bayyinaat

Published time: 02 ,February ,2017      08:04:09
Wannan koyarwar mai hasken littafin Allah tana nuna mana cewa kowane mutum yana daukar nauyin alhalin aikinsa. Da wannan ne zamu ga Imam Ali (a.s) yana ba wa mai tambaya amsa cewa da mutum ya zama abin tilastawa ne ba shi da wani zabi a aiyukansa da shari'a, sakon Allah, lada, zunubi, hisabi, duk sun zama bataccen lamari!.
Lambar Labari: 34
Akidar kaddara tana taka rawa mai girma a cikin wannan lamarin, masu akidar rashin ba wa sababi wani muhimmanci a cikin abubuwan da suke faruwa a rayuwar dan adam sun kausasa suka kan batun kaiyade iyali, don haka ne zamu ga kiristanci da Ash’ariiyanci sun kausasa magana kan wannan lamarin da tunanin cewa Allah (s.w.t) ne yake halittawa kuma shi ne yake bayar da abin da halitta zata rayu da shi. 
Amma masu tunanin da yake karfafa rawar da sababi yake takawa kamar mabiya mazhabar Ahlul-baiti suna ganin da gaske Allah madaukaki ne yake kaddara komai kuma shi ne yake halittawa yake arzutawa amma ya sanya sabuba a kan kowane abu. Misali mutumin da yake da albashi 50 000 a wata, amma yana da ‘ya’ya 15, kuma kowannensu yana bukatar kudin makaranta, tufafi, abinci sau uku a rana, kudin mota, a wata kuma yana biyan kudin wuta da ruwa, sannan yana da waya da take cin recharge card na 500 a kowace rana, ga matarsa tana neman na cefane 30 000 a kowane wata, to babu yadda zaka iya kwatanta rayuwarsa da wanda yake daukar 50 000 a wata, yana da ‘ya’ya 3. 
 Don haka ne ake samun bambancin mahanga duk da kuwa duk bangarori biyu a littattafansu babu wani abu da yake nuni da haramcin kaiyade iyali. Sai dai akidar Jabar (tilasci da cire tasirin mutum da sauran halittu a aiyukansu ko abubuwan da suke wakana) idan ta yi karfi sosai tana kaiwa ga inkari da musun samar da halin da al’umma zata kaiyade haihuwarta. Masu karfafa wannan akida ta jabar suna bayar da misali da wuta da zafi, suna ganin kamar yadda Allah (s.w.t) yake halittar wuta haka nan yake halittar zafinta kuma ita wuta ba ta da wani tasiri a wannan zafin. Sai suka kwatanta aikin mutum da wuta da zafinta ko wuka a hannun mai yanka ko kuma bindiga a hannun mai harbi. 
Amma sabanin wannan akidar akwai akidar zabin mutum da take cewa: Allah (s.w.t) ya halicci wuta a matsayinta na mai zafi mai kuna, kuma tana da tasiri wurin kona abu da lalata shi sakamakon Allah ya ba ta wannan siffar. Kur'ani ya buga misali ga mutane ya nuna musu hanya kuma ya haskaka musu ita cewa duk wani mutum yana da tasiri a aiyukansa kuma wasu suna yin sharri wasu kuwa suna yin sharri, kuma zai saka wa mai yin mummuna da azabar laifinsa mai yin kyakkyawa kuwa za a saka masa da ladan kyautawarsa. 
Wannan koyarwar mai hasken littafin Allah tana nuna mana cewa kowane mutum yana daukar nauyin alhalin aikinsa. Da wannan ne zamu ga Imam Ali (a.s) yana ba wa mai tambaya amsa cewa da mutum ya zama abin tilastawa ne ba shi da wani zabi a aiyukansa da shari'a, sakon Allah, lada, zunubi, hisabi, duk sun zama bataccen lamari!. 
Idan muka duba Kur'ani mai daraja zamu ga yana goyon bayan lamarin nan na hankali ne mai nuni da tasirin abubuwa a cikin rayuwar mutane. Kur'ani ya duba gaskiyar abin da yake faruwa a rayuwa, Kur'ani littafin Allah (s.w.t) ne mai tafiya da kowane zamani, kuma idan ya kasa warware matsalar mutane to don ba su fahimce shi ba ne, sai takaitawar ta kasance daga janibin su mutanen ne da ba su kama hanyar fahimtarsa ba. Duba fadin Allah madukaki yayin da yake cewa: Allah ya buga misalin bawa da ake mallaka wanda ba ya iya komai, da kuma wanda muka arzuta shi daga gare mu arziki kyakkyawa yana ciyar da shi a boye da a baiyane, shin zasu daidaitu, to godiya ta tabbata ga Allah sai dai mafi yawansu ba sa sani. Kuma Allah ya buga misali da mutane biyu dayansu bebe ne da ba ya iya komai kuma yana mai dora nauyinsa kan ubangidansa, duk inda ya sanya gaba ba ya zuwa da wani alheri, shin zasu daidaita da shi da wanda yake umarni da adalci kuma yana kan tafarki madaidaici. Nahl: 75 – 76. 
Kur'ani bai daidaita wanda yake da hali da wanda ba shi da shi ba, bai yarda da cewa ai tun da komai yana hannun Allah ne to babu wasu sabuba da suke da wani tasiri, sai ya yi nuni da tasirin matsayi da halin kowane mutum a cikin rayuwa da kuma rawar da kowanne yake iya takawa daidai gwargwadon yanayinsa. Muna iya duba lamarin ruwaya mu ga cewa ba ta takaita wannan lamarin da batun haihuwa ba, hatta da lamarin aure kansa wanda shi ne ta hanyarsa ake iya samun yaduwa da haihuwa sai musulunci ya sanya hankali kan lamarin, sai ya takaita wanda ba zai iya ba da yin hakuri. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Ya ku samari! Wanda ya samu iko daga cikinku ya yi aure, wanda kuwa bai samu iko ba to ya dimauci yin azumi domin azumi zai yi masa magani . Sai ya umarci samari da yin aure idan sun samu yalwa, ya kuma umarci wanda ba shi da yalwa da kamewa da yin azumi saboda yana raunana sha’awa. 
Tayiwu wani ya ce: To ai ayoyin Kur'ani da hadisai suna nuni ne zuwa ga daidaikun mutane cewa kowane mutum yana da ikon kaiyade iyali daidai gwargwadon yadda ya san cewa zai iya kokarin ganin ya dauki nauyin su a rayuwarsa, ba tare da ya takura kansa ba?!
Sai mu ce: Ai da ma muna son mu ce: Kowane mutum yana da iyakar da yake ganin zai iya faman daukar rayuwarsu don haka sai ya shirya wa rayuwar daidai gwargwadon yadda ya ga zai iya dauka, sai dai wannan ba ya hana gwamnatoci su shiga cikin lamarin idan ya kai ga wani yanayi na larura da ba zasu iya dauka ba. Idan al’umma ita ma ta ga ba zata iya daukar rayuwar mutanenta ba to ya hau kan ma’abota lamarin wannan al’ummar su dauki mataki a kai daidai gwargwadon yadda kasafin rayuwar al’ummar zai wadatar da ita. 
Kamar yadda muka yi nuni da cewa Kur'ani yana kallon rayuwa ta mahangar hakikanin abin da yake wakana ne bai yi watsi da wannan ba yayin da yake kafa dokokinsa. Kur'ani bai taba cire hannun mutum da tasirinsa wurin faruwar abubuwa a wannan duniya ba kamar yadda bai taba cire hannun dan adam wurin sakamakon da zai zo a lahira ba. Duba fadin Allah madaukaki cewa: "Hakika Allah ba ya canja wa mutane abin da yake gare su, har sai dai sun canja abin da yake gare su... ” (Ra'ad: 11). Wannan ayar kawai ta isa ta nuna mana cewa waccan maganar ta cewa Allah na nan shi zai yi komai ba tare da shi bawa ya dauki wani mataki ba babu wani asasi da take da shi!. 
Sau da yawa mutane sukan yi magana su ce: Allah ya kaddara ko ya hukunta, ko kuma Allah ya so, ko Allah ya yarda, ko kuma al’amarin Allah ne, da sauran kalmomi da suke amfani da su wajen bayanin wani abu da ya wakana, wannan al'amarin yana iya kasancewa mummuna ko kyakkyawa, sannan kuma yana iya kasancewa na halittawa ko na shar’antawa. Da wannan kawai sai su yanke hukunci cewa: Ai Allah da ya halicci mutum shi ne kuma zai ba shi abin da zai rayu. Wato bakin da Allah ya tsaga ba ya hana shi abin sawa!. Kuma abin da suke nufi a nan shi ne cire tasirin mutum a cikin abubuwan da suke wakana a rayuwa. Abin da masu wannan tunani suka manta shi ne shi ma matakin da dan adam yake dauka ana kirga shi a cikin kaddarawar Allah ne ba tare da ya cire masa zabin da ya ba shi ba ta yadda idan ya dauki mataki a rayuwarsa ko ya ki daukar matakin to duka biyun kaddarawar Allah ce bisa zabin dan'adam!. 
Wannan lamarin dai yana kama da shan magani ne ga marasa lafiya, ko yawaita istigfari ga mai son ya yi arziki, ko saukar ni’imar Allah ga al’umma idan ta yi imani ta yi takawa. Kuma muna iya ganin wannan a koyarwar musulunci a ruwayar Saduk a littafinsa "Attauhid” shafi na 369, yayin da imam Ali (a.s) yana tafiya ya kauce daga kusa da wani bango da ya karkace kamar zai fado sai wani ya ce masa: Ya Amirul muminin shin kana gudun kaddarar Allah ne? sai imam Ali (a.s) ya ce: "Ina gudu daga kaddarar Allah ne zuwa ga kaddarar Allah”! Shi ya sa muka ga ruwayar da take magana game da mutane biyar wadanda ba a karbar addu’arsu ya hada da wanda ya ga garu ya karkata zai fado bai kauce ba har ya fado masa (wannan yana kama da mai addu’a ne a kan wani al’amari amma bai dauki matakin da ya dace da shi ba don haka ba yadda za a yi ya ga kyakkyawar natija). 
Don haka batun cewa al’umma zata samu yalwa alhalin tana aiwatar da abin da ta so na yawaitar nauyi a kanta alhalin ba ta dauki wani mataki ba babu wata ma’ana gare shi kuma musulunci bai goyi bayan hakan ba. Musulunci ya kalli hakikanin rayuwa ne sai ya sanya dokokinsa yadda zasu dace da yalwa da walwalar dan adam. Wannan ne ya sanya zamu ga idan al’ummar kasa ta yi karanci to sai a kwadaitar da mutane su yawaita amma idan ta yi yawa kuwa sai a kwadaitar da mutane su karanta!. 
Amma mai ganin cewa tun da Allah ya kaddara adadin mutanen da zasu zo duniya to ko da kuwa an bi tsarin kaiyade iyali wannan dai adadin ne zai zo? Shi ma ana iya ba shi amsa da cewa: Ai rashin kaiyadewa da tsarawar iyali ko kaiyadewa da tsarawar duk wanda ya wakana yana daga abin da aka kaddara ne, duk biyun ba sa fita daga cikin kaddarawar Allah madaukaki!. Don haka daukar mataki da rashin daukar mataki ta janibin mutane ba ya fita daga kaddarawar Allah madaukaki. Sai dai idan suka dauki mataki sai Allah ya bayar da sakamakon matakin da suka dauka gwargwardonsa ta fuskacin ci gaba ne ko ta fuskacin ci baya ne!. Don haka Allah Madaukaki ya ajiye sabuban abubuwan da suke wakana a duniya kuma duk wanda ya yi riko da su zai samu sakamakon hakan daga gare shi ba tare da la’akari da addini, mazhaba, jinsi, launi, yare, yanki, da sauransu ba. 
A kan haka ne muke iya cewa; akwai hannun Allah a aiyukanmu duk da kuwa bai tilasta mu ba, wato da Ubangiji bai ba mu ilimi da hankali da karfi da iko da nufi da lafiya ba to da ba mu iya yin wadannan aiyukan ba don haka akwai hannunsa a cikin aiyukanmu, amma kuma bai tilasta mu ba saboda ya halicce mu tare da zabi, domin ba ma'ana ya ce mu yi sannan sai ya tilasta mu kan yi ko kan kin yi, ko kuma ya ce mu bari sannan sai ya tilasta mu kan bari ko rashin bari, domin idan ya yi hakan sannan sai ya azabtar da masu yi ko masu bari sabanin umarninsa ko haninsa kuma ya ni'imtar da masu yi ko masu bari bisa dacewa da umarninsa ko haninsa to wannan ya saba da hikimarsa. Kuma hankali ba zai gushe yana tuhumar rashin adalci a kan wannan ba alhalin Allah ya nisanta daga aikata haka, tsarki ya tabbata gare shi. 
Don haka ruwayoyin da suke cewa: "Alkalami ya bushe da abin da zai same ka ". Ko masu nuni da rubuta komai na ajali da arziki a cikin mahaifiya, ta yadda ko da saura zira’i daya ne ya mutu sai ya yi aikin ‘yan’wuta ko aljanna sai ya shige ta . Da masu nuni da cewa "Kowane mutum  ya yi aiki, domin kowanne an saukake masa abin da aka halitta shi dominsa ne" . Da ruwaya mai cewa: "Wadannan suna wuta ba ruwana, wadannan kuma suna aljanna babu ruwana". Duk ba sa cire sabuba da Allah ya sanya a cikin rayuwar mutane kuma ba sa cire tasirin halittu a cikin aiyuka duk da kuwa wasunsu mun rufe ido game da ingancinsu. 
Don haka tsara iyali wani abu ne da kowane mutum zai iya dubawa bisa yadda yake ganin ya gamsu da nauyin da zai iya dauka. Misali wani zai iya daukar nauyin ‘ya’ya masu yawan gaske, wani zai iya daukar hidima ga mutane 12 ne, wani kuma yana iya daukar nauyin mutane 6. Hankali da shari’a ba su hana mutum daukar mataki ba gwargwadon yadda ya ga zai iya, in ya so idan ya yi nasa to sai ya mika sauran lamari ga Allah. 
Amma shari’a da hankali ba su yarda da ta ci barkatai da sunan Allah na nan ba. Don haka ne shari’a da hankali zasu zargi mutumin da ya ajiye kudinsa a wajen kofar gida sannan sai ya ce: Allah yana nan. Da safe idan ya fito waje bai ga dukiya ba to shari’a da hankali zasu zarge shi domin suna umarni da yin tawakkali ne bayan daukar mataki!. 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: