. Sannan ya miqe kyam har bayansa ya daidaita, sannan ya yi kabbara ya yi sujjada, da kuma yiwuwar goshinsa daga sujjadar har sai gavvansa sun daidaita sun tsaya cak, sannan ya sake kabbara ya xago kansa ya zauna kyam a mazauninsa har sai bayansa ya miqe ya daidaita. Ya wassafa sallar kamar haka har ya gama sannan ya ce: "Sallar xayanku ba za ta cika ba har sai ya aikata ta haka".

Wanda kuma ruwayar wannan Hadisin ta hanyar Al-Haakim ta bayyana a sarari a taqaice abin da za a aikata a cikin Sallah daga Farillai da Mustahabbai, kuma ba ta ambaci Qabalu ba. Kuma haqiqa Ibnul-Qassaar mutumin Baghdaad da wasunsa sun ce tabbas shi wannan yana daga cikin mafi dalilan Sadalu da kore Qabalu a cikin Sallah, a duba cikin (Al-qawlul-fisal na Shehu 3aabidul-makkiy a shafi na 9 – wanda shine Muftin Malikiyyah na Makka can da shuxewa).

8-    Akwai dai Haidisin da ya zo daga Abu Dauda kuma ya inganta shi, daga Saalimul-barraad ya ce: 3uqbah bn 3aamir ya zo mana sai muka ce masa: ka yi Magana a kan Sallar Manzon Allah (S), sai ya tashi a cikin Masallachi ya yi kabbara, ya yin da ya yi ruku'u sai ya sanya hannayensa a kan gwiwoyinsa sannan ya sanya yatsunsa can qasan gwiwoyin nasa, kuma ya tsayu a tsakanin gwiwowyin hannayensa har sai da komai na gavvansa suka tsaya kyam, sannan ya ce: "Sami'allaahu liman hamidahu", sannan ya tsahi har dukkanin gavvansa suka tsaya kyam, sannan ya yi kabbara sai ya yi sujjada ya xora tafukan hannayensa a qasa, sannan ya tsaya a tsakanin gwiwoyin hannayensa har sai da komai na gavvansa suka tsaya kyam, sannan ya yi kabbara ya xago daga kansa ya zauna har sai da dukkanin gavvansa suka tsaya kyam, ya aikata hakan kumawa dai, sannan ya kawo raka'o'i guda huxu kwatankwacin wannan raka'ar, sannan ya ce: Haka muka gan shi (S) ya ke Sallah. Wanda kuma wannan ya katange ko ya kawo qarshe a wajen Malamai, ba bu wani abu saura bayansa da ke nuna neman Qabalu a matsayin Mustahabbi ko Sunna, domin dukkanin Sunnonin sun zo cikin wannan Sallar ta Manzo (S) cikakkiya. Kuma yana nuni ne a kan qarshen aikinsa (S) shine barin Qabalu xin idan ma ya inganta ya tava aikatawa.

9-    Hadisin Hani a kan "Iktitaafi" shi ma yana daga cikin Hadisan da suke tabbatar da Sadalu – "Hadiithun-nahyi anil-iktitaaf fiis-salah" – wanda "Iktitaaf" tana nufin ne Qabalun wato kamun qirji. Kamar yadda ya zo a cikin littafin Al-qawlul-fasl shafi na 35, wanda kuma Hadisin dai Malam Muslim ya fitar da shi. Lafazinsa kuwa shine: Abdullaahi bn Abbaas (R) ya faxa ga wanda ya gan shi yana Sallah da Kitso a kansa: Haqiqa na ji Manzon Allah (S) yana cewa: "Haqiqa kwatankwacin wannan kamar wanda ya ke Sallah ne hannayensa a kan qirji (Qabalu).


Ga Nassin Hadisin: "Mathalullaziy yusalliy wara'suhu ma3qusun kamathalillaziy yusalliy wahuwa maktuufun" a wata ruwayar kuma "Yusalliy dhaafiran ra'suhu".

Wannan Hadisin ya zo a cikin Littafin Al-amthaal fiil-Hadiith na Abiy Muhammad Abdullah bn Muhammad bn Ja3far bn Hayyaan – wanda a gaban Hadisin Malamin ya ke cewa: "Isnaaduhu, Rijaaluhu thiqaat" – Sanadinsa da Mazajen Hadisin thiqa ne. haka nan dai wannan Hadisin ya zo a cikin Ahmad bn Hanbali juzu'insa na 1, shafi na 316, lambata 2905, da Xabaraaniy daga Ibn Abbaas a juzu'insa na 11, shafinsa na 422, lambata 12196, da dai wasu Malaman da daman gaske).

10-    Imam Ahmad ya fitar a cikin Musnadinsa a kan Annabi (S) ya kasance qarshen abin da ya ke gareshi shine Hani a kan yarda da Ahlul-kitabi. Kuma wannan bayan ya kasance ne yana son yarda da su a kan abin da bai sauka gareshi ba ne ko kaxan, haka kuma Qabalu – kamun qirji a Sallah – na daga cikin aikin Ahlul-kitaab kamar yadda Ibn Abiy Shaybah ya naqalto daga Al-Hasanul-basariy da Ibn Siiriina daga Imaman Sunna kamar yadda ya gabata. (A duba cikin Ibraamun-naqdh shafinsa na 33).

Don haka wannan ya na daga cikin gamsassu kuma ingantattun dalilai da za su isa wajen ingancin abin da ya zo a cikin Al-mudawwanah a kan Karhancin Qabalu a cikin Sallah.

Ubangiji ka qara datar da mu, ka sanya mu matabbata a kan tafarkin da Iyalan Annabinka Muhammad sallallahu alaiHi wa Alihi suke kai har komowarmu gareka, mu kasance Yardaddu ababen yarda, kamar yadda ya tabbata a cikin Qur'ani maigirma, a kan cewa Shi'ar Imamu Aliy su ne "Khairul-bariyyah", kuma su ne: waxanda za su tashi a ranar Alqiyama "Raadhiyatan mardhiyyatan".

Aminci ya tabbata ga waxanda suka bi shiriya har ya zuwa ranar sakamako.



comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: