bayyinaat

Published time: 10 ,December ,2020      14:47:59
*Tirkashi!* Duk mai aiki da hankali a lokacin saukar wannan ayar ya kamata ya fahimci muhimmancin wannan al'amarin na wilaya/Khilafa ya tsaya kyam ya bashi kariya. To amma ina da yawan Sahabbai sai suka dauki al'amarin a matsayin sassauka. Idan Ali bai zama Halifa ba maimakon sa wani da ake kyautatawa zato ya zama Halifa ai ba komai ba ne.
Lambar Labari: 362
Lokacin da Allah (swt) yayi umurni da yawa yawan mutane sukan dauki umurnin da sassauci. Salon yadda Allah ya muhimmantar da al'amarin jagoranci ta hanyar Nassaba Ali dan Abu Dalib a matsayin Halifan Annabi, har ya yiwa Annabi (saw) kaka-tsara-kaka ta hanyar bayyana masa cewa idan har bai isar da wannan sakon ba, to tamkar ya rusa duk abinda ya yayi shekara Ashirin da Ukku yana yi ne.

*Tirkashi!* Duk mai aiki da hankali a lokacin saukar wannan ayar ya kamata ya fahimci muhimmancin wannan al'amarin na wilaya/Khilafa ya tsaya kyam ya bashi kariya. To amma ina da yawan Sahabbai sai suka dauki al'amarin a matsayin sassauka. Idan Ali bai zama Halifa ba maimakon sa wani da ake kyautatawa zato ya zama Halifa ai ba komai ba ne.

*'تحسبونه هينا و هو عند الله عظيم'*

Lallai al'amarin mai girma ne, domin zamu iya cewa, sabawa wancan umurnin ta hanyar sauya Halifa shi ne abinda ya kai ga afkuwar waki'ar Karbala. (Wanda wata kila da yawan Sahabbai da sun san haka zata faru da sun bada kariya ga Halifan da Allah ya nada) Domin kuwa da tun asali Ali ne ya zama Halifan Musulmai to da ire-iren su *Yazidu basu isa su rike koda Mai Unguwa ba ballantana har su sunsuni kujerar Halifa kacokaf.* Kuma da tun asali al'umma basu yi sakacin sauya Halifan Allah da Manzon sa ba da ba zai taba yiwuwa ba al'ummar Annabi suyi gangami su kashe dan Annabin Rahma ba a cikin shekaru Hamsin kacal da wafatin Annabin.

Allah (swt) yana cewa:

*"...فاليحذر الذين يخالفون عن أمره أن تصيبهم فتنة أو يصيبهم عذاب أليم."*

Wato masu sabawa umurnin Allah, su kiyayi afkuwar Fitina ko Azaba mai radadi akan su. Wato kenan zamu iya cewa sabawa wancan umurnin na Allah shi ne ya haifar da saukan wannan babban bala'in akan al'ummar musulmi ta yadda ya zama suka iya yin gangami suka kashe dan Annabin su. *Lallai ba wata musiba da ta sami wannan al'ummar kamar kisan Imam Hussain (AS)*

*Allah ya tsare mu raina umurnin sa da rikon sako-sako gareshi*


*UMURNI DA KYAKKYAWA DA HANI GA MUMMUNA*

Hakika Hadisai da ayoyi da dama sun zo suna bayanin muhimmancin umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna. A wurare da dama Allah (swt) yayi bayanin muhimmancin su a inda yake zargin wasu al'ummu da suka fada cikin bala'o'i na halaka sakamakon rashin yin su. A wasu wuraren kuma Allah (swt) ya nuna cewa masu lizimtarsu su ne ma'abota babban rabo a tsakankanin al'umma.

*ولتكن منكم أمة يدعون إلى الخير و يأمرون بالمعروف و ينهون عن المنكر و أولئك هم المفلحون*

Yabo mafi girma da Allah yayiwa wannan al'ummar ya kasance bisa asasin umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna.

*کنتم خیر أمة أخرجت للناس تأمرون بالمعروف و تنهون عن المنكر*

Idan muka dora wannan ayar a karkashin abinda malaman mandik suke cewa 'aksun nakird' 'عكس القيض' zamu fahimci cewa mu al'ummar musulmi idan muka bar wadannan to kenan zamu rasa waccan darajar da daukakan da yabon da Allah yayi mana, natijar haka kuwa shi ne kaskanci da wulakanci a rayuwar duniya da ta lahira, Allah ya kiyashe mu.

Sai dai bisa dukkan alamu sannu a hankali al'umma tana kuwa nisantar wadannan al'amuran, kuma tana fadawa cikin kaskancin da wulakanci. Dalilan da suke sawa a guji wadancan al'amuran sun hada da, tsoro, kwadayi, rashin kula da addini da kuma uwa uba akidar nan ta 'karda wal kadar' 'قضى والقدر'. Ita wannan akidar wato cewa komai mukaddari ne, mai kyau da sharri duk daga Allah ne, wal iyazu billah, Alkur'ani ya karyata wannan. Wannan akidar tasa in an ga wani yanayin mummunan abu sai a ce rabu dashi Allah ya shirye shi haka Allah ya tsara masa rayuwarsa, saboda haka ba wani katabus na a canza shi.
To amma a daya gefen Imam Hussain (as) ya bamu DARASI cewa shi umurni ga kyakkyawa da hani ga mummuna ana yinsa ne koda kuwa zai kai ga salwantar ranka ne. Sannan ya nuna mana cewa duk lokacin da Addini ko al'ummar musulmi suke fuskantar wata barazana to ana iya salwantar da rai ma domin ceto shi da dawo da martabar al'ummar. Hakanan ya nuna mana cewa ana magance barna ne daga tushen ta, da zaka zo kana yakar talakawa akan su daina Bidi'a amma ka kyale shugabannin da suke bawa Bidi'ar kariya to ka bar Jaki ne kana dukan Taiki har abada Bidi'ar ba zata tafi ba, sai dai ma tayi ta sake salo. Hakanan kar kaji tsoron za'a iya kashe ka, domin kisan zai zama sanadiyar rayar da Addinin.


*ZABIN MAFIFICIYAR HANYA KOMAI TSADARTA*

Zamu iya cewa tun asali ba mutanen Kufa ba ne suka sa Imam tsaida Saura ga gwamnatin Yazidu ba. Domin gayyatar mutanen Kufa da wasikunsu basu zowa Imam ba sai bayan daya isa Makka da kimanin watanni biyu ma.

Tun lokacin da sakon Yazidu ya zowa Imam na bukatar yayi mubaya'a, Imam ya kuduri aniyar bijirewa wannan bukatar da kuma tsayawa kyam koda hakan zai zama sanadiyar rasa ransa mai tsarki, kuma koda kuwa ba wanda ya goya masa baya.

Domin zabi ukku ne ke ga Imam;
(1) Ko dai Imam yayi mubaya'a ga Yazidu.
(2) Ko ya ki yin mubaya'ar ya gudu jeji ko cikin duwatsu yaje can ya kebe kansa yayi ta bauta har mutuwa tazo masa ko yanayi ya canza. Kamar yadda As'habul Kahfi suka yi a lokacin su.
(3) Ko kuma ya ki yin mubaya'a kuma ya tsaya kyam har a shekar da jininsa.

Anan babban *DARASIN* da Imam ya bamu shi ne sai ya zabi na ukkun, duk da tsadar farashinta ya tsaya kyam har aka shekar da jininsa mai albarka, wanda wannan ya nuna mana wannan hanyar a wannan addinin namu tafi tasu As'habul Kahfi.

Bayan isar Imam Makka da kimanin watanni biyu sai ga wasiku daga mutanen Kufa, suna kiran Imam da ya je garesu zasu taimake shi.

Gabadayan garuruwan da suke karkashin Daular Musulunci a wancan lokacin, Kufa tafi su yawan gwaraza mayaka, tafi Makka tafi Madina, ba inda za'a kwatanta Kufa dasu sai Sham. Gashi kuma Kufa tana da karin matsayi na kasancewarta dandazo ne na magoya bayan Ahlul Bait (as), domin can ne Amirul Muminin (as) ya zauna a yayin Khilafarsa. Don haka Imam ya karbi da'awarsu ya tura musu dan uwansa Muslim bn Akil domin ya share masa hanya.

Wasu daga cikin Sahabbai da makusantan Imam sun bashi shawarar kar yaje Kufa, wasu sun bawa Imam Shawarar ya tafi Yaman, amma Imam ya nuna musu ba makawa zai tafi Kufar ne saboda wadancan dalilan.
Karin dalili shi ne cewa su mutanen Kufa ne da kansu suka gayyaci Imam. Bayan wannan gayyatar ta mutanen Kufa wanda aka kiyasta cewa wasikun mutanen Kufa ga Imam sun kai kimanin dubu goma sha biyu dauke da sa hannun mutum dubu goma sha takwas, ga su da mayaka, ga su zaratan magoya bayan Ahlul Bait, duk da wannan kuma Imam yaki zuwa to lallai da malaman Tarihi na duniya sun gorantawa Imam, akan rashin amsa waccan gayyatar. Saboda haka zuwan Imam Kufa ya rufe bakin duk wani da zai zargi Imam akan rashin yin abinda ya dace. Don haka Imam ya fita fes yayi abinda hankali ke hukuntawa.


*ME YASA KUFAWA SUKA JUYAWA IMAM BAYA.?*

Kamar yadda rubutun nawa ya zama darussa daga saurar Imam, wadannan darussan zamu dauke su ne daga jinibin Imam da kuma jinibin makasansa, don haka wannan karon darasinmu daga Kufawa ne.

Kamar yadda a rubutun jiya na ambata cewa Kufa ta tattaro wasu abubuwa, (imtiyazat) kamar yawan gwaraza mayaka, dandazon magoya bayan Ahlul Bait bugudakari ga shi su da kansu suka gayyaci Imam. Amma me ya faru duk da wadannan suka juyawa Imam baya?

Tun bayan da labari ya jewa Yazidu dangane da yanayin Kufa da tawayen dake faruwa a can da kuma shawarwarin da makusantansa suka bashi, ga kuma wasiyyar Babansa Mu'awiyya cewa in Kufa ta gagareka ka hada su da Ubaidullah sai ya canza gwamnan Kufa ya cire Nu'uman ya turo Ubaidullah bn Ziyad.

*WAYE UBAIDULLAH?*
Ubaidullah wani Mutum ne wanda bashi da imani da tausayi ko miskala zarratin, ga tsananin gaba da kiyayyar 'ya'yan gidan Annabi fal a zuciyarsa da gabobinsa. Mutanen Kufa sun san shi sarai, domin dama ya taba yin Shugabanci a Kufa kafin wannan lokacin, kuma a wancan lokacin ya nuna tsantsar rashin imani, rashin tausayi da rashin mutumtaka. A wancan lokacin ya kwakwale Idanuwa, ya yanke Kafafu da Hannaye, ya fafe cikkuna, ya hallaka mutane a kurkuku bayan ya dandana musu matsananciyar Azaba.

Bisa wannan dalilin ne da mutanen Kufa suka ji labarin shigowar Ubaidullah garin Kufa a matsayin sabon gwamna, sai jikinsu yayi sanyi, ciki ya duri ruwa, suka shiga firgici da razani. Uwa taje ta kamo hannayen Danta daga wajan Muslim, Mata ta kamo hannayen Mijinta da haka da haka suka rinka zare jiki suna warware mubaya'ar su.

Amma bayan waki'ar sai suka dawo cikin hayyacinsu, suka dawo suna nadama har aka samu Tawwabun a cikinsu, wadanda suka yi bore, kuma daga baya aka bisu aka karkashe su.

Babban DARASIN da zamu dauka shi ne, kar mu tsorata ko razana da kisan makashi, domin hakan zai haifar mana da aikin DANASANI, kuma ba zai hana a kashe mu ba. Da rayuwa cikin kaskanci gwamma mutuwa cikin izza da karama.


HURA RUHI GA AL'UMMA.

Lokacin da Manzon Allah (saw) yazo a cikin Jazirar Larabawa ya tarar dasu da gangar jiki amma babu Ruhi. Domin suna rayuwa ne mafi munin ta Dabbobin Daji. Amma a cikin kankanen lokaci wannan Manzon ya busa musu Ruhi ya rayar dasu ya wayar dasu ta hanyar Kalmar Shahada.
'قولوا لا إله إلا الله تفلحوا'

Sannu a hankali bayan wafatin Annabi sai Larabawa suka fara komawa gidan jiya, Ruhin ya fara kanjamewa zuciyoyi suka fara kekashewa. Tun a lokacin Amirul Muminin (as) a wata huduba a Nahjul Balaga yake cewa dasu;

'ما لى اراکم اشباحا بلا أرواح...'

Wato Amirul Muminin yana kallon su a matsayin gangan jikin da bashi da Ruhi.

Shahadar Imam Hussain (as) bata kasance kadai abin bakin ciki da musiba ba, a'a ta daya janibin ta rayar da Addini ne ta motsa mutane ta farkar dasu daga dogon barcin da ya kusa ya shidar dasu zuwa mutuwa, ta hura musu Ruhi.

Wasu daga cikin al'amura (masu kyau da munana) sukan raya Ruhi wani lokacin kuma su kashe shi wannan al'amuran koda kuwa ilimi ne (yana kashewa kuma yana rayawa) amma banda Shahada ita janibi daya kawai take dashi shi ne RAYAWA, wani abin al'ajabi shi ne duk kuwa da abinda ke tattare da ita na firgici da tashin hankali.

Ita Shahada tana yaudarar masu afkar da ita ne, domin a zahiri zasu ga kamar sun gama da abinda basu so, sun murkushe shi (Allah sarki wawaye). Amma al'amarin ba haka yake ba, ita tana rayar da abinda suka so su gusar da shi ne. Allah (swt) yana fada dangane da Shahidai;

"و لا تحسبن الذين قتلوا في سبيل الله امواتا بل أحياء..."

A nan ba Allah (swt) yana cewa kar ku zaci wadanda aka kashe a tafarkin Allah cewa sun mutu ba? To tunda suna raye Kaga ashe kenan abinda suka yunkuro domin rayar dashi shi ma bai mutu ba, yana nan yana rayuwa. Mutum ba zai fahimci wannan ba sai ya kalli mutanen Kufa wadanda kamar yadda muka fada jiya ba'a dade da Shahadantar da Imam ba Ruhikansu suka rayu, kuma ba'a gushe ba har yau din nan tamu Shahadar Imam tana rayar da Ruhika ne, nan kurkusa mutum ya kalli Karbala, falalen dajin da ba gida gaba ba gida baya a lokacin da aka kashe Imam,amma yanzu ya zama babban birnin da duk shekara miliyoyin mutane suke tudada suna jaddada mubaya'arsu ga Imam (as) suna la'antar makasansa.
Saboda haka sai mu cewa masu kisa su bada kokari insha Allahu abinda basu so din nan (suna cikin Kabarinsu suna karbar sakamakonsu) za'a hasko musu suga irin daukaka da tagomashin da yake samu, su kuma la'anta kullu yaumin tana karawa Kabarurrukansu duhu.

SHAHADA DA MASU AFKAR DA ITA.

Shahada wata karama ce da Allah ya kewa zababbun bayinsa yayin haduwa dasu, wato duk wanda ya mutu zai hadu da Allah ne, ta iya yiwuwa haduwar tayi masa kyau ko akasin haka, to shi Shahidi Allah ne da kansa yake zaba masa yadda yake son haduwa da shi, don haka shi haduwarsa da Allah ta musamman ce. Misali ba zasu yi dai-dai ba wanda ya kawo kansa fada ko wanda aka tura dogarawa su taso keyarsa da wanda aka tura direba da motoci na alfarma cikin jerin gwanon 'yan rakiya ana tafiya ana masa rakiya har zuwa fadar. Kusan kamar haka zamu ce duk wanda yaje lahira shi ya kai kansa ko kamo shi akayi amma shi Shahidi Allah (swt) ne da kansa ya tura a taho dashi.

Bisa wannan ne shahada ta zama zabin Allah ce. Don haka mafi yawan Annabawa da Manzanni sun koma ga Allah ne ta hanyar Shahada. An ruwaito daya daga cikin limaman shiriya na wannan al'ummar tamu yana cewa;

'ما منا إلا مسموم او مقتول'

Wato gabadayan Ma'asumai sha hudu na wannan al'ummar sun koma ga Allah ne ta hanyar shahada ne, ko dai an kashe su ne ko an shahadantar dasu da guba.

Imam Hussain (as) lokacin da yaje bankwana da Babansa Manzon Allah a kabarinsa yayi mafarki da shi yana mai ce masa, 'Kana da wani babban matsayi a wajen Allah amma ba zaka kai gareshi ba sai ta hanyar shahada.'

Hadisai da dama sun zo suna bayanin falalar shahada da girman matsayin Shahidi. Ba wani aikin alheri face akwai wani sama dashi har a tuke ga shahada itace aikin alherin da ba wani aikin alheri birbishinta.

Wannan kenan amma ta janibin masu afkar da Shahadar fa, to su kuma sun kasance mafiya munin halittar Allah. Manzo (saw) ya fada dangane da makashin Ali cewa shi ne mafi tsiyautar mutanen karshen zamani. Hakanan Umar bn Sa'ad yayi furuci da cewa a cikin kisan Hussain akwai wuta madawwamiyya da ba makawa gareta, amma da yake shakiyyi ne maras rabon duniya da lahira yaje ya kashe Hussain (as). Imam Hussain a cikin jerin hudubar da yayiwa makasansa ya ce dasu;

'إنى لارجو أن يكرمني الله بهوانكم'

Yadda naga kun nace akan kisa na to ni kuma ina fatan Allah (swt) ya karramani ta hanyar wulakanta ku.

Wannan jumlar ta kunshi gabadayan abinda muke magana akansa, karamar Shahidi da wulakantuwar wanda ya Shahadantar dashi. Dama haka lamarin yake sai wani yayi kuka sannan wani zai dara, don haka samuwar makasa alheri ne ga Shahidi, su kuma wulakanci ne garesu, don haka ya jama'a kowa ya dage da rokon Allah kar ya jarabce shi da fadawa cikin rukunin makasa, ko baka yi shahada ba to kar ka yadda ka jewa Allah hannayen ka dumu-dumu cudanye da jinin Shahidi don karshen tabewa kenan, Allah ya tsare mu.


ME YASA WAKI'AR KARBALA TAFI FICE.

Kafin da bayan waki'ar Karbala anyi waki'o'i masu munin da ba zai misaltu ba. Bayan kimanin shekara daya da waki'ar Karbala, Mutanen Madina sun tayar da bore ga gwamnatin Yazidu, Yazidu ya aike musu da mayaka suka je suka rutsa da Madina suka halasta haraminta, a wannan waki'ar anyi abinda ko a karbala ba'a yi ba, domin a wannan waki'ar ta HARRA an kashe tsofaffi, mata, jarirai da mahaddata. Wata mata tazo wajan kwamandan yakin ta ce da shi ni ina tare dakai, kuma dana yana cikin ribatattun yaki sai yace a zo da shi, da aka zo dashi sai yasa aka fille masa kai ya ce a bata kan ta tafi. Har walayau mayakan sun shiga wani gida, ba kowa sai wata mata da jaririnta, suka tambaye ta dukiya ta ce musu babu sai suka karbe jaririn daga hannunta suka buga kan sa ga bango kwakwalwarsa ta tarwatse suka jefar da gawar suka fice abinsu. A wannan waki'ar an ruwaito cewa kimanin mata dubu ne suka yi ciki suka haifesu ba tare da miji ba, sannan karnuka sun shiga har masallacin Annabi har mumbarinsa sun yi fitsari. Bayan Kura ta lafa kwamandan ya girke kujera a tsakiyar gari ya zauna kowa na zuwa yanayin mubaya'a ga Yazidu, kuma ya furta cewa shi daga yau ya zama bawan Yazidu, yayi abinda yaga dama da jininsa da dukiyarsa, duk wanda ya bijire ya ce shi bawan Allah ne sai a fille masa wuya. In kuka lura zaku ga akwai abubuwan da ko a karbala ba'a yisu ba.

A lokacin Imam Musa Alkazim anyi wata waki'a mai suna 'WAKI'AR FAKKHIN' wacce Hussain bn Ali bn Hassan bn Hassan bn Hassan bn Ali bn Abi Dalib ya jagoranta, a tarihi ana kiranta da waki'ar Karbala ta biyu ita ma anyi abubuwa na tashin hankali a cikinta har Imam Kazim yana cewa bayan waki'ar Dif bamu da wata waki'a data fita.

Kai a zamanin nan namu anyi kuma ana kan yin waki'o'i masu tada hankalin masu hankalin da a wannan zamanin na wayewa bai kamata ayi haka ba, domin ana yin abinda ko a wancan lokacin a karbala ba'a yisu ba, waki'ar Gyallesu daya ce daga ire-irensu, domin Sojojin Najeriya sun yi abinda ko Sojojin Umar bn Sa'ad basu yi ba,domin har tsohuwa 'yar sama da shekaru Sittin suka rufe a daki suka kunna mata wuta ta kone kurmus, banda mata masu cikin da aka hallakasu duk da abinda ke cikinsu, abin takaici kuma a irin wannan zamanin da ake kallonsa na wayewa da cigaba mai cike da kungiyoyin kare hakkin dan Adam, a mulkin da ba na gado ba, wanda duk abinda kayi mulkinka ba zai dawwama ba in ka dade shekara takwas ce kuma danka ba zai gaje ka ba.
Duk da wannan har zuwa yanzu kuma har duniya ta nade ba za'a taba yin waki'ar data kai ta karbala muni ba, dalili shi ne SHAKKHSIYYA ta Imam Hussain (as), duk wanda za'a yiwa wani abu ba zai kai shakhsiyyar Imam Hussain (as) ba, domin ana kaddara musiba ne da girman wanda ta fada akansa.

MACEN DA TA GIRGIZA AL'ARSHIN YAZIDU.

Bayan 'yan ta'adda sun gama ta'adancin su a karbala ranar goma ga watan Muharram ba wanda yayi saura sai Mata da kananan yara sai kuma Imam Zainul Abidin (as) a matsayinsa na maras lafiya. An daddaure su cikin sarkoki aka kama hanyar Kufa dasu daga can kuma aka wuce Sham fadar Yazidu (LA). Tafiyar ta kai tsawon kwanaki 22, 'ya'yan Manzon Allah su goma sha biyu a cikin sarkoki. Abubuwa da dama sun wakana tun daga shiga garin Kufa da isa fadar Ubaidullah, har zuwa Sham wanda wadannan abubuwan suna nuna jarumtakar Sayyada Zainab, amma abinda yafi jan hankali shi ne abinda ya faru a fadar Yazidu (LA).

Lallai tarihin waki'ar Karbala ba zai cika ba matukar ba'a ambaci jarumtakar Zainab Alkubra ba. Akwai bambamci tsakanin Zainab kafin Karbala da Zainab bayan karbala. Domin waki'ar Karbala ta bayyanawa Duniya boyayyiyar shakhsiyyar da take kimshe a cikin Sayyada Zainab, wadda ta kasance tarbiyar Imam Ali da Sayyida Zahra (Salamullahi Alaihima). Bayan wannan doguwar tafiyar, sun isa garin Sham ranar 2 ga watan Safar, cikin yanayi na gajiya, yunwa, kishirwa da kunar zuciya, fararen idanuwan Sayyada Zainab sun yi jajajur, sunbulallun tafukan kafarta sun yi kirci, fatan jikin ta tayi yaushi, tafukan hannayenta kamar kirgi, saboda wahalar tafiya. Da zuwa kai tsaye an wuce dasu ne fadar Yazidu (LA), a cikin yanayin da duk mai tausayi in ya gansu sai ya zubar da hawaye koda kuwa Kafirai ne aka yiwa hakan bama 'ya'yan wanda yazo musu da Addinin da suka shiga rigarsa suka tabka ta'asa ba. Sun keta zauruka bakwai a cikin fadar kafin su isa inda Ja'irin yake. Sun tarar da shi a zaune a kan AL'ARSHINSA kewaye da 'yan majalisar sa, manyan gari da Ambasadodi na kasashe dabam-dabam suna zaune a kan Kujeru na Zinari da Azurfa a irin wannan yanayin a ka shigar da 'ya'yan wanda yazo da Addinin a matsayin ganimar yaki.

Yazidu (LA) da farko yayi alfahari yayi maganganu na gadara. Bayan gama surutansa sai Sayyada Zainab ta kalle shi cikin wulakanci ta buga masa tsawa ta ce da shi; 'kai yanzu Yazidu kana tsammanin yanda ka jawo mu a matsayin ribatattu,ka kwace daga garemu ikon Kasa da sararin Samaniya mun wayi gari karkashin damkarka cewa wannan wata ni'imar Allah ce a gareka? Ta ce na rantse da Allah kai a idona kankani ne kuma wulakantacce, wanda bai isa komai ba, maras mutunci kwatankwacin kwayar Zarra. Nan take Yazidu ya rude ya hau makyarkyata ganin cewa Mace ta muzanta shi gaban baki da manyan mutane, yanayin fada ya fara canzawa har zuwa karshen abinda ya wakana a majalisar inda ya rasa izzarsa, ya dawo cikin kunya ya fara la'antar Ubaidullah da barrantar da kansa, yasa a ka sake su, suka kama hanyar komawa Madina. Wannan itace JARUMA ZAINAB, amincin Allah ya tabbata a gareta.

DAREN BANKWANA DA MASOYA

"يا أيها الذين آمنوا استجيبوا لله و للرسول إذا دعاكم لما يحييكم"

Ya ku wadanda suka yi imani ku amsawa Allah da Manzon sa idan sun kira ku zuwa ga abinda zai rayar daku. Hakika Iyalan Hussain da Sahabbansa sun amsawa Allah da Manzon sa kira, kuma sun fahimci cewa mutuwa a tafarkin Allah rayuwa ce, musamman a daren Ashura data tabbata cewa gobe ba makawa komawa ne ga Allah.

"إني لا أعلم أصحابا أوفى ولا خيراً من أصحابي ولا أهل بيت أوصل و لا أفضل من أهل بيتى"

Ni ban san wasu Sahabbai mafiya cika alkawari kuma mafiya alkhairi fiye da Sahabbai na ba, ban san wasu iyalan gida mafiya sadarwa kuma mafifita fiye da Ahlin gidana ba.

Wannan furucin ya fito daga bakin Shugaban Shahidai a daren Ashura lokacin da Imam ya tara Sahabbansa da Ahlin gidansa ya gode musu ya ce 'ku sani su makiyan nan ba ruwan su daku, ni suke nema, don haka na muku uzuri duk mai son tafiya ya sulale a duhu daren nan ya tafi, duk wasu nauye-nauyen bai'a na yafe muku, ba komai a kanku. Inda wasu ne irin masu saba umurnin Annabi su sauka diban ganima, masu guduwa a yaki su bar Annabi da 'yan tsiraru (su wane da wane ba suyi burki ba sai a Madina, su wane kuma sun shige kogon dutse suna shessheka) ya ka gani malam ai ko ba'a basu izini ba, ba makawa zasu sulale ne. Amma Sahabban Imam sai suka ce ba inda zamu ya Imam, muna nan tare da kai, kuma kwarzane ba zai same ka da iyalan ka ba sai mun kare (don Allah ina irin wadannan mutanen)? Kai bari ma a irin wannan yanayin shi Habib bn Muzahir ma aikawa yayi 'yan Kabilarsa ta Baniy Asad da basu da nisa sosai da karbala, da suzo su ma su samu nasu rabon na yin Shahada a karkashin mafi alkhairin mutane na zamanin, dan Muhammadu Rasululluh (saw).

A wannan daren, gari yayi tsit ba hayaniya, ba kukan Tsuntsaye ba na Dabbobi, dare mahutar bawa, amma 'ya'yan Annabi da mataimakan su, sun kwana a wannan daren, suna Sallah, suna Karatun Alkur'ani, suna Istigfari, suna bankwana da iyalan su da 'ya'yansu, suna masu sakankancewa da haduwa da Allah.
A daya gefen kuma Imam ya ziyarci Sajjad, Zainab, Sukaina, Laila, Rubaba da Bakir yana musu bankwana ya musu wasiyya ta karshe yana hakurkurtar da su, gobe ya war haka sun zama marayu
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: