bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:23:55
Sai Imam Ridah (a.s) ya ce: haka Manzon Allah (s.a.w) yake kaebar caffa. Daga nan Ma’amun bai sake cewa komai ba sai ya yi wa dansa manoniya sai Abbas
Lambar Labari: 338
YADDA MA’AMUN YA TILASTAWA IMAMU RIDAH (A.S)  KABAR MAGAJIN   HALIFA.
A wannan karon zamu kawa kadan daga cikin yanda Ma’amun ya tilastawa Imam Ridah (a.s) kabar mukamin magajin halifa ko kuman ya ka she shi, yanda aka yin a din da kuma abinda ya faru bayan na din, sai a biyo mu sannu a hankali dan jin yadda lamarin ya kaya.

Sai Ma’mun y ace: da shi ba ko ka matso da hannunka kusa don a yi maka mubaya’a?
Sai Imam Ridah (a.s) ya ce:  haka Manzon Allah (s.a.w) yake kaebar caffa.
Daga nan Ma’amun bai sake cewa komai ba sai ya yi wa dansa manoniya sai Abbas dansa ya yi caffa ta yadda ya dora hannuwansa kan na Imam (a.s).
Sauran mutane ma da suka hallata suma suka zo suka yi caffa ( wato mubaya’a ), mawakan zamanin masu suna khua’i da Nurwas suka  zo suka yi ta rera waka, bayan nansauran mawaka masu ka zo suka gabatar da albarkacin bakinsu.
Sannan mamun ya nemi Imam Ridah (a.s) ya yiwa mutane jawabi. Da farko Imam ya yiwa Allah madaukakin sarki godiya sannan ya ce kamar yadda muke da hakki a kanku saboda kusancin mu da Manzon Allah (s.a.w)da wannan zaku zama masu yi masa biyayya, haka kuma kuke da hakki a kanmu, idan kuka sauke nauyinmu da ya hau kanku to muma ya zama wajibi mu sauke nauyin ku da ya hau kanmu.
Sai ya yi shiru:
Ma’amun da Fadil wazirin Ma’amun da sauran muatne sun nemi Imam ya ci gaba amma yaki ya kara ko kalma guda.
Ma’amun a sarari ya nuna yana cikin farin ciki, amma hakan bai bayyana a fuskarsa ba karshen zama bai yi masa dadi ba.
Sannan ya tashi ya ce:
Daga yau zan bada umarni a buga sulallan zunare da Azurfa  ( wato kamar abuga sunan Imam kenan a jikin kudin sun a wancan lokacin ) da sunan magajin halifa ( wato Imam Ridah (a.s) kenan yake nufi), kuma daga yau a sanar da dukkanin sauran yan kuna Birane   da kauyuka su rika yin huduba da sunansa a kan mimbarori.
Daga nan sai yayi abinda yafi ko wanne muhimmanci a wajensa kuma yafi ko wanne tasiri ya ce: Daga yau ba zan kara sanya bakaken kaya ba, ( da yak bakaken kaya kamar alama c eta shigar Abbasiyawa a wacan lokacin ), sannan yacire abayar sa baka ya dauki koriya wacce dama an riga an tanadar masa ita, ( wato abinda yasa mamun ya sa koriyar abaya kamar yadda muka sani alama ce yayan gidan Manzon Allah (s.a.w),  sannan ya ce dole ne kowa ya yi haka sannan ya ce kaya masu launin kore sune kayan da ma’aikata da masu makami a wannan daular zasu rinka sawa, da haka ne aka kawo karshen taron.

           KOFAR GIDAJE DA KATANGUN GARI.
An yi bikin nada Imam Ridah (a.s) a matsayin magajin Halifa a ranar biyar ga watan Ramadan, Ma’amun ya san cewa dukka nin mutane suna so su yi sallar idin su tare da Imam, wannan yasa Ma’amun ya aikawa da Imam wasika "ka shirya jagorancin yin salla…. Kuma ka yi hudubar idin”.
Sai Imam ya ce da Ma’amun ka san sharadin da muka yi ni da kai a kan matsayin magajin halifa, saboda haka ka sauwake man Jagorancin wannan sallar.
Sai Ma;amun ya ce: Da yin hakan kana so ka ja hankalin mutane su rika fadin falalar ka da kamalarka.
Sau da yawa Imam ya nemi Ma’amun ya sauwake masa amma Ma’amun yaki . ya kuma dage kan cewa dole kai ne zaka yi limancin wannan sallar.
Daga karshe sai Imam (a.s) ya kaiwa Ma’amun cewa zan yi amma da sharadin yadda Manzon Allah (s,a,w) da kuma shugaban muminai Ali (a.s) suka yi zanyi?
Sai Ma’amun ya ce duk yadda kake so kayi.
A wannan lokacin sai Imam ya bada umarni da sassafe kowa ya zo kofar gidansa, dukkanin mutane manya da yara maza da mata suka taru da sassafe, suka yi sahu a gefen hanya wasu kuma suka tafi gaban gaban karaga.
Rana ta fito Imam ya yi wanka yasa rawani fari sai ya daya bakin kafadonsa, ya dora hannunsa a kan kwankwaso sannan ya umarci dukkanin yan tawagarsa da su aikata hakan.
A wannan lokacin ne ya dauki sandar shugabanci a hannunsa na hagu sannan ya fito waje daga cikin gida laoakcin day a fara tafiya sai ya kalli sama sannan ya yi kabbra da murya babba sau hudu zaukin sautin sa na ruhi ya yi tasiri kai ka ce sama da kasa gaba daya sun amsa masa suna mai maita abinda yake  cewa suna cewa Allahu akbar.
Sojoji da masu mukamai a gwamnati cikin azama ta mu samman sun jeru layi suma suka yi kabbara tare da Imam gaba daya arin marwa ya zama tuta daya suna da a murya da kabbara. Masu manyan matsayi da masu kudi da sukaga Imam ya fito ba takalmi ba bisa abin hawa ba gaba daya sai suka sabbko daga kan ababan hawan su , suka cire takalmansu suka biyo bayan Imam gaba dayansu , duk lokacin da Imam ya yi taku goma sai ya tsaya ya yi kabbara sau uku kasa da samu sun hade da sautin kabbarar da yake tashi daga bakunan mutane sai aka bawa Ma’amun labarin wannan fararen abu na mai tasiri a ruhi.
Fadhlu ya ce da Ma’amun: Ya amirul muminina idan Ridah ya isa masallaci da wannan ganganmin mai azama mutane zasu narke a cikin sonsa kuma wannan nada hatsari ga hukumar ka matuka, gara wannan lamarin kawai shine ka ba shi umarni ya koma gida.
Nan da nan kuwa Ma’amun ya bada umarni a gayawa Imam Ridah (a.s) ya koma gida, amma mutane suka sunyi ta daga murya suna Magana kuma a wannan ranar ba a iya yin sallar idi kamar yadda ya kamata ba.
Imam (a.s) ya  dawo gida mutane ma suka waste tun daga wannan rana ba a kara yin sallar idi a tsare ba.
Za mu dan dakata a nan Allah yasa mu samu da cewa,amen summa amen.
 Aminci ya tabbata ga waxanda suka bi shiriya har ya zuwa ranar sakamako.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: