bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2018      22:08:24
Bayan haka: hakika zabar aboki ko abokiyar tarayya wani abu ne da ke motsawa cikin zuciyar dukkanin matashi da matashiya da suka isa aure suka kai ga nunar hankali da tunani
Lambar Labari: 349
kada kuyi gaggawa cikin zaben wadanda zaku aura
 Ina farawa da sunan ubangiji mahaliccin dukkkanin halittu tsira da aminci su kara tabbata da dawwama ga fiyayyen halitta Muhammad da iyalansa tsarkaka

 Bayan haka: hakika zabar aboki ko abokiyar tarayya wani abu ne da ke motsawa cikin zuciyar dukkanin matashi da matashiya da suka isa aure suka kai ga nunar hankali da tunani, wannan zabe yana bukatuwa zuwa ga dogon bincike da zurfafa tunani domin kansa ne samun farin ciki cikin baki dayan rayuwarsa ya dogara, tunanin yaya zan zabi abokiyar zama ko abokin zama na, hakan yana dimauta dukkanin masu niyyar aure, wadannan sharudda da siffofi suka zama lazimi dole abokin tarayya ta ya cika gabanin zabarsa ko zabarta, wanne abu ne ma'auni da sikeli cikin zabar abokin zama, wanne matakai na larura da rayuwa auratayya za ta doru kansu?

Domin samun amsoshin wadannan tambayoyi zamu tuntubi janaral sakatare na Hizbulllahi Lubnan Shaik Na'im Kaseem

Yaya shari'ar muslunci ta ke kallon mafhumin aure?
 Ayar kur'ani mai girma ta tattaro gamammiyar fuskanta da muslunci ya shata ta cikin batun aure:
 (ومن آياته أن خلق لكم من أنفسكم أزواجاً لتسكنوا إليها وجعل بينكم مودة ورحمة إن في ذلك لآيات لقوم يتفكرون)
Daga cikin ayoyinsa ya kagar muku da matayen aure domin ku samu nutsuwa garesu ya kuma tsakaninku ya sanya kauna da rahama lallai cikin hakan akwai aya ga mutanen masu tunani.
Hakika na karkasa unwanul am zuwa mihwari uku: na farko: kowanne daya cikin biyun ya fara sanin cewa halittarsa bata da banbanci da ta dan'uwansa a wurin Allah ta'ala, sannan wajibi kowannensu ya la'akari da cewa yana zaune da mutum ne da yake tattare da siffofin mutum na gamagari.
Mihwari na biyu: cikin wannan mihwari yayi bayanin hadafin yin aure, shine cewa miji ya samu nutsuwa da matarsa ita ma haka ta nutsu da mijinta da ma'anar samun kwanciyar hankali, wannan yana bukatar a samu kauna da jin kai a tsakanin juna.
Mihwari na uku: shine fadinsa madaukaki:
 (إن في ذلك لآيات لقوم يتفكرون)،
Lallai cikin hakan akwai ayoyi ga masu tunani.
Sannan bugu da kari cikin hakan akwai kira ga mutum da yayi tunani ya tabbatar ya samu cikakken sani da tsinkayar hakika dangane da aure da dabi'unsa da haduffansa, saboda idan ya samu fahimtar ma'anar aure to hakan zai bashi damar tsara abinda ya kamata, sai dai cewa idan bai zurfafa tunani kan abinda Allah maduakaki ya halitta da kuma abinda ya hukunta kanshi ba to zai rayu cikin raurawa da rashin nutsuwa.
Saboda haka wadannan sune mihwarori na gaba-gaba cikin samun ingantacciyar zamantakewar auratayya da kyakkyawar makoma, sai dai cewa kafin aure mene ne ma'aunai cikin zaben aboki ko abokiyar zama da siffofinsu da kuma abinda shari'ar muslunci ta yi bayani da hadisan Imamai (as) ?
Riwayoyi sun tattaro wasu adadin unwanai sun kuma iyakance su cikin unwani biyu na tushe:
Unwani na farko shine riko da addini, unwani na biyu kyautata zamantakewa da juna, saboda wannan ne ma manzon Allah (s.a.w) ya zantar damu wadannan siffofi biyu, riwayar ta ambaci cewa akwai wani mutum ya zo wajen Imam Bakir (as)  ya bashi labarin kan irin wahalar da yake ciki da tsanani wajen samawa diyarsa miji, sannan ya ambaci sifofin da suka dabbaku kansa matsayinsa na uba ya kuma fatan ace irin wadannan siffofi ko da kadan sun dabbaku kan wanda zai bawa diyarsa, sai Imam (as) ya bashi amsa da cewa na fahimci dukkanin lamarin diyarka lallai ka sani cewa ba zaka ka samu mutum misalinka ba, saboda ka daina duba cikin hakan, Allah yayi maka rahama, ka sani lallai manzon Allah (s.a.w) yace:  
«إذا جاءكم من ترضون خلقه ودينه فزوجوه، وإلّا تفعلوه تكن فتنة في الأرض وفساد كبير».
Idan mutumin da kuka yadda da addini da dabi'unsu ku aurar masa, idan kuka ki yin hakan fitina da fasadi  mai girma zasu afku ban kasa.
Amma me ya sanya wadannan sharudda biyu suka banbanta da ba'arinsu tareda ilimi.
Shin riko da addini ya kunshi kyawawan dabi'u? sakamakon yayi nufin bayyana mana cewa abin bukata shine sauya riko da addini da bayyanar da shi cikin alakar ma'aurata ta yau da gobe, riko da addini bai wadatarwa cikin fatar baki kadai da da'awa ko kuma cikin tara kakkausan gemu da yawan sallah da azumi, saboda miji nagari shine wanda wadannan sharudda biyu ke tabbatuwa cikinsa, sai dai cewa ya zamo dole mu waiwayi takalifin miji da rawarsa cikin abinda ya rataya da ciyar da iyalinsa da tsayuwa kan jagorantar iyali, wadannan al'amura ne biyu cikin da'irar wajiban da suke kan miji
* عن الرسول (ص) أنه قال: الكفوء هو من يكون عفيفاً وعنده يسار،
Ankarbo daga manzon Allah (s.a.w) yace: tsara cikin aure shine wanda a kasance mai kame kai kuma mai yalwar hannu (iko).
Ta yaya wannan riwaya za tai mana bayanin wannan lamari?
Wannan riwaya tana jan hankali zuwa ga ikon namiji kan ciyarwa, saboda mas'alar bata takaita cikin kyawunta zamantakewar aure cikin da'irar kyawun dabi'u ba kadai ko kan mutumin da ya fifita da kebantattun siffofi ba, ya zama dole kari kan wadancan siffofi nasa ya kasance yanada wani aiki da yake yi da zai dauke hidimar iyalinsa, ta yanda iyalinsa ba zasu ga gazawarsa ba kan hidimar iyali, a wannan wuri ya kamata mu jawo hankali da a gane cewa abinda ake nufi iko shine samun ikon ciyarwa.
Mene ne bayani dangane da ma'aunai na hankali da gangar jiki wadanda ake ganinsu matsayin abubuwa masu muhimmanci cikin gina iyali masu lafiyar hankali?
A dabi'ance, akwai wasu siffofin da ake da bukatarsa gwargwadon yadda daidaiku da inda mahallan rayuwa mabanbanta da juna, alal misali matashiya yar jami'a adaidai wannan lokace akwai wani saurayi da bai iya karatu da rubutu ba ko kuma ace yana can kasa da ita a matakin karatu, gaskiya ni bana bata shawarar ta aure shi, saboda zata ji kuntatuwa cikin rayuwarta ta yau da gobe sannan shima zai dinga jin kaskantuwa a gabanta bisa fifikon da take da shi kansa, sai dai hakan bai nufin wannan bai dace da wata yarinyar ba da siffofinta ka iya kasancewa mai ilimi ta kuma dace da mustawansa., to a iran wannan muhalli zai kasance mafi alheri mazaje gareta.
Wani misalin za a iya samun wani mutum mai wata larura a jikinsa adadai wannan lokaci mustawan kyautatar dabi'unsa da rikonsa da addini ya lullube wannan larura ta jiki, idan yarinyar ta shirya ta zauna da shi ba tareda damuwa da larura jikinsa ba sannan kuma shi ya kasance yana yalwar hannu da zai iya dauke hidimdimunta tareda wannan larura da yake da ita to anan babu matsala cikin auranta  da shi a shari'ance ya halasta, saboda haka ba zamu iya tilasta ta ba aurensa ba tareda wannan larura kadai dai zamu karfafeta da cewa ta karkatar da kallonta zuwa ga rikonsa da addinin da kyawuntar dabi'arsa da ikon da yake da shin a dauke nauyinta kada kallonta ya shallake hakan game da shi, sai dai cewa muna iya wasu ba'ari nasiha kada suyi irin hakan sakamakon banbantar dabi'ar rayuwarsu shi da ita.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: