bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:37:07
Allah ya kaimu gari karbala Al`muqaddasa. Amma abun la`akari a hanyar karbala shine tun daga Najaf zuwa karbala haya ce miqaqqiya sambal, sannan hanyoyi ne
Lambar Labari: 342
Da sunan Allah, mai rahama, mai jin qai, tsira da Amincin Allah su tabbata ga manzo da Iyalen sa tsarkaka, managarta.
A cigaba da kawo tsarabar Karbala, Na tsaya ne a inda muka je muka kwana, don washigari, mu dauki harama zuwa Karbala.
Washi gari bayan mun karya kumallo a garin Najaful Ash`raf, sai muka kama hanya domin yin tattaki daga nan garin Najaful Ash`raf zuwa  garin karbalal muqaddasa, wanda tafiya ne da ya kai kimanin kilo mita 90 kuma munyi wannan tafiyar ne a cikin kwana ukku, ga yadda tafiyar ta kasance:
A ranar farko ne bayan mun tashi da  misalin karfe 9:00 na safe, bamu tsaya ba sai da mukayi tafinyar da ta kai kimanin kilo mita 15 zuwa 20 sai muka isa masauki, mukayi salla, mukaci Abinci, bayan mun huta, da kimanin karfe 3:00 sai muka kama hanya muka yi tafaiyar da ya kai kimanin kilo mita 15 har muka isa masaukin da a gunne za mu kwana, bayan mun kwana, washi gari  mun karya, sai muka dauki harama muka sake irin tafiyar a baya mukayi, a rana ta biyu, da rana ta  ukku, har Allah ya kaimu gari karbala Al`muqaddasa. Amma abun la`akari a hanyar karbala shine tun daga Najaf zuwa karbala haya ce miqaqqiya sambal, sannan hanyoyi ne guda hudu biyu na masu tattaki, biyu kuma na masu mota, sannan baza ka taba yin takun da ya kai goma ba tare da kaga tanti na mutane a gefen titi ba, wadannan mutane da suke da tanti a gefen titi aikinsu shine:  wasu sun dora ma kansu shayar da masu zuwa ziyara shayi, wasu kuma sun dora ma kansu dafa Abinci don bada masu tattaki zuwa ziyara, wasu kuma sun  dora ma kansu sanya wakokin ta`aziyya na Imam Husaini (a.s), wasu kuma suna dora ma kansu yin bayanin falalar zuwa ziyarar Imam Husai (a.s) wasu kuma sun dora ma kansu yin bayanin Ladubban ziyarar Imam Husaini (a.s), wanda suke bayani wa mata cewa dole ne su kula da Hijabi, a yayin da wasu kuma sun dora ma kansu kula da lafiyan masu zuwa ziyara ne kawai, kamar yadda a baya na yi bayanin tanti lallai wadansu suna da teburi ne, wasu kuma suna da tanti ne, wasu kuma gini ne sukayi mai dauke da dakuna na yin barci da kicin da ban daki, wanda a cikin su ne muka kwana.
Amma dangane da masu tattaki kuwa, lallai a wannan tattaki ba`a bar Malamai, da dalibai, da ma jahilai a baya ba, don kuwa a cikin tawagarmu Akwai babban Arifin nan mai suna Ayatullahi Tahariri, wanda ya kai kimanin shekaru kusan 70, amma haka ya taka da kafafuwarsa masu girma tun daga  garin Najaf madaukakiya, zuwa karbala mai tsarki, sannan ba`a bar tsofi, da mata, da yara  a baya ba, don ni ganin idona naga wacce ta kai shekaru akalla 85 don a duke da kuma da sanda take tafiya, itama ba`a barta a baya ba, hakama naga yaro dan shekaru 3 shima ba`a barshi a baya ba.
Amma dangane da maziyartan kuma, sai ince daga Qasashe kimanin 50 ne mutane suka samu damar zuwa, kasashen da suka hada da: Amerika, Ingila, jamani, chaina, turkiyya, indiya, fakistan, tajkistan, Azarbajan, ozbakistan, saudiyya, Iran, bahrain, yaman, falastin, Nijeriya, nijar, sahilil aj, borkina faso, juzurul qamar, miyan mar, da sauran su.
Amma Adadin wadan da suka halarce wannan taro sun kai kimanin mutane miliyon 16 zuwa miliyon 17 wanda ya ninka masu aikin Hajji sau 5.
Kamar yadda a baya nayi bayani cewa: wasu daga cikin mutanen kasar Iraq, musamman  wadan da suke kusa da garin karbala, sun kafa tanti don ciyar da maziyarta, to lallai sun kasance ne suna tsayawa ne a gefen titi don roko da hada masu ziyarar da Allah don su Amince su ci abincin da suka dafa, wasu kuma ba dafafen  Abinci suke badawa ba, suna bada tuffa ne, wasu kuma suna bada lemo, wasu kuma suna raba lemon kwalba, bayan mun shafe kilo mitoti kamar 90 ne muka isa zuwa garin karbala  Almuqassa.
Abiyomu nan gaba don cigaba.
Wassalam.     


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: