bayyinaat

Published time: 21 ,December ,2018      18:48:17
Tabbas mun qudurce a cikin Manzanni akwai manyansu guda biyar, su ne ma’abota sababbin shari’o’i da sabon littafin Allah
Lambar Labari: 351
HIKIMAR AIKO ANNABAWA:
Haqiqa mun qudurce Allah (SWT) ya aiko Annabawa da Manzanni domin shiryar da mutum da kai shi ga samun cikakkiyar kamala da samun arziqi tabbatacce, wannan manufar ba ta tabbata har sai idan Allah ya aiko Manzanni, ba dan haka ba da mutum ya nutse a cikin tavon vata; Allah ya ce: (Manzanni ne masu bishara da yin gargaxi, domin kar mutane su sami wani hanzari a wajen Allah bayan Manzanni, Allah mabuwayi ne mai hikima).( )
Tabbas mun qudurce a cikin Manzanni akwai manyansu guda biyar, su ne ma’abota sababbin shari’o’i da sabon littafin Allah, na farko shi ne Annabi Nuhu (A.S), Annabi Ibrahim, Annabi Musa, Annabi Isa, na qarshen su Annabi Muhammad (SAW). Allah ya na cewa: "Ka tuna lokacin da muka karvi alqawuransu, da na ka da na Nuhu (AS) da na Ibrahim (AS) da na Musa (AS) da na Isa xan Maryam (AS) mun karvi alqawarin ku da gaske [wato ba wasa]).( )
Allah (SWT) yana cewa: (Ya Muhammad ka yi haquri kamar yadda manyan manzanni suka yi).( )
Lallai mun qudurce tabbas Annabi Muhammad (SAW) shi ne cikamakin Annabawa kuma qarshen Manzanni, shari’arsa ta game duk mutane kuma wanzajjiya ce matuqar duniya ba ta qare ba, ma’anar hakan shi ne duk ilumummuhka da hukunce-hukunce kai har ma da koyarwar Musulunci sun game komai tare da amsa duk buqatun xan Adam na fili da na zahiri, duk wata sha’awa sabuwa ta Annabta ko Manzanci da’awar qarya ce wacce dole a yi watsi da ita, Allah ya ce: (Muhammad (AS) bai zama mahaifin xaya daga cikin ku sai dai shi Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa, Allah fa shi ne masanin komai).( )

 ZAMANTAKEWA TSKANIN MABIYA ADDININ ALLAH:
Duk da cewa mun lura addinin Musulunci shi ne addinin Allah na gaskiya a wannan zamanin, mun sakankance da wajiban zaman lafiya da sauran mabiya addinai, sun zauna ne a qasashen Musulmai ko sun zauna a wajen qasashen mu ne, sai dai wanda ya xaga tutar yaqar Musulmai da Musulunci, Allah yana cewa: (Allah bai hana ku yin alheri har ma da yin adalci ga waxanda ba su yaqe ku ba, kuma ba su fitar da ku daga gidajen ku ba, haqiqa Allah yana son masu adalci).( )
Tabbas mun sakankance cewa zai yiwu a bayyana haqiqanin Musulunci har ma da koyarwarsa ga kowa ta hanyar gudanar da magana ta hankali tare da yin munaqasha (wato qarar da juna ta hanyar hujja) a cikin wasu mas’aloli, mun gamsu da cewa Musulunci yana da qarfin jawo masu neman gaskiya zuwa gare shi tare da waiwayo da su gare shi idan aka bayyana musu menene Musulunci, musamman a wannan duniyar da mutane suka fuskanto shi domin kiyaye wannan saqon.
Don haka ne bamu yadda da a danqarawa mutane Musulunci ba, Allah yana cewa: (Babu tilastawa a cikin addini, ai shiriya ta bayyana vata ya matsa gefe guda).( )
Haqiqa mun gamsu da cewa babu kirna da ya fi kamar Musulmai su yi riqo da koyarwar addinin su, kamar yadda Imam Ja’afarussadiq (AS) yake cewa: (Ku kasance masu kiran mutane ba da harshen ka ba (wato da aikin ta hanyar bin addini sak da qafa) ba buqatar a takurawa mutane tare da yi musu dole don su karvi Musulunci.

  ISMAR ANNABAWA:
Mun gamsu da cewa duk Annabawa Allah ya kare su daga yin laifi da kura-kurai a gaba xayan rayuwarsu (kafin Annabta da bayanta), Allah ya tsare su daga kura-kurai ko kuma abu ya rikice musu, Allah ne ya qarfafe su da haka; domin Annabin Allah idan ya yi kuskure ko laifi to ya rabu da wannan makarin da yake tsare da kambun Annabta, to a wannan lokacin mutane ba za su aminta da shi ba a matsayinsa na tsani tsakanin su da Allah, ballantana ma su riqe shi abin koyi kuma shugaba a cikin ayyukan su.
Saboda haka muka qudurce duk zahirin wasu ayoyin Qur’ani waxanda akan iya zaton cewa wasu Annabawa sun yi kura-kurai, to wannan yana nufin barin abin da ya fi ne (manufa zavin abinda bai fi ba, akan wanda ya fi, tare da cewa kowanne ya halatta), ko kuma mu ce kamar yadda xaya daga cikin A’immatu Ahlil baiti (A.S) ya ce: "Kyawawan ayyukan bayi masu nagarta su ne kura-kuran makusanta, (waxanda Allah ya yadda da su).( ) domin kowane mutum ana duba irin aikin da ya dace da matsayinsa ne.

  ANNABAWA BAYIN ALLAH NE:
Mun qudurce cewa babban abin alfahari a wajen Annabawa (AS) shi ne kasancewar su bayin Allah masu yi masa biyayya, don haka ne kullum a sallolin mu na yau da gobe muke mai-maita kalmar ‘ash’hadu anna Muhammadan Rasulullah, wa ash’hadu anna Muhammadan abduhuu wa rasuluhu’.
Mun tabbatar cewa ba wani Annabi da ya yi da’awar allantaka, ballantana ya kira mutane su bauta masa; {Ba wani mutum don Allah ya bashi littafi da hukunci da annabta ya cewa mutane ku bauta mini ku bar Allah}.( )
Haka Annabi Isa (A.S) bai cewa mutane su bauta masa ba, shi kansa ya xauki kansa a matsayin bawan Allah kuma Manzonsa, Allah yana cewa: (Annabi Isa baya qyamatar ya zama bawan Allah, haka ma Mala’iku ba sa qin su zama bayin Allah).( )

  MATSAYIN CETON ANNABAWA:
Haqiqa mun tabbatar cewa Annabawa (A.S) musamman Sayyadina Muhammad (SAW) suna da damar ceto; domin za su ceci wasu masu laifi: {Babu wani mai ceto sai bayan izinin Allah (SWT)}.( )
{Waye zai yi ceto a wajen Allah, ai sai bayan Allah ya bada izini}.( )
Idan wasu ayoyi sun kare ceto kamar: (Tun kafin wata rana ta zo wacce babu ciniki, ba soyayya ba ceto)( ), to ana nufin ceton da ba izinin Allah, ko ceton wanda bai kai matsayin yin ceto ba; domin ayoyin Qur’ani - kamar yadda muka faxa - wasu sashi suna fassara sashi.
Tabbas mun haqiqance mas’alar ceto tsari ne mai muhimmanci na tarbiyyar xai-xaikun mutane, tare da mayar da masu laifi zuwa ga madaidaiciyar hanya tare da qarfafa su akan taqwa da raye manufa a cikin zukata; saboda mas’alar ceto ba aba ce mara kan gado ba, ta game wanda ya can-canci a cece shi ba kowa ba, abin nufi wanda laifuffukan sa ba su yi yawan da zai zama alaqa tsakanin mai savo da mai ceto ba ta yanke ba; dangane da haka ceto a matsayin tsoratar da masu laifi ya ke don kar su rusa gadar dake bayansu, kar kuma su bar hanyar dawowa dan kar su rasa can-cantar a waiwaye su don a cece su.
Muna karantawa a qissar Annabi Yusuf (A.S) ‘yan uwansa sun yi tawassali da mahaifin su (Sun ce: ya mahaifin mu ka nema mana gafarar laifin mu, haqiqa mun kasance masu laifi). Sai mahaifin su ya amince da abin da suke so, sai ya ce: (Ai zan neman muku gafarar Ubangijina).( ) Wannan dalili ne wanda ke nuni akan cewa tawassali ya watsu a wannan al’ummar.
Sai dai wajibi ne kar yin tawassali ya jawo a qetare abin da hankali ya yadda da shi, kar kuma a shige gona da iri a cikin yinsa, kar kuma a bawa waliyyai qudra ta kansu a wajen tasiri, kar kuma ya surantu a zukata cewa za’a iya wadatuwa da izinin Allah, wannan zai jawo yin shirka da kafirci.
Kamar yadda tawassali ya wajaba kar a xorashi ya yi kama da bautar waliyyai; saboda hakan kafirci ne kuma shirka ce, saboda ba sa iya mallakarwa kansu amfani ko cutarwa ba tare da yardar Allah ba: (Ka ce ban mallaki amfani da cuta ba a karan kaina, sai dai abin da Allah ya so).( )
Muna iya ganin shige gona da iri da kuma sakaci a cikin mas’alar tawassali a cikin baki xayan jahilan qungiyoyin Musulunci, wanda wannan yana buqatar shiryar da su tare da nusar da su.

  ASALIN KIRAN ANNABAWA XAYA NE:
Mun qudurce cewa baki xayan Annabawa masu yin tarbiyya ne kuma suna nuni a kan manufa xaya, wannan manufar ita ce ci gaban mutuntaka ta hanyar yin imani da Allah da ranar alqiyama da koyarwa tare da yin tarbiyya ingantacciya, kai har da qarfafa tushen xabi’u masu kyan a zamantakewar al’umma; don haka muna girmama baki xayan Annabawa, wannan shi ne abin da Qur’ani ya xora mu a kai: (Bama banbantawa tsakanin Manzannin Allah).( )
Haqiqa addinin Allah sun cika a hankali, sannan koyarwawr Addinin ta yi zurfi tare da wucewar zamani, kuma tare da yunqurin mutane don su karvi wannan koyarwar, har dai a qarshen zangon cikar addinan ya zo wanda shi ne qarshe, wato addinin Musulunci: (A yau ne na kammala muku addinin ku na cika muku ni’imata na yadda da ku yi addinin Musulunci).

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: