bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      21:38:55
Maganar son Addini kuma da nace mutanen qasar suna yi, dalilina shine idan kaje za kaga lallai suna matuqar qoqari wajen d'abbaqa shi'ancin yadda ya kamata ta yiwu sirri anan shine miqa wuya ga marja'iyya da sukeyi
Lambar Labari: 344
Da sunan Allah, mai rahama, mai jin qai, tsira da Aminci su tabbata ga manzo, da Alayensa tsarkaka managarta.
A cigaba da kawo tsarabar karbala nake cewa akwai abubuwan da tun shigarmu qasar ta Iraqi na zuwa fitarmu yi mulahaza,  wad'annan abu masu mahammanci kuawa shine:
1-Matuqar tsaro da kasar ke dashi.
2-Son Addini da mutan qasar ke dashi.
3-Girmama bakon Imam Husaini (a.s) da mutanen qasar keyi.
Maganar tsaro da nayi, lallai tun sa qafarmu a cikin kasar ya kasance motocin yaqi ta sojoji ke gabanmu da bayanmu har muka isa masaukinmu, sannan ko wanne madakata idan muka isa sai anyi cekin, da na'ura mai sunsuna makami tun daga nesa, haka abin yake har muka dawo, sannan sabo da rashin Aminci ya hana akaimu wasu wuraren, kamar KAZIMAIN da SAMARRA sakamakon rashin cikekken Amincin hanyar da ba'a dashi.
Maganar son Addini kuma da nace mutanen qasar suna yi, dalilina shine idan kaje za kaga lallai suna matuqar qoqari wajen d'abbaqa shi'ancin yadda ya kamata ta yiwu sirri anan shine miqa wuya ga marja'iyya da sukeyi.
Sai maganar girmama baqin Imam (a.s) da nace mutanen qasar suna yi, wannan ya bayyana acikin bayanai na, kamar yadda nace za kaga sun fito kan titi suna had'a ka da Allah akan kayarda ka kar'ba abinda suka dafa, kuma suna da Aqidar cewa amatsayinka na bakon Imam Husain (a.s) idan har ka karba abinda suka dafa sun cimma burinsu don hakan zai faranta wa Imam Husaini (a.s) rai.
Akarshe ina cewa: Ya Aba Abdillah, wannan shine Alqawarin da ke tsakani na da kai.
ولا جعله الله آخرالعهد مني لزيارتكم.
ولسلام عليكم ورحمة الله.  

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: