bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:38:08
`yan tawagarsa ba sai dai ya tsinci kansa a wata tawagar ta daban, haka dai muka cigaba da kutsawa har muka isa kusa gunda Sayyida zainab (a.s)
Lambar Labari: 343
A cigaba da kawo tsarabar karbala, na tsaya ne a in da muka isa garin karbala mai tsarki.
Lallai mun isa garin karbala ne gab da magriba, duk da mun isa ne kwana biyu kafin Arba`in, amma sai gashi mun samu garin karbala ba masaka tsinke, shigarmu garin ke dawuya sai muka hangi kubbar haramin Imam Husaini (a.s) a yayin da muke tare da malam Hasan Adam, a gefen mu kuwa sai wani sayyid daga cikin `yan tawagarmu ya fashe da kuka ai sai na gefensa ma ya buge da kuka, nikuwa sai na kama karanta ziyarar Arba`in karewana ke da wuya sai naga har munyi kusa da haramin, a yiyin da ko ina ya cika da wakokin Ta`aziyyar Imam Husaini (a.s) sannan ta kowanne titi da lungu jama`a ne iya kallonka, wanda idan mutum bai dage ya tafi tare da `yan tawagarsa ba sai dai ya tsinci kansa a wata tawagar ta daban, haka dai muka cigaba da kutsawa har muka isa kusa gunda Sayyida zainab (a.s)ta tsaya ta yi khuduba ga mutanen kufa, sai kaga wurin ya yake musamman ma idan dare yayi, su kuma maukibobi daban daban dake dauke da wakoki daban daban suna shigowa cikin gari don suje su samu masauki kafin ranar Arba`in, haka dai muka isa zuwa masaukinmu wanda kusa yake da haramin, wanda bani tsammanin yakai taku 30 daga gun da muka sauka zuwa cikin haramin, bayan kowa ya sami wurin kwanciya, sai mukayi salla tare da limanci Ayatullahi tahariri, bayan mun idar da salla ne, sai muka ci Abinci wanda Aka karbo ne daga haramin Abul fadlil Abbas, a nan ne mu uku ni da malam Hasan da malam Aminu mukayi ittifaqi cewa zamu yi barci da wuri don mutashi da daddare kamar karfe 2:00 tayiwu a lokacin jama`a sun ragu don muna so bayan munyi ziyarar kuma sai mu taba jikin karfe kabari do neman tabarruki, hakan kuwa akayi kimanin karfe 2 da motsi sai naji malam hasan na kirana, sai na tashi na yi Alwala muka kama hanya mu 3 isarmu ke da wuya sai na tsaya a farfajiyar haramin musammanma da yake mun shiga ne ta (Babur ra`as) watau kofar da aka shiga da kan Imam Husaini (a.s), amma dukda munje ne da misalin karfe 2 da motsi amma fa saman `yan yatsuna 2 ne kawai suka iya taba jikin haramin sabo da yawan jama`a, haka dai bayan munyi ziyara muka dawo gida. Washi gari kuwa mun fita, da ni da malam hasan, da malam sa`id, da malam husain, don muje haramin Abul fadlil Abbas, amma a hanya muka yanke shawarar cewa ba dole sai mun shiga cikin haramin ba, sabo da yawan mutane zai yi wuya a ce mun samu damar kutsawa, don haka ko da isarmu kusa da kofar haramin sai muka karanta ziyararsa ba tare da mun shiga cikiba, bayan mun gama mun dawo gida mun kwana, haka ma washi gari sabo da yawan jama`a na samu damar yin ziyarar ne kawai  a waje ban samu damar taba karfen jikin kabarin Imam ba, a yayin shi kuma malam Hasan ya samu damar tabawa kai harma ya sanya aikan da aka bashi, amma ranar Arbain wannan shine ma ranar da akafi ko wanne rana cika sabo da yawan jama`a, a wannan ranar kam Tawagarmu da yake zagayawa zamuyi kafin muje hama, ai ko kusa da jikin haram bamu kai ba sabo da yawan jama`a, a karshe dare ya kusan yayi, sai muka komo gida, sai aka sanar da mu cewa washi gari ranar jumma`a zamu tafi a tawaga zuwa haramin  Abul fad`lil Abbas, bayannan, sai mu dawo zuwa masallacin jumma`a wanda ke gefen haramin Imam husain (a.s), hakan kuwa ya faru. Ya dan uwa in taqaita maka na samu damar shiga in taba jikin barin Imam husaini kamar yadda nake so kuma kamar yadda ya kamata ne a ranar da zamu bar garin karbala, bayan harma mun shirya kayayyakinmu, sai na fita ni kadai nayi kamar zanje sayar wani abu ne, daga nan sai naje nayi bana kwana da Imam, lallai na taba jikin karfen kabarinsa mai Albarka da hannayena biyu wadanda ba wai sunkai matsayin yin hakan bane, kuma ina shaida wa `yan uwa cewa sam ban barsu ba a cikin Addu`oina.
A karshe ina mai cewa: a biyomu a nangaba don cigaba.
Wassalam.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: