bayyinaat

Published time: 19 ,October ,2020      20:36:21
"ما اوذي نبي بمثل ما اوذيت"
Lambar Labari: 352

Kamar yanzu ne Allah ya tseratar da mutanen Musa daga damkar Fir'aun ta wata hanya mai cike da al'ajabi, amma kafafuwan su basu gama bushewa daga danshin ta6on da suka taka suka haure ba, suka ce Musa ya sama musu Ubangiji irin na masu bautar gumaka, wannan wacce irin cutarwa ce ga Annabin Allah.

Bayan an dan wuce gurin kadan, Musa ya tafi munajati ya bar wa mutanen sa wanda zasu koma gareshi, wani mutum dabam ya canza musu alkibla, suka kafircewa wasiccin sa, suka koma bautar Dan Maraki, wannan wacce irin cutarwa ce ga Annabin Allah.

Kai sun ma cewa Annabi Musa, ka tafi kai da Ubangijin ka ku yi yaki mu muna nan ba inda zamu. Wannan wacce irin cutarwa ce ga Annabin Allah.

In muna lissafa cutarwar mutanen Musa ga Musa, hankali ba zai ta6a sawwara hakan ba. Amma duk da wannan wacce irin cutarwa Al'ummar Muhammad suka yi masa wacce tafi hatta ta Al'ummar Musa ga Musa?

Ku gane cutarwa a nan a na nufin cutarwar mabiyan Annabi wadanda suka yi imani da shi ga Annabin da ya zo musu da tsira, ba cutarwar Kafirai ga Annabin ba.

Na barku ku bincika ku ji, ku gani, ku gano.

Amincin Allah ya tabbata ga wanda ya ji shiriya kuma ya bi ta.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: