bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:34:07
Har suna kafa hujja da maganar da Imam zainul Abidin (a.s) ga mutanen kufa inda yake cewa
Lambar Labari: 340
Da sunan Allah, mai rahama, mai jin qai, tsira da Amincin Allah su tabbata ga manzo, da Alayensa tsarkaka managarta.

A sakamakon yaduwar shubuhohin akan Imam Husaini (a.s) da ranar Ashura da qoqarin da wasu suka daukar ma kansu na canja tarihi, sai naga cewa yakamata in d’aukar ma kaina yin bayanin haqiqanin abinda ya faru.

Daga cikin shubuhar da yanzu ake yadawa akwai cewa:
1- (‘YAN SHI’A SU NE SUKA KASHE IMAM HUSAINI (a.s)!!!).
Har suna kafa hujja da maganar da Imam zainul Abidin (a.s) ga mutanen kufa inda yake cewa:
 أيها الناس ناشدتكم بالله هل تعلمون إنكم كتبتم إلى أبي وخدعتموه وأعطيتموه من أنفسكم العهد والميثاق والبيعة قاتلتموه.
سيرةالإمام الحسين. ج1,ص14.
Ya ku mutane ina hadaku da Allah shin kun san cewa kune kuka rubuta wa mahaifina-cewa ya zo ku taimake shi- kuma kuka yaudare shi, kuma kuka masa Al-qawarin kanku da mubaya’a amma kuka yaqe shi.
Siratul imamul husaini. Juz’i na 1, shafi na, 14.

Amsa:
Da farko dai kashe Imam Husaini (a.s) ya gudana ne akan umurni wanda ya gangaro daga Yazidu (L) zuwa ga gwamnansa Ubaidullahi bin ziyaad, zuwa ga kwamadansa Umar bin Sa’ad, kamar yadda zamu iya gane hakan a cikin wannan jumla cewa:
ومجموعهم اثنان وسبعون رأسا، وذلك أنه ما قتل قتيل إلا احتزوا رأسه وحملوه إلى ابن زياد، ثم بعث بها ابن زياد إلى يزيد بن معاوية إلى الشام.
البداية والنهاية. ج,8, ص,206.
Kawuna saba’in da biyu ne cikarsu, saboda ba a kashe wani ba face sai da aka yanke kansa aka kaiwa dan ziyaad (Ubaidullahi) sannan shi kuma ibni ziyaad ya tura da kawunan zuwa ga yazidu dan mu’awuya a sham.
Al-bidaaya wanni haaya. Juz’i na,8, shafi na,206.

 Abin da zamu iya fahimtar daga bayanin Al-hafiz ibni kathir wanda muka kawo yanzu shi ne Ubaidullah bin ziyaad ya kashe Imam Husaini ne a kan umurni daga yazidu shi ya sa ma ya tura masa da kawunan don ya gani cewa ga shi an aiwatar da umurnin da ya bayar.
Ta yiwu wani ya ce ai har yanzu dai ba a bada Amsar ba don idan ba ‘yan shi’a ne suka kashe Imam Husaini (a.s) ba to me zai sa Imam Zainul Abidin ya ce wa mutanen kufa (ku kuka kira babana kuma kuka yaudare shi kuma kuka yaqe shi?)
Amsa:
Da farko  dai babu wani dalili akan cewa wadanda suka rubuta wasikqa zuwa ga Imam Husaini (a.s) ‘yan shi’a ne, sannan kamar yadda muka tabbatar a baya cewa kisan ya kasance ne a kan umarni daga yazidu zuwa ga gwamnansa  ubaidullahi bin ziyaad zuwa ga kwamandansa umar bin sa’ad, wanda babu wani dalili akan cewa yazidu da ubaidullah da umar bin sa’ad ‘yan shi’a ne!!!, tambayar da za a iya yi shi ne to wadanda suka rubuta wasiqa zuwa ga Imam husaini ‘yan mene ne idan ba ‘yan shi’a bane? Kuma ina su ‘yan shi’ar suke?
Amsa:
   Wadanda suka rubuta wasika zuwa ga Imam Husaini (a.s) sun hada da:
1-wadanda suka gaji da zaluncin da banu Umayya suke yi.
2-masu ganin cewa Imam Husaini (a.s) aqalla ya fi yazidu(L).
3-masu raya son Imam Husaini (a.s) a zuci amma takobinsu na kan Imam husaini (a.s) kamar yadda ya zo cewa Imam Husaini (a.s) ya tambayi wani mutum:
.
فقال له الحسين: كيف خلفت الناس بالعراق ؟ قال: خلفتهم، وقلوبهم معك، وسيوفهم عليك.
الأخبار الطوال. ج,1,ص,245.
Sai Husaini ya ce masa yaya ka bar mutanen Iraq? Ya ce: na barosu zuciyarsu tana tare da kai amma takobinsu yana kanka.
Akh’baard diwaal. Juz’i na, 1, shafi na 245.

Sai dai abin da ta yiwu wani zai tambaya shi ne, shin wadannan kashi na ukun ba sune ‘yan shi’a ba? Sannan su kuma ‘yan shi’an ina suke?
Amsa:
Don mutum kawai ya ji yana son Imam Husaini (a.s) baya mai da shi dan shi’a kyakkyawar misali anan shi ne yanzu mutanen da suke son Imam husaini wadanda ba ‘yan shi’a ba suna da yawa, sannan batun cewa Ina ‘yan shi’a suke har suka bari aka kashe Imam Husaini (a.s) ba su taimake shi ba?
Amsa:
Wasu daga cikinsu an kashe su kamar irinsu Hani bin Urwa wasu kuma daga cikin ‘yan shi’an suna kurkuku kamar irin mukhtaar bin yusifus saqafi kamar yadda ya zo cewa:
فخرج من السجن المختار، وقد التف عليه خلق من الشيعة.
تاريخ الإسلام للإمام الذهبي. ج,5, ص,50.
Sai mukhtaar ya fita daga kurkuku, sai gungu na ‘yan shi’a suka taru a gunsa.
Tarikhul islam na Imamuz zahabiy. Juz’i na, 5, shafi na, 50.

Sannan bayan fitowan Mukhtaar daga kurkuku da haduwan gungun ‘yan shi’a a tattare da shi, sai mukhtar ya bi wadanda suka kashe Imam Husaini (a.s) daya bayan daya ya kashe su kamar yadda ya zo cewa:

وقد شرع المختار في تتبع قتلة الحسين ومن شهد الوقعة بكربلاء من ناحية ابن زياد، فقتل منهم خلقاً كثيراً، وظفر برؤوس كبار منهم، كعمر بن سعد بن أبي وقاص أمير الجيش الذين قتلوا الحسين، وشمر بن ذي الجوشن أمير الألف، الذين وَلُوا قتل الحسين.
الدولة الأموية عومل الإزدهار وتداعيات. ج,2, ص,421.

Sai mukhtaar ya fara bibiya wadanda suka kashe Imam daga cikin wadanda suka halarci waqi’ar karbala, daga bangaren dan ziyaad (Ubaidullah) sai mukhtaar ya kashe jama’a da dama daga cikinsu, kuma har ya ci nasarar yanke kan manya daga cikinsu, kamar umar bin Sa’ad bin Abi waqqaas wanda shi ne kwamandan rundunar da suka yaqi Imam Husaini (a.s), da kuma Shimr bin ziy jaushan wanda shi ne kwamandan mutane dubu na wadanda suka jibinci kashe Imam Husaini (a.s).
Addaulatul Umawiyya Awaamilul izdihaar wa tadaa’iyaat, juz’i na, 2, shafi na, 421.

A biyo mu a karo na gaba don Amsa wata shubuhar.
Wassalamu Alaikum warahmatullahi wa barakaatuhu.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: