bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:35:37
Da farko dai ina so in bada Amsa ne akan shubuha ta farko wato (sanya baqaqen kaya) da ta biyu (yin kuka a ranar Ashura) amma shubuha ta ukun (yanka jiki a ranar Ashura)
Lambar Labari: 341
Da sunan Allah, mai rahama, mai jin qai, tsira da Amincin Allah su tabbata ga manzo, da Alayensa tsarkaka managarta.

A sakamakon yaduwar shubuhohin akan Imam Husaini (a.s) da ranar Ashura da qoqarin da wasu suka daukar ma kansu na canja tarihi, sai naga cewa ya kamata in d’aukar ma kaina yin bayanin haqiqanin abubuwanda suka faru.

Daga cikin shubuhar da yanzu ake yadawa akwai cewa:
2-ME YA SA ‘YAN SHI’A SUKE:
a)    sanya baqaqen kaya aranar Ashura?
b)    Yin  Kuka a ranar a ranar Ashura?
c)    Yanka jikinsu a ranar Ashura?

Amsa:
Da farko dai ina so in bada Amsa ne akan shubuha ta farko wato (sanya baqaqen kaya) da ta biyu (yin kuka a ranar Ashura) amma shubuha ta ukun (yanka jiki a ranar Ashura) bana so in ce komai a kai sakamakon cewa ba dukkan ‘yan shi’a ne suke da Aqidar yin hakan ba, kuma tunda ni bana daga cikin wadanda suka tafi akan yin hakan ba zan daukar ma kai na karewa ba, amma sauran abubuwa biyun watau (sanya baqaqen kaya ranar Ashura) da (yin kuka a ranar Ashura) dukkan ‘yan shi’a- har da masu yanka jikkunansu- suna da Aqidar yin hakan, kuma ni ina daga cikin masu yi, don haka nake so in tabbatar da samuwarsu a musulunci, a yayin da wasu kuma suke ganin cewa mun kauce hanya,
Masu ganin cewa mu ‘yan shi’a mun kauce hanya suna kafa hujja ne da hadisin da Imam Aliyu (a.s) cewa:

  قال أميرالمؤمنين(عليه السلام): لا تلبسوا السواد، فإنّه لباس فرعون.
مستدرك سفينة البحار. ج,5,ص,278.
Shugan muminai Aliyu (a.s) ya ce: kada ku sanya baqin kaya, saboda baqin kaya tufa ne na Fir’auna.
Mustad’raku safinatul bihaar. Juz’i na 5 shafi na 278.

Sai dai  masu kafa hujja da ire iren wannan Hadisan sai muce masu:
عرفتم شيأ وغابت عنكم أشياء.
Kun san wani abu, amma wasu abubuwa sun shige maku duhu.
Domin wannan hadisi da muka kawo a kwai hadisin da ya qayyede shi, kuma kamar yadda duk wanda ya karanta Ulumul Qur’aan ya san Aya tana qayyade Aya, haka ma wanda ya karanta Ulumul Hadis ya san hadisi yana qayyade hadisi, kamar yadda zamu iya gani a wata Aya Allah yana cewa:(أقيموا الصلاة)  (ku tsaida salla) amma ba a yi bayani akan lokutan da za a tsaida sallar ba, wannan Ayar ita ake kira da (MU’DLAQA) sai kuma aka samu wata Ayar kuma ta zo ta yi mana bayanin lokutan da za a tsaida sallolin inda Allah ke cewa:
(أقم الصلاة لدلوك الشمس إلى غسق اليل وقرآن الفجر...)
(ka tsaida salla lokacin zawalin rana, zuwa rabin dare, da sallan Al-fijir...).
Wanda acikin wannan Ayar ce aka samu lokuta uku na salla, 1-Dulukish shams, wanda shi ne lokacin sallar Azahar da la’asar, 2-Gasaqillail, wanda shi ne lokacin sallar mag’rib da Ishaa’i, 3-Qur’anul fajr, shi ne lokacin sallar Asuba, wannan Ayar da ta ambaci lokutan salloli ita ake kira da (MUQAYYADA) saboda ita ce ta Qayyade  Ayar da ta gabata, duk da ba a jere a guri daya suke ba.
To haka ma Hadisin da ya gabata akwai hadisan da suka Qayyade shi da cewa  banda ranar Ashura, watau sanya Baqaqen kaya a ranar Ashura babu matsala ba kuma kamanceceniya da Fir’auna ba ne, ga zancen daga cikin littafin da ya naqalto cewa baqaqen tufafin fir’auna ne, amma akan batun Imam husaini (a.s) ya nuna cewa ba matsala, ga zancen kamar haka:

ذمّ لباس السوداء. تقدّم في «سود»: لبس السواد في مأتم الحسين(عليه السلام).
مستدرك سفينة البحار. ج,9,ص,220.
An zargi sanya baqin tufa, amma ya gabata cewa a sanya baqin tufa a taron imam Husaini (a.s).
Mustad’raku safinatul bihaar. Juz’i na 9 shafi na 220.

Sai wani hadisin shima kamar haka:
وعن الحسن بن ظريف بن ناصح، عن أبيه، عن الحسين بن زيد، عن عمرو بن علي بن الحسين قال: لما قتل الحسين بن علي (عليه السلام) لبس نساء بني هاشم السواد والمسوح وكن لا يشتكين من حر ولا برد، وكان علي بن الحسين (عليه السلام) يعمل لهن الطعام للمأتم.
وسائل الشيعه لحر العاملي.  جزء 3 / صفحة (238).
Da ga hasan bin zarif bin naasih, daga babansa, daga husaini bin zaid, daga Amru bin Ali binil husaini yace: a yayin da aka kashe Husaini dan Ali (a.s) matan banu hashim sun sanya baqaqen kaya maras kima, kuma basu kasance masu damuwa da zafi ko sanyi ba, sai Ali dan Husaini (a.s) yana dafa masu abinci na zaman makokin da suke yi.
Wasaa’ilush shi’a na hurrul Amuli, juz’i na 3, shafi na 238.
  Saboda haka masu ganin cewa: mun kauce hanya yana da kyau su san cewa muna da dalilai da hujjoji na abubuwan da muke yi.

Amma maganar kuka da muke yi akan Imam husaini (a.s) da farko dai muna so mu tabbatar wa mutane cewa: musulmai sun ginu a kan kuka idan aka yi masu rasuwa, ga misali kadan daga ciki:
حدثني يونس قال أخبرنا ابن وهب قال أخبرنا يونس بن يزيد عن ابن شهاب قال حدثني سعيد بن المسيب قال لما توفي أبو بكر رحمه الله أقامت عليه عائشة النوح فأقبل عمر بن الخطاب حتى قام ببابها فنهاهن عن البكاء على أبي بكر فأبين أن ينتهين فقال عمر لهشام بن الوليد ادخل فأخرج إلي ابنة أبي قحافة أخت أبي بكر فقالت عائشة لهشام حين سمعت ذلك من عمر إني أحرج عليك بيتي فقال عمرلهشام ادخل فقد أذنت لك فدخل هشام فأخرج أم فروة أخت أبي بكر إلى عمر فعلاها بالدرة فضربها ضربات فتفرق النوح حين سمعوا ذلك.
تاريخ الطبري. ج,2,ص,350.
Yunus ya bamu labari yace ibni wahab ya ce yunus bin yazid ya bamu labari daga ibni shihaab ya ce sa’id binil musayyib ya ban labari ya ce: lokacinda Abubakar ya yi wafati Aisha ta tsayar masa da zaman makoki, sai Umar dan khaddaab ya zo kofar gidanta, sai ya hanasu kuka akan Abubakar sai suka qi su daina, sai Umar ya ce ma Hishaam binil walid ka shiga ka fito min da ‘yar dan Quhaafa ‘yar uwar Abubakar, sai Aisha ta ce ma Hishaam a yayin da ta ji Umar ya fadi haka, ban yarda ka shiga gida na ba, sai umar ya ce ma hishaam shiga ni na maka izini, sai hishaam ya shiga ya fito da ummu farwa ‘yar uwar Abubakar, sai ya lakkada mata duka da bulala ya yi mata shegen duka, da sauran masu kukan suka ji haka sai suka watse.
Tarikhud dabari. Juz’i na 2, shafi na 350.
Dukda tsananin umar akan yin kukan mutuwa amma da khalida ya rasu ya bar mata sunyi kukan, watau ina nufin cewa shima a qarshe ya canja ra’ayinsa na rashin yin kuka ga mamaci, kamar yadda zamu iya gani a cikin wannan zance:
وقال عمر دعهن يبكين على أبي سليمان هو خالد بن الوليد.
مقدمة فتح الباري. ج1,ص,266.
Sai umar ya ce barsu (watau matan da suke kukan kenan) su yi kukansu akan Abu sulaiman wanda shi ne khalid bin walid.
Muqaddimatu fatahul baari. Juz’i na 1, shafi na, 266.

Wannan kenan sai kuma kukan da manzo (s.a.w) ya yi akan Imam husaini (a.s) wanda littaffan dukkan musulmai suka kawo, ga kadan daga cikinsu:

وقال الامام أحمد: حدثنا محمد بن عبيد، ثنا شراحيل بن مدرك، عن عبد الله بن يحيى، عن أبيه أنه سار مع علي  فلما جاؤوا نينوى وهو منطلق إلى صفين
فنادى علي: اصبر أبا عبد الله، اصبر أبا عبد الله، بشط الفرات قلت: وماذا تريد ؟ قال: " دخلت على رسول الله صلى الله عليه وسلم ذات يوم وعيناه تفيضان فقلت: ما أبكاك يا رسول الله ؟ قال: بلى، قام من عندي جبريل قبل، فحدثني أن الحسين يقتل بشط الفرات، قال فقال: هل لك أن أشمك من تربته ؟ قال: فمد يده فقبض قبضة من تراب فأعطانيها فلم أملك عيني أن فاضتا ".
البداية والنهاية.ج,8, ص,217.
Imam Ahmad (bin hanbal) ya ce: muhammad bin ubaid ya bamu labari, sharaahil bin mudrak ya bamu labari, daga Abdullahi bin yahya daga babansa cewa ya tafi tare da Aliyu (a.s) zuwa NAINAWAA, a yayin da zai tafi yaqin siffin, sai Aliyu (a.s) daga murya ya kira ya ce:haquri yaa Abaa Abdallah, haquri yaa Abaa Abdallah (wato imam husaini (a.s) a gaa6an teku, sai nace me kake nufi? Ya ce: na shiga wurin manzo (s.a.w) wata rana, sai nasamu idanuwansa suna zubar da hawaye, sai na ce manzon Allah me ya sanya ka kuka? Ya ce: dazu jibril ya tashi a guri na, sai ya bani labari cewa lallai husaini za a kashe shi a gaa6an teku ya ce sai yace: ba na kawo maka qasar wajen ka shinshina ba? Ya ce: sai ya miqa hannunsa sai ya damqi damqa daga qasar, sai ya bani ita, sai na gaza mallakan idanuwana don hanasu kuka.
Al-bidaaya wanni haaya. Juz’i na 8, shafi na 217.

Don haka ne ‘yan shi’a muke ganin cewa: Idan har Ummul muminina Aisha za ta sanya a yi zaman makoki na mutuwan mahaifinta, kuma umar zai ce a bar mata suyi kukan mutuwan khalid, kuma manzo (s.a.w) zai yi kuka akan husain (a.s) to yin kuka akan Imam Husaini (a.s) SUNNA CE.
A qarshe ina cewa a biyomu a bahasi na gaba don bada Amsar wasu shubuhohin.
Wassalamu Alaikum warahmatullahi wabarakaatuhu.





    

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: