bayyinaat

Published time: 10 ,December ,2020      11:33:34
Shi Hankali dama Allah (swt) ya bamu shi ne domin bambamce tsakanin abinda yake gaskiya da wanda yake karya, mai kyau daga maras kyau, mai amfani daga mai cutarwa, sabanin Dabbobi da Allah bai basu shi ba basa iya banbance (galiban) tsakanin wadannan abubuwan. Bisa wannan dalilin ne ma yasa ake dauke alkalami daga wanda hankalin sa ya gushe.
Lambar Labari: 356
A dai-dai lokacin da muke kokarin tabbatar da Khalifanci Ali dan Abu Dalibi (As) muna yin amfani da hanyoyi guda uku ne wadanda basu da na hudu. Wato *Hanyar Hankali, Hanyar Ayoyi da kuma Hanyar Ruwayoyi.* Duk abinda ba'a iya tabbatar da shi ta daya daga cikin hanyoyin nan guda uku ba to ya zama son rai.

*DALILIN HANKALI:*

Shi Hankali dama Allah (swt) ya bamu shi ne domin bambamce tsakanin abinda yake gaskiya da wanda yake karya, mai kyau daga maras kyau, mai amfani daga mai cutarwa, sabanin Dabbobi da Allah bai basu shi ba basa iya banbance (galiban) tsakanin wadannan abubuwan. Bisa wannan dalilin ne ma yasa ake dauke alkalami daga wanda hankalin sa ya gushe.

Hankalin dan Adam, (a duk lokacin da yake da zabi tsakanin abu sama da daya) ya na shiryar da shi zuwa ga zabin abinda yafi. Idan da zai zabi kuma ya fifita wanda aka fi akan wanda yafi, kai tsaye kowa zai ce kai amma wannan anyi sakarai, bai yi aiki da Hankalin sa ba. Misali idan mutum ya je Asibiti yana zabin Likitan da yafi kwarewa ne domin ya duba lafiyar sa. Hakanan idan zaka sa yaron ka makaranta ka fi son sa shi wacce tafi fice a garin da kake. Haka al'amarin yake a kowanne fage na rayuwa, kuma tabbas haka yafi cancanta ya kasance a fagen Shugabanci (a yanzu ma haka mutane suke a shugabancin siyasa suna duba dan takarar da suka ga yafi sauran sai su zabe shi, Allahummah sai dai in an murde musu). Na'am wani lokacin a bisa tsukakkiyar Kwakwalwar dan Adam da kuma rashin sanin sa ga gaibu yakan zabi wanda a tunaninsa shi yafi sai daga baya ta bayyana a gareshi cewa yayi kuskure.

Tabbas Ali dan Abu Dalibi (As) a bisa mahanga ta Hankali shi yafi dacewa al'umma su mikawa al'amarinsu domin ya fi sauran Sahabbai fifiko ta fuskacin Ilimi, Gwarzantaka, Rigayen karbar Addinin, Kusanci da Annabi, domin a wurare da dama wadanda ba zasu lissafu ba Annabi da kansa ya fifita Ali akan sauran sahabban misali; Auren diyarsa Fatima sun nema ya hanasu ya ba Ali, Isar da sakon ayoyin Bara'a, Yakin Khaibar, Ranar Mubahala, Kulla 'yan uwantaka, Rufe kofofin Masallaci, Kebancewa da wasu ilimummuka,(shi ne kofar Birnin Ilimin Annabi) kuma shi ne kadai (na fada na bugi kirji na ce shi kadai ne) wanda Annabi bai taba shugabantar da wani Babba ko Yaro a kansa, a zaman gida ko a tafiya ko a yaki ba. To tayaya bayan wafatin Annabin mu zamu shugabantar da wani akansa.
*'ما لكم كيف تحكمون'.*

*DALILIN AYOYI:*

Kamar yadda a rubutun da ya gabata muka bayyana dangane da Hukuncin Hankali na zaben abinda yafi cancanta, to amma a lokuta da dama mutum, saboda karancin Ilimi, tsukewar kwakwalwa da rashin sanin gaibu, yakan zabi abinda daga baya zai zo yayi nadama. Bugi da kari kan cewa, shi Halifancin Annabi al'amari ne mai girma wanda yake bukatar takatsantsan wajan fitar da wanda ya cancanta, musamman a wancan lokacin da Addinin bai jima da kafuwa ba, kuma ga barazana ta ciki da ta waje tana bibiyarsa. Ga Munafuqai ga Yahudu ga Nasara ga Mushirikai da ma masu ciwo a zukatansu. A irin wannan yanayin idan ba'a yi dace da *Masani, Jajirtacce, Gogagge, Tsayayye kuma Sadaukin Shugaba ba to Addinin zai iya rushewa.* Wannan kenan ta daya bangaren kuma iya gano wanda yake da wadannan sifofin *(a zahirinsa da badininsa)* ba abu ne mai sauki ba, musamman saboda abinda muka ambata na cewa mutum yana zabi ne bisa cancanta, amma ya gama darjewa sai yaga ashe zaben tumun dare yayi (mukalli zaben 'yan Najeriya ga Buhari).

To menene mafita Allah ya bar mutane su zaba alabasshi idan suka yi zaben tumun dare, Addinin ma duk ya wargaje? Ko kuwa Allah (swt) da kansa ya zaba musu wanda yafi a saninsa da gaibu don Addinin ya tsira?

A bisa *LUDUFI* na Allah (swt) ga bayinsa ba makawa ya jibinci zaba musu wanda zasu mikawa ragama kuma komai ya tafi dai-dai. Don haka Allah (swt) kai tsaye ya zabi Ali dan Abu Dalib (As) a matsayin wanda zai riqe ragamar Addinin kuma ya kaishi ga gaci. Bisa wannan ayoyi da dama sun zo suna mai nuni ga hakan ko dai kaitsaye ko kuma a bisa hannunka mai sanda.

Daga cikin irin wadannan ayoyin akwai; Ayar Wilaya (sura Ma'idah aya ta 55), Ayar Tsarkakewa (sura Ahzab aya ta 33), Ayar Tablig (sura Ma'idah aya ta 67), Ayoyin saukar Azaba (sura Ma'arij ayoyi 1 zuwa 3) da sauransu Ubangiji Ta'ala bai tsaya nan ba sai da ya karkare da *GHADIR.*

*Ko da wasa ba yadda za'a yi mai cikakken Hankali ya ce Manzo (saw) zai tara dubun-dubatan Sahabbansa tsawon kwanaki uku a wani kwazazzabo ba gida gaba ba gida baya ba inuwa balle wajan shakatawa a cikin garjin Rana bayan kammala aikin Hajji kowa Hankalinsa ya koma wajan iyalinsa, sannan ya dauki tsawon lokaci yana musu bayani, sannan ya daga hannun Ali ya ce*
*' من کنت مولاه فهذا علی مولاه'*
*Ma'ana 'WANDA DUK NA ZAMA SHUGABANSA TO ALI MA SHUGABANSA NE.'*

Bayan kammala bayani kuma ya tsaya ya tilasta kowa yazo yayi *mubaya'a maza da mata, har a ruwaito cewa wasu manyan Sahabbai sun taya Ali murna da furuci na sallamawa a gareshi. Duk da wannan wani yazo yace mana wai mun yarda an yi GHADIR amma Annabi ya tara Sahabbansa ne don ya nuna musu cewa *WANDA DUK NA ZAMA MASOYINSA TO ALI MA MASOYINSA NE.* Wato kenan ba ma batun Shugabanci ko Halifanci ake yi ba.
*HABA! HABA!! HABA!!!*
*"ما لكم كيف تحكمون"*

Ta fuskacin Ruwayoyi kuwa, tun farkon da'awar nan ta Annabi (saw) ya ayyana Ali dan Abu Dalibi a matsayin wanda zai Halifance shi a bayan bayanan, wannan kuwa ya faru a Hadisin da ya shahara da sunan Hadisin Dar. (Hadisin Gida). Wato lokacin da Allah (swt) ya umarci Manzon sa da ya gargadi danginsa makusantansa, sai ya tarasu ya sanar dasu cewa shi Manzon Allah ne zuwa garesu kuma ya bukaci taimakon su amma ba wanda ya amsa masa sai Ali, to tun a lokacin Manzo ya bayyana Ali a matsayin wanda zai gajeshi, kuma Halifansa a bayansa, wannan maruwaita da dama ne daga bangaren Shi'a da Sunnah suka ruwaito shi. Wannan hadisin shi ne mabudin Halifanci, Hadisin Ghadir kuma marufin Halifanci.

Akwai Hadisai da dama wanda suke nuni ga Halifancin Ali wannan kuwa sun hada da: Hadisin Manzila, Hadisin Saqalaini, Hadisin Wilaya, Hadisin Wanda ya mutu (man mata), Hadisin Ghadir da sauransu. Zamu dauki hadisan uku karshe a takaice muyi bayaninsu.

*HADISIN WILAYA:*

Matanin hadisin yazo da sigogi dabam-dabam, daga cikinsu akwai:
*(علي ولي كل مؤمن بعدي)، (هو ولي كل مؤمن بعدي)، (أنت ولي كل مؤمن بعدي و مؤمنة)، (فإنه وليكم بعدي)، (إن عليا وليكم بعدي)، (أنت ولي المؤمنين من بعدي)، (إنه لا ينبغي أن أذهب إلا و أنت خليفتي في كل مؤمن من بعدي)، (فهو أولي الناس بكم بعدي).*
Wadannan hadisan Maluman Sunnah ne suka ruwaito su a littatafan su, kamar; Musnad Ahmad, Musnad Abi Dawudul Dayalisi, Albidaya wal Nihaya, Tarikhu Bagdad, Al,Isabah da sauransu. Shi wannan Hadisin ma'anar sa a sarari take bashi da bukatar karin bayani.

*HADISIN WANDA YA MUTU:*

Muslim ya ruwaito daga Manzon Allah (saw) yana cewa;
*"من مات ولیس فی عنقه بیعة مات ميتة جاهلية"*
Ma'ana; *Wanda duk ya mutu ba tare da igiyar mubaya'a ba, yayi mutuwar Jahiliyya.*

Yanda wannan Hadisin yake nuni ga Halifanci Ali kuwa shi ne, Buhari da sauran maruwaitan Ahlul Sunnah da dama sun ruwaito cewa Sayyida Fatima Zahra (As) ma'asumiya diyar Manzon Allah (saw) bata yiwa Abubakar mubaya'a ba, kuma ta koma zuwa ga Allah, alhali tana fushi da shi, bisa wannan sai muce, idan da Abubakar ne Halastaccen Halifan Annabi, (ba mijinta Ali ba) wanda ya zama wajibi kowa yayi masa mubaya'a ciki kuwa hadda ita kanta sayyada, kenan ta yi mutuwar Jahiliyya, tunda gashi an ce batayi mubaya'a ba har ta rasu. *Tambaya ta yaya shugabar Matan Aljanna zata yi mutuwar Jahiliyya?*
*ما لكم كيف تحكمون*

*HADISIN GHADIR:*


Hadisin Ghadir matsayin sa ya kai abinda malaman hadisi suke cewa mutawatiri, wato irin hanyar da aka samar da Alqur'ani, don haka wanda duk yayi inkarinsa to zai iya inkarin Alqur'ani ma.

Hadisin Ghadir, hadisi ne mai tsawo domin kuwa, huduba ce Manzo (saw) ya gabatar mai tsayi mai cike da hikima, da kalamai na wasicci da bankwana ga al'umma da ma duniyar bakidayan ta. Sai dai abin takaici mafiyawancin maruwaita sun gutsuro wani dan bangare ne, na hudubar suka rubuta, ba ma wannan ne mafi ban takaici ba a'a yadda kuma wasu suka yi kokarin murguda ma'anar hadisin da bashi wata siffa ta dabam, wadda zata tashe shi daga ainihin hadafin sa, tattare da cewa Allah (swt) da kansa ya girmama al'amarin domin kuwa ayoyi biyar ya saukar a gabanin faruwar taron hudubar da bayan ta.

Ayar farko itace ayar Tablig, sai ayar kammala addini da cika ni'ima, sai ayoyin saukar azaba da ke cikin Suratul Ma'arij. Zamu dauki ayoyin kammala addini da na saukar Azaba muyi bayaninsu a takaice.

*AYAR KAMMALA ADDINI:*

Bayan Annabi (saw) ya kammala doguwar hudubar sa kuma ya daga hannun Ali ya nuna shi ga al'umma kuma ya cire rawanin sa ya nadawa Ali (alama ce ta nadi), sannan ya umurci Sahabbai da kowa yayi mubaya'a, kuma kowa yayi, a take sai Allah (swt) ya turo Jabara'il da wannan ayar:
*"...اليوم یئس الذین کفروا من دینکم فلا تخشوهم واخشون اليوم أكملت عليكم دينكم و أتممت عليكم نعمتي و رضيت لكم الإسلام دينا"*
Bayan saukar wannan ayar an ji Manzo (saw) ya yi Kabbara yace 'Allah ya kammala addini kuma ya cika ni'ima, kuma ya karbi Manzanci na da wilayar Ali a bayana. Domin a baya Allah dama ya fada masa cewa idan bai isar da wannan sakon na Wilaya ba to tamkar ma bai isar da manzancin sa ba.

*AYAR SAUKAR AZABA:*

Bayan kammala waccan hudubar ana shirin tafiya sai wani Sahabi yazo wajan Manzo yace: ka ce mana Allah daya ne mun yarda ka ce kai Manzo ne mun yarda ka ce muyi Sallah, Azumi da sauransu duk mun yarda,wannan bai ishe ka ba sai ka sa mana dan Amminka a matsayin shugaba, shin wannan daga Allah ne ko daga gareka, sai Manzo yace na rantse da wanda babu abin bauta face shi daga Allah ne, to sai ya tafi yana mai rokon Allah ya saukar da Azaba a kansa idan abinda Muhammad ya fada gaskiya ne, bai gama rufe bakinsa ba sai ga ruwan duwatsu a kansa take ya sheka barzahu. Sannan Allah ya saukar da wadannan ayoyin:
*"سأل سائل بعذاب واقع، للكافرين لیست له دافع، من الله ذي المعارج"*

Wannan duka haka malaman Ahlul Sunnah suka ruwaito amma duk da haka suke wa hadisin Ghadir Tawili.
*"ما لکم کیف تحکمون"*

*Allah mun gode maka da ka sanya mu daga cikin masu riko da wilayar Ali dan Abi Dalib, Allah wanda ya haskaka mana wannan tafarkin Sayyid Zakzaky ka kara masa lafiya da yawancin kwanaki ka gaggauta dawo mana da shi tsakaninmu.*
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: